Sashe 98
Zumuntar Kenan Part 1 Complete Hausa Novel · about 5 min read
***
Jirgin 'Aric' muka bi zuwa Lagos a washegari, 'already su Zanirah sun san da zuwan mu. Don haka muka same su a filin jirgin saman sunzo tarbar mu da yaransu Fa'izah da Amra mai sunan Hajjah.
Yaya Aliyu yayi kiba har da tumbi tabbacin hutu ya zauna, kazalika itama Zanirar, Zannura inji Hajjah tayi kiba mul-mul da ita, tayi haske na tsabar hutu, daliba a jami'ar Lagos (UNILAG) tana karantar likitancin kashi.
Suka tarbemu da farin cikin da baya misaltuwa. Ni da Zanirah muka rungume juna, haka Fa'iz da Yaya Aliyu. Tun daga (Airport) labari ke cin kowannenmu har cikin gida bakinmu bai yi shiru ba ni da Zanira.
Na kasa shiru da irin daular da naga yaya Aliyu da iyalinsa ciki, na ce.
"Shin wai Zanirah ba aikin kamfani Yaya Aliyu ke yi ba?" Zanirah tayi dariya ta ce, "Da kenan. Ai Yaya Aliyu likkafa ta mugun ci gaba. Yana daya daga cikin mamallaka kamfanin sarrafa gilashi tsura dake Japan. Sannan yana safarar tagogi da kofofi na gilashi daga kamfanin zuwa gida Nigeria".
Na ce, "Na fahimta. Allah Ya kara arziki mai albarka takowanne fanni".
Anyi zumunci wanda aka dade ba'ayi ba. Diyar Zanirah ta biyu mai sunan Hajjah da suke kira Amrah kamar Ya Fa'iz ya haifeta saboda kamanninsu.
Kwananmu uku a Lagos muka juyo gida Kaduna, muka fara shirye-shiryen tafiya Wales.
***
A CARDIFF (WALES)
Gidan da Abubakar Mukhtar Giwa yake zaune yana Cardiff, wata irin rayuwa ce muka tsinci kanmu, wadda ba zan iya bayyanawa ba. Ubangijin da Ya halicce mu, Ya kuma yo mu jini daya, Ya sanya wata irin soyayya da shaquwa a tsakanin mu da biro ba zai iya rubutawa ba. Abinda zan iya cewa kawai shi ne aurenmu tattare yake da albarkar iyaye wadda ita ce komai. Ita ke haifar da komai, ita ke bude hanyar kowanne alheri cikin rayuwar dan Adam.
Ko wata uku bamu rufa a Cardiff (Wales ) ba Yaya Fa’iz ya samar min ‘admission’ a jami’ar Cardiff University of Cardiff ). Ala dole na sauya layi kasancewar turai basa yin ‘course’ dina. Na soma karantar (Civil Law).
Watanninmu Shidda a Wales muka ji kira daga gida Nigeria. Wani irin kiran waya mafi muni a rayuwarmu da dukkan zuri'ar Abubakar Bamalli. Wato mu zo gida Hajjah babu lafiya, jikinta ya rikice kuma mu kadai ne a bakinta.
Haka Ya Fa'iz ya tattara hidimomin nemansa ya ajiye a gefe muka taho gida. A lokacin ina da cikin fari dan wata hudu.
Ashe Hajjah sa'i yayi, kwananmu uku a Giwa Allah Ya yiwa Hajjah rasuwa tana mai sa mana albarka da mu da iyayenmu baki daya, da alfahari da haihuwar su. Tana addu'ar da rokon su ko bayan ranta, su cigaba da daura igiyoyin data bari na aurarraki a tsakanin jininta.
Mutuwar Hajjah ta girgiza ta kuma dimauta baki dayan A.B, wata irin girgizawa da ba'ayi irinta ko lokacin mutuwar Abubakar Bamalli ba. Babu wanda bai gigice ya fita hayyacinsa ba, kada Abubakar Fa'iz ya ji labari. Wanda sai da aka yi da gaske kafin ya koma bakin aikinsa. Hatta abinci yasan Hafizi ya rasa Hajjah, tunda shima ya rasa Hafizin na lokaci mai tsawo.
Watanni biyar da rasuwar Hajjah na haifi yaro namiji, Fa'iz ya cika burin Hajjah ya mayar mata da maigidanta kuma takwaransa muna kiransa Sadiq.
Bayan haihuwar Sadiq da shekaru biyu na haifi Mukhtar, a lokacin karatuna yayi nisa sosai. Ahmad ya biyo baya muna kiranshi (Khazrajy), sai haihuwata ta hudu ne Ubangiji (S.W.T) Ya nufe ni da cika burin Hajjah na samu 'ya mace. Gaba daya daga mu har 'yan uwa HAJJATY muke kiranta. Allah ya dauki son Hajjaty ya sanya a zuciyar Yaya Fa’iz. Su Mukhtar sai suka zama ‘yan kallon sha’anin Daddy da Hajjaty. Gashi ta yo kamannin Hajjah sosai da dan banzan wayau.
Haihuwar Hajjaty ta zo mana da sabon sauyi. Rana daya naga Yaya Fa'iz yana tattara 'belongies' dinsa daga kasar Birtaniya, ya aje aiki da 'British Airways' akan kashin kansa ba da son ransu ba, a cewarsa lokaci yayi da zai bada gudummuwarsa ga jiragenmu na gida Najeriya wanda rashin kishin kasa namu na ‘yan Nigeria yasa har gobe suke koma baya, British Airways suka yi mishi tukuici mai yawa wanda koda bai koma aiki ba nan da shekaru ashirin a gaba, a rayuwa dai ta dan Nigeria, Nigeriar ma Arewa, kuma dan asalin garin kauyen Giwa, ta ishe shi shida iyalansa su kasance cikin rufin asirin Ubangiji.
Gidanmu na Malali aka sabunta aka fadada shi don walwalar yaranmu. Muka dawo Kaduna ina dauke da cikin kanin-ko-kanwar Hajjaty.
Ya debi samarin dukkaninsu ya zuba a British International School dake Lagos, Yaya Aliyu ke kula dasu a can. Gidan daga ni sai Hajjaty, itama da cikina ya shiga watanni takwas Maman Kaduna ta dauketa.
Ranar da na haifi MAIMUNATU ranar Yaya Fa'iz ya fara aiki da 'Aric’.
Duk yadda dan Adam ke burin rayuwa zan iya cewa mun sameta. Ba zamu gushe ba face muna masu godewa Ubangijin Halitta. Mai azurta wanda Yaso, a kuma lokacin da Yaso. Ya talauta wanda yaso, ba don baya son shi ba sai don ya jarraba imaninsa. Rayuwa mai cike da so da kauna, irin wadanda basa 'fading' (kodewa) har muka fara furfura. A lokacin da nake da mukamin babbar Lauyar Gwamnatin Tarayya a Federal High court reshen jihar Kaduna, ina rokon Allah Ya kara soyayyar juna a zukatanmu, yarda, aminci da arziki mai albarka, ya raya mana yaranmu cikin tarbiyyar islama har zuwa ranar da muka daina numfashi.
MASHA ALLAHU LA-QUWWATA ILLA-BILLAH!!!!
Nan na kawo karshen littafin ZUMUNTAR KENAN! Da fatan za'a dauki darussan da littafin ke koyarwa muyi amfani dasu cikin rayuwar mu ta yau da kullum. Taku har abada Sumayyah AbdulQadir (Takori ).