← Book details Zumuntar Kenan Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 51 OF 98

Sashe 51

Zumuntar Kenan Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

****
[17/02 5:24 PM] Sumayya Takori: Fa'eez da ya tafi dauko Yaya Bashir a Airport a washegari wanda ya sauka ta Kano, qarfe hudu na yamma suna kan hanyar Kaduna daga Kanon. Bashir ya yi kwance a bayan (Henessy) yana kwarara hamma, yayin da Fa'ez ke ta tuqi kamar Allah Ya aiko shi ba mai magana da dan uwansa cikinsu. Tun can Fa'iz da yayanshi Bashir ba sa ga maciji.
Bashir ya fiddo taba ya cinna mata (lighter) wadda aka yi da qarfen azurfa ya soma fesar da hayaqi. Sanye yake cikin (Italian suit) baqaqe, da gani kaga baqon Russia cikakken Injiniya a vangaren wutar lantarki Eng. Bashir Mukhtar Abubakar.
Fa'iz ya yi maza ya toshe hanci da hannunshi, yayin da ya rage gudun motar ya sauka bakin kwalta ya kashe motar gaba xaya, ya fito ya mai da qofar ya rufe ya zauna a saman bannet xin motar. Tunanin halin da ya baro Fa'izah a asibiti jiya yake yi, wata zuciyar na ce da shi kawai in ta farfaxo ya haqura ya saketa.
To amma abin tambayar anan shi ne, idan ya biye ta zuciyar ya saketa yaya zai yi da soyayyar da ta zamo masa qaqa-nikayi? Shekaru dai-dai har goma sha... yaya zai yi ya dinke zumuncin iyalin Abubakar Giwa da ya yiwa givi saboda wauta da quruciya? Yaya zai yi ya xinke varakar da ya wanzar a A.B House? idan ya saketa tayi nasara kenan akansa wannan karon? (She's always a loser on him and so she will remain till eternity.... Wata rana na zuwa insha Alla da Fa'iza zata san babu mai sonta duk duniya kamar shi da ta riqa maqiyin da babu ya shi a duniya.
Shi kam ya tabbata alhakin mahaifiyarta ne da nata Allah Yake hukunta shi da shi ta hanyar xora mashi azabar SOYAYYAH... soyayyar kuma ba ta kowa ba ta Fa'iza Ahmad Abubakar Giwa. Wata yarinya da ya addaba, ya kyara, ya hantara babu gaira babu dalili sai a dalilin KABILA NCI, wauta da quruciya.
"To in ka qi sakinta ta mutu fa a dalilin qiyayyar ka?"
Wannan kam bai san makomar shi ba a wurin Ubangiji.
Bai tava faxawa a soyayya ba, bai tava son mace ba a kafatanin rayuwarsa, mata kala-kala kuma iri-iri ya gani a rayuwarsa musamman abokan aiki da ke qarqashinsa da ake kira 'yan matan jirgi (Caterers) na qasashe daban-daban, musamman yankin Asia inda yafi yiwa jigila da suke binshi da tayin soyayya ta banza ko ta aure, amma tunanin kucakar qanwar nan da ya baro a qauyen Giwa, ya dishe hasken duk wata diya mace daga qwayar idanunsa.
Har zuwa tahowarsa yanzun, bai manta da Alicia ba, wata (caterer) dake aikinsa shi kaxai ransa, da zai iya cewa ya tava kulawa da soyayya a dalilin abotarshi da Yayanta pilot Johari, mutanen Berlin ne. Da qyar ya samu ya taho gida shi kadai a dalilin kafewa da tayi sai ta biyo shi Nigeria sunyi aure a garin nasu Giwa, iyayenshi su Musuluntar da ita.
Alaqar shi da Johari, ta faro ne tun daga karatu a (Ukranian Institute of Aviation) wanda shi yazo karantar tuqin jirgi Rasha daga Berlin ne, shi ne kuma ya samar mishi aikin da yake yi yanzun da kamfanin tashin jirage na mahaifarsa (Berlin Airlines) aka xauke su take, abinda ya hana shi dawowa gida kenan bayan kammala karatunsa.
Don haka zai iya cewa idon Johari ne yasa yake kasa (ignoring) Alicia har kowa dake tare da su ya xauka soyayya yake yi da ita. Shi kuma yana biye mata ne don Johari yafi qarfin komai a wajensa in yana da iko. To sai dai mutum bashi da iko da ZUCIYA, barta akan abinda take so, komin munin shi da wahalar samunshi.
Abubuwa da yawa sun faru wadanda zai ce su ne silar soyayyar da yake yiwa Fa'iza ko ba sune ba. Muhimmi a cikinsu shi ne, bayan SO na haqiqa akwai son ya gyara wannan qasaitaccen zumuncin na A.B family da yasa almakashi mai kaifi ya farka ya zama wound wato (gyambo) a zuciyar FA'IZAH AHMAD ABUBAKAR, yana so ya warkar da wannan gyambon ne da SOYAYYAH. Ko da zai rabu da Fa'izah zai rabu da ita ne (only) in ya yi nasarar warkar da wannan gyambon da shi ne silar samuwarsa a zuciyarta, wadda itama bata da ikon sarrafata, domin SO da QIYAYYA duka halittar Allah ne da basu tava zama wuri guda.
Wani sashe na zuciyar Fa'iz Giwa ya ce.
"Shin me Fa'iza take taqama da shi ne haka da yasa ta ci galaba mai yawa haka a kansa, in ba don sharrin SO ba? In ba don son ta ba da ya sameshi rana xaya baiga abinda ma zai sa shi yin aure a halin yanzu ba, bai shirya masa ba (at all) yana cin kuruciyarsa ne.
In ba don so da ba ya shawara ba, bai ga dalilin da zai sa ya baro aikinshi wanda kullum ranar Allah samu ne mai xumbin yawa a gareshi, ya zauna yana ganin baqin ciki ba. Ko ma me zata yi tayi ta gama, however, yana son matarsa, saki a tsakaninsu yana ganin wataqila shi ne abu na qarshe da ba zai tava yi ba a rayuwarsa, sai in mai yanke hanzari ce ta cika umarnin Ubangijinta (mutuwa).
Mutuwar tashi ma, zai so ace daga hannun Fa'iza ce ba don Allah baya yafe haqqin rai ba, a ganinsa in tayi hakan wataqila gyambon zuciyarta zaya warke.
Tunani na qarshe da ya ziyarce shi, shi ne ta gama suman, qafarshi qafarta, kwas xin nan da zai tafi Amsterdam sati uku masu zuwa, tayi ta suman tana farfaxowa yana da ruwan da zai yi ta yayyafa mata, indai ba mutuwa zata yi ba Falillahil-hamdu.
Bai kai qarshen tunaninsa ba Bashir ya bude murfin motar da qarfi, ji kake butt! Ya fito yana fadin.
"Kai, don ubanka ance ma ni bawan gidanku ne da za ka tsaida ni a gefen titi zafin rana na duka na?"
Fa'iz ya yi tsaki ya ce, "Kada ka sake zagar min uba Yaya Bash! Ta yaya zaka kunna min hayaqi cikin mota in zauna ina shaqa, na tayaka sha kenan? Iyaye kuma tunda ba ka ganin darajar su ni ina son kayana, kada ka sake ka sake zaginsu a gabana, na rantse ba zai yi maka dadi ba".
Bashir ya dubi Fa'iz sosai yana cikin wani irin yanayi na tashin hankali da bai tava ganinsa ciki ba, har wata rama ya yi, kafin ya baro Russia ba haka ya sanshi ba sam. Jikin Bashir ya yi sanyi, ya koma mota ya zauna ba tare da ya yi magana ba sai da Fa'iz ya mula, ya kammala shan qamshinsa da harare-hararensa kana ya ja motar aguje tare da sakin qira'ar Abdurrahman-Sudaith a rediyon motar cikin Suratul Nisa'i. Wannan ya taimaka wajen sanyaya zuciyarshi dake tafarfasa babu gaira babu dalili.
Bashir dai binsa yake da ido, da zuciya, ya kasa shiru, bayan sun jima suna tafiya yana kallon Fa'izun wanda idanunshi suka kaxa suka yi jawur.
"Wai kai me ke damunka ne?"
Fa'iz ya harare shi ta cikin madubi, "Ai ni babu abinda ke damuna face tawa matar da ta tsane ni tamkar mutuwarta, duk da bani da wani hali abin qi, baya ga shirmen quruciya na can baya, wanda da ace zata saurare ni ta saurari kalaman dake qunshe cikin baki da zuciyata da ta fahimce ni, kai kuwa ke da damuwa.
Baya ga baqin munanan xabi'un da kayo guzuri, shan giya, taba da bin matan bariki tamkar tsohon bunsuru, kai da wai an kaika ne domin ka zama ubana, mai dorani bisa hanya sahihiya, ka rikide ka zamo tantiri, wacce irin qiyayya ce ba zaka gani daga taka matar kamila Hadizatu ba?"
Bashir ya tashi zaune daga kishingidar da ya yi a kujerar baya tare da wurgi da abinda ke hannunsa ta taga gaba daya, ya antayo ashariya cikin harshen (Ukrain) wadda Fa'izun a duk zamansa a Russia shekaru goma vai tava jin wani ya yi ba, haka ya lailayota da turanci wadda Fa'izun bai san akwai ba ma, sannan ya shimfidota da Hausa ji kake.
"Abu kazan uban nan!
Uban waye ya xaura min auren? Sharrin da zaka je kayi min a gida kenan Fa’iz? Wato dama ido ka sa min a duk motsina ko me? Duk tambadar da kake yi da Alicia na tava daga ido na dube ka da zaka ce ina neman mata? Ai dama gwano baya jin warin jikinsa...".
Fa'iz ya yi saurin miqa hannu ya kashe qira'ar da ya kunna na karatun Alqur'anin dake tashi, ya juyo ga Bashir bayan ya kashe motar baki dayanta. Ya yi rantsuwa da Allah ya sake rantsewa ya ce.
"Wallahi-wallahi ka sake zagar min iyaye sai na sauke ka a dajin nan yaya Basheer!".
Basheer ya dubi qwayar idon Fa'iz sosai har wani blue-blue take, jijiyoyin kansa sun tashi rada-rada saboda fushi da mazantaka, ya ce a ransa.
"Anya Fa'iz qanina ne?"

Fa'iz qato ne qwarai murzajje mai wasu irin qarfafan damatsa da ginannen jiki na Bamallin usli tamkar (Late) Abubakar Giwa a sanda yake nashi tashen quruciyar, yana nome manyan gonakinsa da hannunsa ba tare da ya nemi mai tayashi ba. Irin mazan da jarumtakar su ce kadai tasa duka rabin rayuwar su cikin iska suke yinta, ruwa, hazo, zafin rana, sanyi ko duhun dare baya hana su lulawa cikin sararin samaniyar Subhana. Wanda duk ya yi qoqarin dambe da su, mace ko namiji labudda uwarshi ta haifi wani kawai amma ba shi ba.
Savanin shi Basheer da (gulder), hayaqi da zina da ya jefa kanshi a Russia rana daya suka haxu suka tsotse masa jiki da kuzarinsa. Sai dan banzan bakin tsiya da kaudi wanda ba a kashe shi a magana. Inda suka bambanta da Fa'iz kenan, wanda kafin ya yi qwaqqwarar magana ma aiki ne jawur, sai lokacin da ya sa kansa.
Bashir ya ja bakin (glass) ya mannawa idanunsa, ya koma yadda yake da, wato kishingida, yana ta huci shi kadai kamar kumurci, bai qara magana ba. Fa'iz ya ja motar a guje, bai tsaya ba sai a qofar gidansu dake unguwar Jabi Road cikin garin Kaduna.
Chapter 51 · 0% Book details