← Book details Zumuntar Kenan Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 71 OF 98

Sashe 71

Zumuntar Kenan Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

A firgice na cira kai na dubi Baba. Kuka nake har naji babu dadi, na gyara dankwalina, bana ko batun takalmi balle mayafi, tuni na riga Fa'iz kaiwa bakin mota, na bude baya na shige. Na kifa kaina jikin kujerar gaba ina rusa kuka na gani kasheni! A can cikin gida kuwa gardama ce tsakanin Fa'iz da Baba. Ya ce shi ba zai tafi dani ba a yanzun ya fasa. Ayi duba da halin da nake ciki. Wane farin ciki zai tsinta a tare dani?" Baban ya ce, "To Fa'iz in ka saki auren ne kamar yadda take so ka bani takarda wadda zan nunawa Hajjah da sauran dangi Fa'iza tayi zama mai dalili a gidana, domin Hajjah har ta fara nuna fushinta da zaman Fa'izah tare da mu bamu mikata Kaduna ba. In kuma kana aure, to Fa'izah bata kara zamar min gida ta kara kwana daga yau. In baka tafiya da ita inda kake kasan inda zaka ajeta amma ba dai gidana ba! Yarinya daya tal na neman zautar dani kamar ita kadai na haifa? Na gaji wallahi". Fa'iz ya sake kwantar da murya ya ce, "Baba Fa'izah ta rantse ba zata zauna dani ba. Ta yaya zan kaita inda ake ganin mutunci na ake girmamani ta dizgani ko ta rufe ni da duka don Allah Baba? Ni kam a kyale Fa'izah, ayi mata addu'a ta samu saukin bacin ranta kafin mu tafi. Amma bai dace in tafi da ita cikin wannan hali ba". Baba ya ce, "Na gama maganar nan Fa'izu, Fa'izah ba zata sake kwana mini cikin gida ba sai in baka aure. To wannan kuwa, bani da yadda zanyi da ita". Fa'iz ya fice fuuu shima nashi ran a bace. Ba haushin Baba yake ji ba, zuciya yayi mai cewa ya yiwa Fa'izah duk abinda take so don a zauna lafiya. Kamar yadda Baba ya gaji shima ya gaji. In so cuta ne to hakuri ma magani ne. Bai taba ganin yarinya mai taurin kai da taurin zuciyar Fa'izah ba da kullaci wanda baya jin lallashi. Ya bude kofar motar ya shiga ya zauna, har ya tayar da ita ya juyo yaga ban rufe kofar ba. Ya fito yazo ya rufe ya sake ta da motar aguje, ban san inda ya nufa ba sai dai jikina ya bani ba Kano bane, ba Kaduna bane. Ya manta shaf da Shu'aib dan rakiyarsa. Shima Shu'aib din yana kallon mu muka fita bai yi gigin binmu ba. Nayi kuka nayi kuka har na gode Allah, na kuma ba uku lada. Hawaye sun kafe, murya ta dishe, haka idanuna sunyi luhu-luhu. Don haka nayi shiru na zubawa sarautar Allah ido ta hanyar kurawa tsirrai halittar Ubangiji ido dake giftamu aguje suna tsere da junansu (bishiyoyi da dazuzzuka). Ko ma mahalaka Fa'iz zai kaimu, a wannan lokacin ban damu ba. Domin na fidda rai da rayuwar farin ciki tunda iyayena da suka haifeni ma basa so na, na kuma tsani rayuwar ita kanta muddin tare da Fa'iz zan yi ta. Na kuma tsani wani abu wai shi farin ciki ya sake ratsowa cikin rayuwata.. [19/02 4:34 PM] Sumayya Takori: *** Ban tashi kaduwa da al'amarin Fa'iz ba sai da na ganni cikin jihar Niger (Minna). Ya samu gefen wani titi yayi (parking) ya doshi wasu masu kirar wukake da ludaya na garin Minna ya yi cinikin wata sharbebiyar wuka gayawa jini na wuce, irin ta yankan shanu, suka yi 'yar magana da makerin, sai naga an fara rubutu a jikin wukar. Ya kunso wukarshi cikin takarda ya biya kudi ya shigo ya ajeta a gefenshi ya kunna mota. A raina na ce. "Eh, gara kayi min yankan rago ya fiye mini da hada rayuwa da kai. Mugu, azzalumi, munafiki, mara imani. Ko kuma kayi min yankan kifi gunduwa-gunduwa zai fiye min kwanciyar hankali fiye da in karashe rayuwata matsayin matar Fa'iz Bamalli Giwa. Uhh! Daga wurin masu wuka kun san ina Fa'iz ya dosa? Fa'iz shahararren kogin Nigeria da nake ji cikin tarihi da 'Geography' sanda nake sakandire, wato 'RIVER NIGER' ya nufa damu wanda an tabbatar yanki ne daga kogin Nilu (Nile). Can ya dosa damu gadan-gadan ya zagaye masu kamun kifi zuwa can inda babu mutane ko daya. Ya danna wani madanni jikin motar glassai bakake suka maye gurbin farare (tinc) suka rufemu ruf. Ya kwantar da kujerarshi baya sosai ya bita ya kwanta yayi matashi da hannayensa ya yi 'facing' dina (fuskantata) sai kuma ya yunkuro ya taso ya dauko wukar nan ya cireta daga cikin takardarta tana walwali da walkiya. Duk da abinda na ce a baya na gara min ya kashe nin, yayi min yankan rago ko na kifi gunduwa-gunduwa amma a wannan lokacin da matuwar ta iso muraran sai na samu kaina da matsawa gefe na soma marmasa kalmar shahada tare da duk irin addu'ar da tazo bakina. Walwali take da walkiya inba za'a ce idona bane yake min gizo da sai ince har huci wukar take yi. Sunan Allah nake kira a halshena da zuciyata, idanuna sun kankance sunyi wuri-wuri, amma babu hawaye a cikinsu sai firgita da razana. Na tabbata yanzu Fa'iz ya fini hauka, na dubi rubutun da aka yiwa wukar a sace, "FA'EEZAH". Na fiddo ido kuru-kuru na sake makurewa jikin kofa. Fa'iz ya cillo mini wuka akan cinyata ya tube riga baki daya, har singiletin jikinsa itama ya cire yayi kira da kakkausar murya. "Fa'izah!". Subhanallahi-subhanallahi, Hasbunallahu wani'imal wakeel kawai na shiga furtawa, na runtse idanuna. Ban taba ganin namiji a tube ba balle kato mai girma irin Fa'iz, yayinda haiba da kwarjini na Fa'iz Giwa yayi min lullubi, ya kara fuskantata ya ce. "Dauki wukar nan ki caka mini ko ki yanka ni karewar kiyayya kenan, ko kya huce bakin cikin zamowa na miji a gareki, ko kya yafe laifin da kike ikirarin na miki, wanda kika kasa yafewa! Kika kuma ki saurarona inyi miki bayaninsa. Idan kika yi hakan na tabbata zaki huce ba karya...". Nayi salati na dire ba tare da na kai karshen sa ba na dauko sabo. Na ture wukar daga cinyata ta fadi kasan kujera, na soma murda murfin motar ko na samu ya bude in san inda dare yayi min amma ko gezau kofa bata yi ba, yasa (lock) ya kulle ta gaba daya. Cikin dakiya da tsare gida ya ce. "Haba Fa'izah, (be brave) mana! Babu wanda zai sani, babu wanda zai ganki. Na tabbata in kin yankani zaki huce kiyi rayuwa mai dadi da nagarta. Ki samu rangwamen kullaci na dake zuciyarki na zagin Momi, mugunta da azabar dana kwashe shekaru ina yi miki, takardar saki dana hanaki, tare da huta auren direban tasha tunda ni dai hannuna ba zai iya rubuta saki ga Fa'izah ba ko da ace na iya rubutu!!!". Idona rufe na ce, "Fa'iz ka bude min kofa in fita, naga alama ka haukace. Wallahi ba don komai na yarda na sanyo kafata a motar ka ba sai don furucin Babana, na yafeni da ya ce zai yi". Na fashe da kuka. Ya sake matsowa ya dauki wukar dana yasar, ya ce cikin taushin murya. "Fa'izah, ki kwantar da hankalinki ki yanka ni, kinga in ba hakan kika yi ba baki huce haushi na ba, baki kuma ci nasarar kiyayyarki ba. Kamar yadda bakin cikina ba zai kyale zuciyarki ta samu sassauci ba don kuwa ni ba sakinki zanyi ba...". A yayin da ya zura min kotar wukar cikin hannuna, nayi maza na yi baya da hannuna na kwalla kara tun karfina. Ihun da ake kira kunu a makota babu wanda yasan ina yi. Ihu nake ina karawa ko Allah Zai kawo wani giftawa yaji ya kawo min dauki. Sai dai ga dukkan alamu ihu na ya tsaya ne cikin motar kadai ko ta taga baya fita. Ya ce (in subdued) wato cikin raunin murya. "Ki yiwa Allah ki aikata abinda na umarce ki, sai ki jani ki tura cikin kogin nan. Babu wanda zai ganki, wukar ma ki jefata cikin ruwan. In yaso ki samu wani ki roke shi ga kudi zan bar miki ya tuka ki zuwa Kaduna ko Giwa tunda baban ABU yasan tare muka fita...". Na girgiza kai da sauri, "Ko da nake kinka babu yadda za'ayi in kashe ka da hannuna tunda ba ni nayi maka ran ba. Sai dai na kasance cikin addu'ar Allah Ya kashe ka in huta wannan bala'i". Wannan karon murmushi ya yi, sannan ya cira ido a hankali ya dube ni. "Kin kasa gane abinda nake ankarar dake har yanzu, wato babu wanda zai ganki, ki kashe ki tura RIVER NIGER shi ne maganin kiyayyarki ga Fa'iz. To tunda kina tsoron kama wukar taki...". "Ka daina cewa wukata, ba tawa bace, kai ka san inda ka samo abarka...". "Ai don ke aka yi ta. Ko baki ga sunanki ne a jiki ba? Wai ma shin, ina haukanki da rashin imaninki yaje ne da kike yin baya-baya dani yanzu ba kamar dazu da wannan bakin ke gartsa min cizo ba?" "Na rantse da Allah ka isheni, ka maida ni inda ka dauko ni, ko kuma ka bude min na fita". Ya sha mur sosai, "Ki fita kije ina? Wajen 'yan daudu da 'yan ashana? Fa'izah babu wannan damar in har kin barni da rai. Baya ga wannan kyakkyawar dama da na baki, (remember that opportunity comes only once in life!) Muddin kika bar wannan damar ta subuce miki, to kiyayyarki ta karya ce... Kina son FA'IZ BAMALLI. Ba kuma zaki iya kaiwa 'yan bariki, 'yan daudu da 'yan ashana jikin da ya zam mallakin Fa'iz ba! Za ki bar mishi abinsa ne ya yi yadda yaga dama da shi daga yanzu har gaban abada! Muddin baki aikata abinda na umarce ki ba kina son rayuwar Fa'iz Bamalli Giwa ta ci gaba da wanzuwa a doron kasa...!". Ai jin hakan da ya fada, ya sani daukar wukar na riketa gam-gam cikin yatsuna amma na kasa motsa hannuna ko kadan. Sai Fa'iz ya matso gaba gareni sosai har hucin numfashinsa na dukan fuskata tare da sassanyan kamshin 212 dake tashi sannu a hankali daga jikinsa. Ya daga gira, tare da dan ware ido, ya kuma buda hannuwansa. "Uhm? Ina jiranki, (I'am ready)". Na runtse ido tamau, yayin da hawaye suka
Chapter 71 · 0% Book details