Sashe 45
Zumuntar Kenan Part 1 Complete Hausa Novel · about 4 min read
****
Kwana biyu kacal duk na rame fiyet na zabge na fita a hayyacina. Sai ka rantse na yi shekara ne a kwance. Likita ya bamu sallama tare da kashedi iri-iri ga su Babana. Baban Kaduna ya ce, “Af! Ai aure ba makawa za a kwance shi me ya yi zafi?’
Wata sabuwa in ji ‘yan caca! Hajjah ta dawo ta girgije ta sanya ranar biki kwanaki bakwai masu zuwa, kasancewar ana jiran Basheer da zai dawo kwanaki uku da zuwan Fa’iz. Ashe daman rudewar ganin halin da na shiga ya sanyata canza alqibla a baya? Uhm! Zan ga wanda za su yiwa bikin kuwa.
Babban rangwame ga zuciyata ban sa fuskar azzalumin ko sau daya a idanuna ba balle keyarshi. Wannan ya tabbatar mani lallai ne shima yana tsoron haduwar mu which I believe must be the most dangerous approach bayan gushewar shekaru masu dama.
Ummi kam ta rungumi kaddara, ta bi umarnin iyayenta, a cewarta, iyayenmu ba za su taba zaba mana abin da zai zama cuta garemu ba. Ba za su taba kaimu mahalaka ba (Ummi fa ba ni ba).
Karfe tara na dare na kadaice kaina cikin (store) kuka nake kamar raina zai fita. Irin shirye-shiryen da na ga A.B baki daya na yi ya tabbatar mani biki babu fashi za su yi shi. Ba ruwan kowa dani, ba mai shiga sabgata don da alama basu ma dauke ni a cikakkiyar mai hankali ba.
Da na yi na gaji, babu mai rarrashi, babu kuma abin da kukan zai tsinana mini, sai na daura dukka hannuwana biyu a ka na shiga kwarara ihu tun karfina, ina bubbuga hannuwana jikin buhunhunan masara da shinkafa dake lode a store din.
Jama’ar gidan duk suka baro abin da suke yi suka taru a kaina ban ga alamar akwai mai shirin lallashi na ba ko tambayar ba’asin ihun da nake yi. Kallo na suka tsaya yi tamkar masu kallon talabijin.
Ummi ta yi tsaki ta ce, “Allah wadaran rashin tawakkali da rashin hankali da sakarci wallahi! Shin cikinmu don wa kike wannan haukan Fa’izah? Aure dai baya wurinmu kuma bamu muka daura ba balle mu warware miki, don haka ki kyale mana kunnuwanmu su huta”.
Hajjah ta fito daga kitchen ta ce, “Don son Annabi wanda duk ke son gamawa da duniya lafiya ya tafi a wurin nan ya kyale Fa’izah!”
Na sake sheko ihun tun karfina, na ce, “Hajja kun cuce ni, ku doke ni ku hanani kuka? Ku kulla min igiyar aure da mutumin da na ki jini a duniya fiye da mutuwa ta, bayan kin raba ni da wanda nake so da farko da na karshe, sannan ki ce ba zan yi kuka ba? Shin in ban yi kuka ba ya rage min radadin da zuciyata ke yi kashe kaina kike so in yi don bakin ciki ko me?”
Baban Giwa ya ratso mutane bayan ya karyo reshen dalbejiya ya ce, “Uwar waye ta cuce ki ba dai uwarmun ba ko? Ja’irar yarinya har nake daga hakarkari nake son ayi miki son ranki don a zauna lafiya, ashe baki da mutunci baki da da’a? Hajjah kike cewa ta cuce ki?”
Ya zuge ganyen baki daya ya shiga dankara min dukan da ake kira dukan mutuwa, wanda tunda nake a rayuwata ko makamancinsa ba a taba kwatanta min ba, amma bakina bai mutu ba, bai huta ba da fadin “Hajjah kin cuce ni.... kin raba ni da burin da na ciwa rayuwata.... ba zan taba yafewa ba muddin rayuwata.....”
Hajjah ta soma kuka da idonta a yayin da ta kama hannun Barau ta ce, “Kyale ta haka nan, Fa’izah ba ta cikin hankalinta, ka kyaleta na ce kada ka yi abin da za ka zo kana nadama, in kuma baka bari to ka sauke zuciyarka a kaina ka karasa min dukan”.
Baba Barau ya yar da tsumagiyar ya yi waje fuuuu! Kamar kububuwa, jikinsa har tsuma yake. Na tabbatar da Babana ne yau sai dai a dauki gawata in ya so shima a kashe shi.
Hajjah ba ta yi fushi ba ta kama ni za ta mikar dani, cikin kurarin kuka na ce, “Kada ki kuskura ki taba ni..... Daga yau ba zaki sake ganina ba balle ki yi iko dani. Ki tuna Ubana kika haifa ba ni ba, don haka ko kashe ni aka yi babu ruwanki......”
Zaneerah da Ummi suka saki kuka, “Fa’izah kina da hankali?”
Na ce, “Kwarai, Baba Muntari da Aunty Hauwa ke rabon ciwon hauka har na je Kaduna na samo. Ko me za ku ce ku ce wallahi banni zaman aure da Fa’izou......”
Jini ke bulbula ta hancina yana shiga bakina inda Baban Giwa ya shauda min dalbejiyarshi a kan hanci. Na kai hannu na share a yayin da na zaro jajayen idanuna suka kumbure suka suntume suka yi luhu-luhu jajir. Na ce, “Ku bace min da gani ko in kakkarya ku na rantse yanzun nan, manyan munafukai algungumai, ai daku aka kulla komai amma babu wadda ta gaya mini. Tsakanina daku sai Allah ya isa!”
Ai kamin in rufe bakina na nemi kowaccensu daga yaran har manyan na rasa. Na ci gaba da gunza kuka ban ko damu da radadi da zugin da jikina ke yi mani ta ko ina ba.