← Book details A Bakin Wawa Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 68 OF 108

Sashe 68

A Bakin Wawa Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Yace' najeni,wasu Kaya ne za'a shigo da wasu,yau din nan aka kawo su, engines ne da machines, sai kuma wani sabon business da zasu fara iya su manya,na Kaya Sawa Suma sunzo, sannan kuma company din ya samu karbuwa har a Chicago to yanzu sun hada hannu da su, shine fah Akan wannan aka wani ce babu aiki, yau,
Tace'
okay, a wannan aikin da zakuyi na satin nan Ka tabbatar da anyi komai ba daidai ba,yarda wa'ancan zasu ji labari,nasan sunsa kudi,dayawa dole kuma sai an biyasu kudin su, sannan ka tabbatar business din nan ba'a fara ba,
Taya Kenan zanyi hakan?

Kai kasani, kuma,
Tace' kaifa physics Ka karanta ina?

Yace' ehh,
Tace' to kayi aiki dashi mugani anan,
Ta kashe wayarta,
Ta Kira Mus'ab sai da suka gaisa cikin mutumci yace' komai Yana tafiya yarda Muka tsara lokaci kadan ya rage komai ya kwabe,
Tace' hakan yayi kyau glip kaci gaba da kokari,
Yace' ok,ina mijinki?

Yana jinka,
Ki gaidashi,
Sukayi sallama ta kashe,
Tace' wai daman kana aiki ne?

Yace' ehh mana,
Tace' yayi kyau, wannan ginin na meye?

Yace' tambayar fah?

So nake nasani,
Yanzu fah kinfiye magana dayawa,
Tace' idan kuma Nayi shiru ace Nayi shiru ko?

Yace' a,a,
Yace' yanzu kin danne min kafada idan na Rama ace ba haka ba,
Tashi tayi tace' kama ji an kira magriba Ka tashi Ka tafi,kuma karka jima,
Ta tashi ta tafi dakinta, tayi alwala tayi sallah bedawo ba har tayi Isha tayi wanka ta Shirya tadawo parlour ta zauna
tana Zama suna dauke nepa takaici ya kamata,ta cika tayi fam, ta leka dakinsa shiru, kwafa tayi ta koma daki ta kwanta ta kashe fitilar wayar ta Kenan taga an medo da nepa,kin tashi tayi ta kashe wuta ta rufe ido taji ya turo kofar dakin, ya shigo daga Shi sai vest da gajeran wando, gadan ya hawo,
yace' Lafiya?

Banza tayi da Shi,
Yace' ok Bari nagani ko wurin da aka ce Yana zafi ko ya dena,
Tashi zaune tayi rufe Ido ta fara ruwan masifa yafita ya barta ita kadai a gida, ba kallo ba komai, bata Kai karshe bata ji ta hade bakinsu, Yana Mata wani irin salan Abu data kasa fassara Shi,Tama kasa gane kansa, su Ummusalma anji bakon yanayi tuni ta fara karbar sakon itama,abunda yake
Mata jiya nafila jiya batani komai ba Ashe kukan dadi jiya tayi yau tayi na dalili yau tazama cikakkiyar Mata jiya kawai sha'ani aka sha,bata sani ba, yau ake bidiri.

Tana kwance tana juyi a Kan gadan dakin tun sanda suka sato ta bata Kara ganin fuskar ko Daya daga cikin su ba, yau kwana biyar zuwa hudu Kenan kullum sai dai a kawo Mata Kaya abinci, yakasa gane inda aka kawo ta.

Tayi tunanin sune suka sauya mata wuri Ashe basu bane, Tambayar ta anan shine INA AKA KAWOTA??

By: '''Hijjart Abdoul'''
Cwthrt
*A BAKIN WAWA*
_Akanji magana_
39
Abba babu abinda yake zirga zirga a daki shikenan yanzu beda wani shago,sai company biyu da kuma business din da yake Wanda ko matar Shi batasan Yana yi ba, Zama yayi Yana tunanin mafita, mama ce ta shigo,
tace' Alhaji wai Dan Allah bazaka fada min abinda yake damunka ba?

Tun jiya kake cikin damuwa fah,
Numfashi yaja yace' saratu bazaki gane ba,
Kamar bazan gane ba?

Sai dai idan ba'a fada min ba,
Yace' kinsan de munsai da shagunan mu
sannan kuma mun fara gina katafaran asibitin mu,kinsan idan mun Gama zamu Sami kudi sosai a cikin sa, to orphanage din dake Lagos Ai kinsan Shi shine wani bature daga can Paris ya taya Shi, wai ya taba zuwa shine aka bashi number ta,kuma beda lokaci sanda yazo Amma yanzu zai zo
sai mu zauna,
Tace' indai ya taya da kudi dayawa inaga ai ba matsala,
Yace' kudin, a dollars ma zai bayar da kudin,
Tace' to kawai a sayar mana,
Yana zaune aka masa waya, dagawa yayi, abinda aka fada masa yayi saurin mikewa, dandanan zufa ta keto masa ya tashi tsaye bema Gama Jin abinda akace ba,ya kashe wayar ya Fadi
reras a Ka gado, mama tayi kansa tana Kiran sunansa Mahmud Mahmud Alhaji Ka tashi mana, ruwa ta zuba masa shiru babu motsi ga Yara duk sun tafi makaranta
da gudu tayi dakin Sameera itama bata nan bata dawo ba, fita tayi ta Kira driver yazo suka kama Shi suka a mota da gudu ta koma ta dauko hijabinta tana kuka, suka tafi asibiti.

Abba
Dakyar ta tashi ta Shiga kitchen sauran kayan da bata Adana ba ta karasa sa su inda suke, ta hada masu breakfast lafiyayye ta haddan tea yasha kayan Hadi shayi, ta jera a dining, tayi wanke wanke ta gyara inda tayi girki, gidan ta tsab yake shiyasa ma bata tarki Shara ba kawai turaren wuta tayi ta fesa Freshener shikenan, abinda tayi, daki ta Shiga taga har lokacin bacci yake wanka tashiga tayi ta fito ta shirya kayan Sawa ta Rasa Sam ta Rasa wanne zata saka, ita bata San wannan kayan ganewa ce ba'ayi ba, dakyar ta samu wani Riga da skirt English wears masu Dan Karan
kyau tasaka ta hada karami bakin Vail ta daura akanta ta Kara fesa turare, ta kalli taga goma saura, yake ta uban bacci ko baza Shi wurin aiki bane.

Gadan ta hau ta kwanta ta shige jikinsa, a hankali ya bude idansa ya ganta rungume ta yayi ta baya,
yace' Mi Amor,
Tace' uhm, Ka tashi ko bazaka aiki ba?

Yace' Amma de kinsan ba tashi na kika so yi ba,
Tashi tayi daga jikinsa tace'
Ka tashi tou,
Yace' ya jikin?

Harara ta Galla masa tace' bansani ba,
Murmushi yayi yace' to shikenan ni Bari na duba na gani ko ya....

Da sauri ta tashi,sai dai bata Ida tashi ba tace' washh Allah zafi wallahi,
Zuwa yayi yace' sannu baki Shiga ruwan zafi bako?

Turbune fuska tayi tace' Naga de da zafi,
Yace' to naji, taso muje ki Shiga,
Sunkuyar da kanta tayi tana wasa da bracelet din hannunta tana cuno Baki, sunkuyawa yayi daidai kunna ta yace' hala kina so a Mai maita
ko?

Juyowa tayi da sauri sai
suka hada goshi sukayi gware kowa dafe goshin sa
yayi, atare suka ce
yace' kinga ko?

Tace' kaga ko?

Hannunta ya kama suka tafi ita de tana dafe da goshinta tana mulmulawa taji zafi ba laifi, har dakin sa ya kaita,
yace'
jeki hada min ruwan ka,Naga kin warke harda su gyaran parlour,
Marairaice wa tayi tace' komai fah a hankali nakeyi, daurewa nake,
Shi kansa yasan tana da dauriya,kuma tayi dauriyar Amma sai, yace' a haka?

Ai bangani ba,
Fakar idansa tayi Yana cire Kaya ta Kara Galla masa harara, ta shige toilet ta hada masa ruwa zata fito sukayi kicibus shikuma zai shigo matsa masa tayi sai da ya shigo zata fita ya rufe kofar, kwalalo Ido tayi zatayi magana,
Yace' Wana kama?

Gabanta taji Yana faduwa, tace' to menayi?

Tana kif kifta ido,
Yace' laifi biyu, kin harareni dazu yanzu ma kuma kinyi, sannan yanzu kuma kinzo zaki bigeni Ashe ma uku ne ba biyu,
Tace' yaushe din Zan bige Ka?

Ohh kin yarda kin harareni din Kenan?

Juyar da Kai tayi, yace' ga kuma wani laifin,
Tace' babu kyau magana a toilet de,
To shikenan karshen magana kawai punishment dinki shine kimin wanka,
Bata juyo ba, tace' taabb kujimin da mutum Shi Bemin wanka ba daya wahalar dani sai nice karama Dani Zan masa wanka, cib,
Sarai yaji abinda tace, yace' magana kike?

Juyowa tayi ita tazaci a zuciyar ta,tayi maganar da yake a fuskarta,
tace' a,a kawai fah,
Sai kuma tayi shiru, takowa ya fara yi tana ja da baya Yana takowa tana ja Baya, haka sukayi tayi, bayan da zata ja kawai tajita tsudum a cikin ruwa, me zaiyi idan ba dariya ba,
Tsayawa tayi sororo acikin ruwan tana kallan shi, yau ta taba ganin sa yayi dariya haka, sai da taga yana murmushi, sai da ya tsagaita dariyan Amma still da murmushi a fuskarsa, ya zauna a bakin bath tub,
yace' tsuntsun daga Sama gashashe,
Daure fuskayia bata yarda ba, babu wasa a fuskarta,
yace' yarinya duk wani cikar ki da batsewa sai dai an...

Ruwa ta watsa masa hakan yasa Shi yin shiru shima ya watsa mata haka sukayi tayi be Masan sanda ya Shiga ruwan ba shima sai dakyar ta yarda yasata a ruwan zafi kuma taji sauki laifi sannan ta fito shikuma yayi wankan sa, kin Zama tayi a dakin ta koma dakin ta, ta shirya atampa tasa bata daura Dankwali ba ta fito, ta zauna a dayan parlourn, tana Danna waya,wani lokacin kuma ta kira, ta jima sannan ya fito cikin kanan kaya sai kamshi ke tashi, sannan sukayi breakfast, sai da suka Gama,
yace' muje na rakaki kiga gidan ki,
Batayi musuba suka fito suna zagaya gidan har part din su Mas'ud suka je, three bedroom ne a ciki sai parlour sai kuma kofar baya, yayi kyau shima, suka zo Garden,
tace' meyasa ba'a Kula dashi?

Yace' Nima bansani ba,haka kawai,
Girgiza Kai tayi kawai, yace' Allah ya shirya ni ko?

Tace' ohh daman idan Ka girgiza Kai abinda kake nufi Kenan?

Yace' kusan haka?

Amma ba haka bane,
Yace' Kai kekam ko?

Menayi?

Babu komai,
Suna tafiya sun zo wurin
field dinsu,
tace' idan umma tazo gidan nan ca zatace gida ba rahama, babu iska, babu sanyi sai sanyin nasara,
Murmushi yayi yace' Umma ai, jarabar ta tafi karfinta,har addu'a nake Kar Allah yabani Dan ko ya masu halinta,
Tace' ba ruwana idan tajika kaida ita ne,
To na nawa kuma, sai dai Kar a kuma,
Tace' wai tsaya kaga wata kofa a can karama, kuma kaga wata ma anan suna kallan juna,ina ne?

Murmushi yayi ya rungume ta, yace' nazaci bazaki gani ba, shiyasa ban fada maki ba,
Tace'ko bangani yau ba,wataran zangani nida gidana?

Yace' haka fah masu gida,
Fadi Ka Kara,
Ina ne?

Yace' muje mu gani ko ina ne?

Zuwa sukayi ya bude da key din hannunsa suka Shiga gida taga ni irinna su komai da komai iri daya tunkafin ta Shiga tasan hakan,
Yace' laaaa ai gidane,
Tace' gidan waye?
Chapter 68 · 0% Book details