Sashe 40
A Bakin Wawa Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Tace' haba Umma kiyi hakuri mana,a ganina idan yayi komai da kansa zaifi rike auren da daraja kina gani fa yawancin eanda akayiwa auren gatan nan basa rike matar da daraja Umma aganina a barshi yayi komai da komai yarda zaiji jiki kudin sa zaiyi kuka kinga idan ya tashi zai rike ta hannu biyu kuma ma Babansa ya fada min labarin ta kinga kuwa wannan ne kadai gatan da zamu bata,Umma mazan yanzu ba irin nada bane nima zan iya yiwa Binaif komai kodan bashi ba kodan albarkacin mahaifiyar sa,Umma kiyi hakuri don Allah,
Jikin Umma ne kuma yayi sanyi da wannan kuwa don wannan tana gani ma nan da aka yiwa wani yaro aure a kusa da ita ma yaran ko wata biyu ba'ayi ba ya saki yarinyar
gaskiya ne auren gata ma yana sawa a ki daraja mace
tace' shikenan to ai kece daman uwar 'da, kuma ki jamasa kunne idan ya kuskure ya tabo ni wallahi sai dai ya wayi gari yaga matar sa a can Ilorin baruwana ni ato,
Haba Umma kiyi hakuri mana kefa ana maki lefi wataran a rasa ma me aka maki don Allah kiyi hakuri ku rabo
lafiya Umma,
Hmmmm to naji,
Daga nan kuma aka fara tattauna yarda zasuyi daman wurin aiki zata je nurse ce kuma sai karfe biyu zatayi shifting shiyasa ma tace zata zo yau din.
A dakin kuwa sosai yarinyar ta burgeta gata da surutu ganin kanta a tsafe gashi kuma tubarkallah dashi yasa tace' ya sunanki?
Yarinyar tace sunana Rukayya Amma ana cemin Ummi shikuma
uncle Binaif haka yake cemin wai Anty Ummi,
Murmushi tayiwa yarinyar tace' sunan maman sa ai kikaci shiyasa yake cemaki Anty,
Yarinyar tace to yanzu tana ina?
Ai ta tafi bazata dawo ba har abada sai de muma mu bita,
To yaushe ta tafi?
Ta jima da tafiya ai,
Tace' kinga Bari na maki kalba ko?
Kinga kanki ba kitso kuma karfa Monday tayi a duke ki a school ko?
Da zafi fa nidai bana so ta fada tana niyyar tashi ta tafi janyota tayi tace' a,a Anty ummi zan fa baki alawa dayawa kina so?
Daga kai tayi amma badan tana so ba, tashi tayi ta dauko Mata Allah yasa tana da sauran Wacce ta taho da ita daga London tama manta da ita sai da ta ganta a cikin Jakarta sannan ta tuna da ita.
Bata tayi tace' amma sai kin yarda idan baki tsaya ba bani Kaya na zakiyi, ribbon din da ya sayo mata ta diba tayi tayi mata kamata Mata Kan dashi ta shafa Mata mai, kan yayi kyau sosai gashi mai laushi itama yarinyar har aka Gama batasan anyi ba don alawar ta take sha ba ruwanta.
Kallan kallanta tayi a madubi tace' laa kinga nayi kyau yimin hoto,
Murmushi tamata sannan tayi Mata hoto sukayi wani tare,itama ta cire mayafin kannata a haka sukayi ta hotuna abin su sai da
Goggo safiya tazo tukunna suka dena,
tace' lalle kin ciri tuta irin wannan gyaran kai haka,
Samun kanta tayi da murmusawa irin naji kunyan nan kamo hannunta tayi ta zaunar akan kujera itam ta zauna,
tace' sunana Safiya zaki iya cewa Anty safiya ko sister ok?
Shiru tayi kafin tace' Ummusalma nasan cewan Binaif zai rike ki da mutunci da amana, kema don Allah ki rike shi dahakan,
Dagowa tayi ta kalleta, murmushi tayi tace' selfish ko?
Shiru ta kuma tayi daga bisani kuma,
tace' kiyi hakuri da halin Binaif bani na renashi ba kanwata ce labarinsa kawai nakeji daga wurinta duk wayar duniyar da za muyi sai tace Binaif kaza Binaif kaza tana mutukar San shi, ita tafi kowa sanin halinshi sai kuma ni da take bani labari,Yana da dadin zama idan ka iya zama dashi,wani lokacin Yana da san barkwanci wani sa'in kuma magana ma baya so, baida san kanshi ko kadan sannan idan ranshi ya baci to bazaiyi magana ba koda kuwa yana Jin yunwa kuma bazai je ya zuba ba, haka yake wani irin juyyayyen mutum ne shi, abinda nake so dake shine Don Allah kiyi hakuri da kome zaki tarar ko mekyau ko marar kyau, hakuri shine komai, dan hakuri shine auren ma gaba dayansa musamman na yanzu maza basu da tabbas bazan yabe shi ba don
Yana 'dana
sai dai cikin kaso tamanin haka halinsu yake, kiyi hakuri wannan hakuri Shi kadai zan iya baki shi kinji ko?
Batasan mezatace ba magana zatayi tace ta karba kome?
Me kuma take son ji game dashi ?
Abinda yake so?
Me yake burgeshi ?
Kome?
Kallanta tayi ahankali kamar me tsoron magana
tace' me yake so kuma?
Murmushi Anty safiya tayi,
tace' a bangaren abinci Yana san dambun cuscus,tuwo, yadai fi san abincin gargajiya, Zan iya fada maki sauran kya gane da kanki na Baki hint,
Hannunta ta kuma kamawa tace' taso muje parlour,
Parlourn suka koma Anty safiya ta je dakin Umma sai gata da
yar jaka ta fito tana Kiran mai aikin Umma zama tayi tace' sauko kasa na maki kitso, babu yarda ta iya haka ta sauko ta zauna badan taso ba sai don bazata iya musu ba, mai aikin kuwa da
lalle ta fito a hannun ta,
Umma tace' ki mikar da kafar a miki kunshi,
Shima mikewa tayi aka fara Mata, ummi da tun dadewa ta fito daga daki tana kan kujera tayi nan tayi nan bata zama wuri daya sai kace rainan Maza.
Ji yayi ma zuwa gidan ya masa nisa gabadaya wani tashin hankali yake ciki wani irin zufa ce ta jika masa kayansa babu abinda yake furtawa sai Innalillahi wa'inna ilaihirraji'un, har ahak
a yazo gida ko jira agama parking beyi ba ya fito ya Shiga gida,bakowa a parlour sai TV dakin Mama ya wuce fitowar ta kenan daga wanka ganin yanayinsa
tace' Alhaji lafiya kuwa?
Yace' wanne lafiya?
Mutane ashe daman kawai kiwon mutane suke haka?
Yau kinji tambayar da aka min ne?
Bazan iya tantance maki tashin hankalin da na Shiga ba,daman da ace ba a gaban su nake ba wallahi sai na shako su sun fada min uban wa ya fada masu wannan maganar, wannan ai tozarci ne,
Fada yake bilhakki da gaskiya,
Mama tace' haba Alhaji Ka fada min me ke faru mana ba wai ka
daureni ba da jijiyata ba, yi min bayani meke faruwa,
Banza yayi da ita ya fara zirga zirga sai da ya lafa sannan ya fada Mata abinda ke faruwa,
tace' Alhaji baka
ganin kawai 'yan adawa ne da basa son ci gaban mu?
Tace' kuma beyasa Ka sai da company bacin bamu da takardu a hannu,
yace' dalilin shine,zamu sami riba biyu kinga ga kudi sannan kuma ga companyn mu zai dawo gare mu, kinga idan na bashi takardun karya da shi zai dogara kuma kinga bayan kwana biyu sai naje da shaidu na kinga daga nan zai dauko waccan takardar a matsayin shaida kuma ta karyace shikenan zai dawo hannuna idan ma ba'a ci tarar sa ba,
Tace' to da kasan da wannan wannan zancen banza zai daga maka hankali kyalesu kawai sai mu dauko 'yar gidan Yaya hajjaty dake Cyprus kaga shikenan kuma ita Salma ba Ummusalma ba,
Jin wannan batu nata yasa Shi cikin farin ciki tuni yama manta da batun 'yan jarida kuma zaiyi maganin su amma ta yaya?
Bashi ya dawo ba sai karfe uku na rana
kasancewar yau juma'a akwai cunkoso shiyasa ya jima be dawo ba har uku, gaba daya ya gaji rigar bayan ya cire
ya riko a hannu ya daura a kan kafadar shi dayan kuma ya riko Leda
ya shigo gidan,a Kan kujera ya zube ya kwanta yana sauke ajiyar zuciya rufe Ido yayi ya bude dakyar ya tashi ya Shiga daki tana kwance kamar me bacci sai dai ba bacci take ba tunanin sa kawai take har yanzu bai dawo ba kuma ta kasa kiranshi kawai sunansa ta zubawa ido wayar a hannun ta take Idan ta a rufe kanta a bude
kitson ya zubo har kafadar ta ta sha riga da wando sun Mata kyau sosai kallanta kawai yake
baima San ya karaso ba sai ganinsa yayi a Kan gado gefen ta yasa hannu ya fara shafa gashinta kanta, a hankali ta bude ido suka hada Ido kasa dauke nata tayi sai ma kara zuba masa su da tayi samun kanta tayi da,
cewa' ina kaje?
Baka tashe ni ba?
Bai dena shafa kannata ba cikin muryan nuna alamar gajiya kuma a hankali,
yace' Baki min sannu da zuwa ba zaki fara tambaya ta?
Tace' Baka fada min ba,kuma sannan Ka tafi kana fushi dani,
Hawayefa yake hangowa kwance a idanta yana daf da zubowa. ji yayi bai kyauta mata ba ya fada laifinta atleast yasan zata gyara, ganin idan tasake magana hawayene zai zubo mata yasa ya sunkuya daidai fuskarta ya furta
am sorry,
Ya fada yana lumshe ido,
Tashi tayi zaune tana goge Dan hawayen da zai zubo mata,ta tashi ta shiga toilet bata jima ba ta fito,
tace' na hada maka ruwan Ka kaje kayi,
Ware ido yayi irin really......
By: '''Hijjart''' '''Abdoul'''
Cwthrt
*A BAKIN WAWA*
_Akanji magana_
Yace'
thanks,
Haka nan ta ji dadi a zuciyar ta tare da wani farinciki, bayan ya Shiga wanka,itakam tasan indai tana tare dashi ji take gaba daya damuwar ta yayewa take baza ta iya fassara yarda take ji ba, kitchen taje ta zubo masa abinci har lokacin bai fito ba ajiyewa tayi a akan center table din dakin komawa tayi ta dauko ruwa tare da cup ta dawo ganinsa daure da towel yasa ta saurin dauke kanta taje ta ajje zata fita taji ya rike hannunta, gabanta taji ya fadi janyota yayi,
yace' ina zaki kinga mijinki ya fito a wanka shine zaki fita ko?