Sashe 4
Zumuntar Kenan Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Jim kadan sai ga shi ya dawo a fusace, ya dangwara min ma’adanar abincin a cinya yana zazzare fararen idanusan wadanda tun a wancan lokacin suke da wata irin baiwa ta kwantaccen ruwa kamar hawayen da bai kai ga zubowa ba a cikinsu, da babbar murya ya ce, “Ke kwalamammiya amayo naman da kika ci ko billahillazee in yi kuli-kulin kubra dake yanzu a gidan nan, in lallasa ki dukan da uwarki ba ta taba yi miki ba”. Na ma rasa me zan ce don mamaki da takaicin ambaton uwata da ya yi, haka Ummi da Zanira sunyi wuri-wuri. Ya ci gaba da magana cikin bala’i. “Kazamar banza mai kashi a wando, wa ya ce ki sa min kazamin hannunki cikin abincina? Tunda ma kika saka wannan kazamin hannun naki wanda ya saba yin dama-dama da kashi cikin fo ba zan ci abincin ba....” Ya daga kwanon shinkafa da taliya da miya ya zazzage min a tsakar kaina, ya ja dogon tsaki ya wuce yana cewa, “Dama dai kwalamammiyar nan ba ta zo gidan nan bane za a tadda kwayar nama cikin abinci. Ni kam shekarar bakin ciki ta zo min in dai da wannan mai kashi a wandon zan zauna cikin gidan nan. Mtsw!” Ya yi ficewarsa yana ci gaba da bambamin fada da muryarshi mai karyayyen harshen larabawan Hijaz, Hausar shi ba ta fiye fita sosai ba. Na fashe da kuka nan take, don ni babu abin da na tsana a rayuwata irin a ce min mai kashin wando (da gaske mai kashin wandon ce a baya, har na kai shekara biyar ban san idan na ji poo-poo in dauko fo in hau ba, sai dai in saki abuna a wando. Hajja da Momi sunyi fadan har sun gaji, kuma a wancan lokacin babu pampers sai napkin, haka su Inna Kubra dake gidan za suyi ta aikin kashi da yi min wanka a famfon wajen wanke-wanke). Tun a wancan lokacin ne bama ga maciji da Fa’iz, kasancewarshi mai masifaffiyar tsaftar gaske da kyankyami. Ya dauki tsana da hantarar duniya ya dora a kaina, duk inda ya ganni sai tsawa da raraka yana toshe hanci. Ban samu sa’ida a zaman gidan Hajja ba sai da Fa’iz ya wuce babbar sakandire a Saudiyaya. Su kam su Zanira dariya ce ta kama su suna makewa bayan wucewar Fa’iz, don sun san halina in ina cikin fushi kayi min dariya a kanka zan huce. Da na kai karar abin da Fa’iz ya yi min wurin Hajja a uwar dakinta tana lazimi cewa ta yi Allah ya kara, ai na gaya miki amma da yake kunnen kashi ne dake sai da kika ci. In gaya miki wannan dabi’ar banza ce, ki daina ta. Kada ki kuma cin rabon wani bayan rabonki haramun ne. Ni bai burgeni ba ma da bai shake ki kin amayo shi ba. Washegari Baban Giwa ya amso min transfer daga makarantarmu (ABU Staff School Primary School) zuwa ta su Ummi wato GIWA SOUTH PRIMARY SCHOOL. A rana ta farko da na fara zuwa Giwa South Primary na dawo da damuwa mai yawa, basu yin Arabiyya ko kadan, babu Arabic a darassanmu sabanin Staff School da muke zuwa ni da Abdallah a Zaria. Shigowarmu gida ke da wuya na watsar da littafan a falon Hajja na zauna shirim ina ta zumbura baki. Hajja dake rike da littafin Bulugul-Maram da Medicated glass a idanunta tana karantawa ta dago ta dube ni ta ce, “Lafiya?” Na yi tsaki na ce, “Bari ke dai Hajja....” Kafin in karasa sai ga Yaya Aliyu, Yaya Bashir da Yaya Fa’iz sun yaye labulen falon sun shigo, kowannensu dauke da sallama a bakinsa. Sun sha anko na farar shaddah (Hilton) sai salki take. Hajjah ce ta amsa musu, kana ta ce, “Har an daura auren?” Suka zazzauna cikin duma-duman kujerun falon, Basheer ya ce, “Eh, alhamdulillah an daura Hajja. Sadaki naira dubu dari Baban ABU ya biyawa Usman (Dan Baba Barau da ‘yar Baba Ibrahim Maryam aka daurawa aure). Sai fatan Allah ya basu zuri’a dayyaba da zaman lafiya da yalwar arziki mai albarka”. Duka suka ce, “Ameen”. Yaya Aliyu da yake duk mun fi shiri da shi ya dube ni a nutse ya ce, “Hajja lafiya Fa’iza ke fushi?” Hajja ta ce, “Gaka gata nan tambaye ta mana, nima haka ta shigo min”. Ya dawo da idonshi kaina alamar sauraro ya ce, “Wa ya tabo min Fa’iza ta?” Na tura baki sosai na ce, “Bayan makarantar su Ummi ba a yin Larabci sai Turanci”. Duka suka sa min dariya ban da Fa’iz da ya ce, “Ji ta don Allah baka kirin da ita, duk gidan nan ita ce mummuna, ko meye gamin ta da Larabawa oho?” Bashir dariya yake shi da su Ummi, Yaya Aliyu ya ce, “Rabu dasu Fa’iza, ai black is beauty. Na rantse dukkan su babu wanda zai samu mata mai kyan ki. Na yi alkawarin canza muku Islamiyya wadda ake koyar da Larabci sosai kin ji Fa’iza na?” Kuka nasa sosai, ba abin da Fa’iz ya fadi bane ya sani kuka, a’a, na tsani ayi min gwasale cikin mutane. Shi kuma Ya Fa’iz na lura baya shakkar a gaban kowa ya ci mutuncina. Halinshi sam ba irin na Yayan shi Bashir da Yaya Aliyu Haydar bane, in ya raina ka kawai ya raina ka, in ya tsane ka sai ka gwammace ko hanya ba ta gama ku ba balle jini. Zama na a gidan Hajjah tare da Fa’iz daga farkon sa har zuwa inda yau ke motsi ba mai dadi bane, kai ka ce babu digon jinin juna a jikinmu. Fa’iz ya tsaneni on the ground of kazanta, ni kuma na tsane shi on the ground of mugunta. Shi Yaya ne ba mai dadi ba ga kannensa, akasin Yaya Aliyu mai son mu, mai janmu a jikinsa da nuna mana kauna ta ‘yan’uwantaka. A sannu nake fahimtar kazantar da Fa’iz yake yawan ambatawa a gareni da na soma tasawa. Na farko ban damu da sanya wankakkiyar suttura ba balle gogaggiya, ban san wani abu wai shi kintsi ko gyaran jiki ba. Uwata ba ta ja ni a jiki ta koya min wadannan abubuwan ba, ban san in gari ya waye in tatsa maclean jikin burushi in goge baki ba, sai dai in afa ruwan shayi da burodina in ci. Ga Hajja tsohuwa ce ba ta mai da hankali kan irin wadannan abubuwan ba, wanka su Ummi kullum sai sun yi amma ni sai in kwana hudu fatar jikina ba ta ga ruwa ba. Balle sabulu da soso, gani kuma daman bani da hasken fata irin na Bamalli, kalar jikina irin na mahaifiyata ne. Idan na cire kaya ban san wanne ne mai datti ba wanne ne mai tsabta ba, haka zan hada duka in danna su a wardrove dina babu ninki balle kintsi sabanin Zanirah da Ummi su da suke ma goyon Kaka. Dalili kenan da in Fa’iz na wujijjigani da wulakanci da kaskanci bani da bakin kare kaina sai dai in yi ta kuka da tunanin na yi gudun gara na tadda zago, ko in komawa zagon ne (Momin ABU), amma in na daga ido na dubi Ummi da Zanirah na tuna irin kewarsu da zan yi idan na bar Giwa, sai in manta da al’amarin Fa’iz in shigar harkokina, in kuma yi kokarin kaucewa duk wata hanya da za ta sada ni da shi a gidan don in zauna lafiya. Lokacin da muka gama makarantar firamare muna da shekaru goma sha biyu, muka samu gurbi a FGGC Gusau aji daya. Da yammacin ranar Yaya Aliyu ya shigo falon Hajja muna kallon shirin Risalah (The message) daga tauraron dan Adam ba tare da mun juyo ba duka suka amsa sallamar shi amma ban da ni, domin a lokacin ina gefen Ummi ina kuka sosai ni ba zan je makarantar kwana ba, Hajja da su Zanirah sun yi rarrashin duniya na ki yin shiru. Hajja ta ce da Yaya Aliyu a sanda ya zauna, “Yanzu nake cewa Ummi ta kira ka ku je kanti su hado duk abin da za su bukata nima nan na yi musu duk nawa tana din na su yaji da soyayyar miya, dambun nama na Fa’iza da su garin rogo ko za su bukace shi, to mutuniyar taka gata nan ta ja ta kafe ba ta zuwa makarantar kwana, ba ta kuma fada ba sai yanzu da aka gama musu komai gobe tafiya”. Yaya Aliyu ya matso gefena ya zauna a hankali yana dubana ina ta share hawaye da majina da habar zanina, jikina na tashin tsamin tashen balaga da rashin wanka. Ya ce, “Princess Fa’iza Bamalli, gaya mani matsalarki ta kin son makarantar kwana a yau, bayan a da baki ce hakan ba....” Cikin kuka na ce, “Yaya Aliyu Ummi ta ce ana saka yara yin kitso duk sati, yanke farce duk sati, wanka kullum, kuma dole kullum sai ka yi brush safe da dare, ni gaskiya za a takura min, wallahi ba zan iya ba.....” Su Ummi suka bushe da dariya har shi Yaya Aliyun. Daga bayanmu muka ji an saki wani dogon tsaki, dukkanmu muka juya, Yaya Fa’iz ne. A hasale ya ce, “Yaya Aliyu don girman Allah ka fita hanyar yarinyar nan mahaukaciya ce. Raina yana matukar baci idan na ga kana shiga sha’aninta. Ni wallahi ba don kamanninta da Baban ABU ba sai in ce canza ma uwarta ita aka yi a asibiti can inda take aiki suka hada baki aka bamu”. Fuskar Yaya Aliyu ta rine da bacin rai, ya dubi Fa’iz a hankali amma ya kasa cewa komai. Hajja ce ta ce, “Hafizi! Wacce irin magana ce wannan? Kada in kara jin makamanciyarta”. Ya sadda kai ya ce, “Allah ya huci zuciyarku Hajja, amma yarinyar nan na bukatar makarantar kwanan da ba ta so, don kwata-kwata ba ta san ciwon kanta ba, uwarta ta jawo mana baragurbi cikin zuri’a. Kaico! Auren bare bai yi ba wallahi.....” Ya juya ya yi ficewar sa. A fusace Yaya Aliyu ya mara masa baya, ya suka karke ya suka kare oho! Ya dawo fuskarshi babu annuri, ya ce (ba tare da ya dubi kowaccen mu ba) “Ku tashi maza mu tafi sayayyar”. Yanayin yadda na bude motar cikin matsanancin fushi ya sanya Yaya Aliyu