Sashe 86
Zumuntar Kenan Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
*** [23/02 11:32 AM] Sumayya Takori: *** Washegari haka na tashi sukukui! Babu kuzari ko yaya a cikin jikina. A wannan lokacin, babu abinda nake tunani illa hanyar da zan bi na gyara girgidadden aurena tun lokaci bai kure min ba. Kaunar Fa'iz da soyayyar sa ke lallasa ni ta duk hanyar da suka ga dama. A duk lokacin da na daga ido na dubi tangamemen hotonmu (window size) da aka manna a (main-palour) kamar za muyi magana, sannan tsananin kamar mu da juna ta fito sosai a hotunan. Kyau ne ke bugun kyau na mallawan usili, sai kwarjini da ya dara mini da wasu ilhamomi na daban da aka halicci Fa'izun dasu da ban taba ganinsu a tare da wani da namiji ba. Nakan tuno abubuwa da dama na irin cin kashi da rashin arzikin da na shekara yiwa iyayena da 'yan uwana akan auren mutumin da na tabbatar ban dace da kowa ba cikin duniyar nan face shi, sai inji na tsani kaina da mata masu irin halina na kafiya da taurin zuciya, riko da zuciyar rashin afuwa da yafiya, bayan dukkaninmu da Allah ba Ya hakuri damu, Yana afuwa a garemu albarkacin mai albarka, da bamu kawo yanzu ba. Hakika da Allah Baya afuwa ga al'ummar Annabi Muhammadu (S.A.W) da tuni an shafemu a doron kasa kamar yadda aka shafe al'ummar sauran Annabawa da suka gabacemu saboda kura-kuran da muke tafkawa Ubangijinmu da tsakanin mu kanmu 'yan Adam. Misalin karfe uku na yamma na dauki waya na bugawa Momi, jikina a matukar sanyaye, kamar yadda zuciyata ta mace, babu karsashi ko kankani a tare dani. Jin muryar Momi tana yi min sallama wani matsanancin tausayinta yazo ya lullubeni. Kenan ita bata da kowa a duniya da zata kalla ta ce nata ne, bayan mijinta. Baiwar Allah koda wasa bata taba gaya min ba don kar hankalina ya tashi. Ni Allah Ya bani dangin kamar ruwa masu kaunata da son yiwa rayuwata gata amma nake wulakanta su ina bata musu rai akan abinda sunyi ne amma sai nafi kowa cin ribar sa. Wato zaba min miji daya da daya a cikin 'ya'yansu wanda sun tabbata ko bayan ransu zai rikeni amana kamar rikon da uwa da ubana za suyi min. Momi taji nayi shiru, bayan ta jima da amsa wayar, ta ce. "Lafiya?" Na ce, "Lafiya". "Kin kirani kuma kinyi min shiru". Na sharce hawaye da suka yo wani irin ambaliya akan kuncina, sai naji ba zan iya tambayarta komi akan rayuwarta ba, kada in tado mata abinda ta riga ta manta dashi, tana cikin rayuwarta mai tsafta. 'And a total submission to ALLAH' da yadda Ya kaddara mata rayuwar. Na kasa 'controlling' kaina da tausayin Momi, kawai sai na fashe da kuka gaba daya. Kuka kawai nake ta rusa mata a wayar har na gaji don kaina bata katse ba, kamar yadda bata nemi taji dalilinsa ba, balle ta lallashe ni akansa. Sai da nayi mai isata sannan naji muryarta cikin sanyi tana magana. "Na rasa ke wace irin yarinya ce, na rasa a cikin mutane ke wacce iri ce, na rasa abinda yake damunki, ba mamaki gata ne yayi miki yawa. Menene aibun Fa'izu? Me kika fishi? Dame kike takama nayin butulci da irin wannan miji da Allah Ya baki? Har sai yaushe zaki shiga hankalin ki kisanAnnabi Ya faku? Duk sa'o'inki da tsararrakin ki kowanne na dakinshi cikin kwanciyar hankali, ga albarkar aure, sai ke don dai ki tabbatarwa da danginku da cewa uwarki bare ce abinda suke gudu a bare dai-dai ne. To ni dai wannan hali naki ba a wurina kika gado ba (kafiya da taurin kai na rashin tunani) ke kadai kika san inda kika kwaso abinki. Yanzu da kika ki kwantar da kai kibi Fa'izu ribar me kika ci? Meye ribar zaman da kike yi? Ke ba ga ladar aure ba, ke ba kwanciyar hankali ba, ke ba ga komawa karatun ba, ba wan ba kanin wai karatun dan kama... Saboda ke shashasha ce kuma dabba, wadda bata san ciwon kanta ba ko?" Hawaye ya ci gaba da wanke min fuska, ita bata san cewa tausayinta da nake ji ya rinjayi tasirin fadan da take yi min. Muryata cikin sanyi da shasshekar kuka mai yawa, na ce. "Don Allah Momi kiyi hakuri, ni yanzu babu abinda yake damuna. Hakuri zan baiwa Fa'iz din ma in ya dawo. Insha Allahu nayi alkawarin daga yau ba zaku sake jin wani abin assha daga gareni ba. Shima Baba zanzo in bashi hakuri. Walida nake so ki taimaka min tunda sauran sati biyu su koma wannan hutu, ba wanda ke zuwa min daga Giwa har Jabi Road, ni kadai cikin wannan katon gidan... Don Allah Momi...". Na rushe da kuka sosai wanda ya tayar da hankalin Momi, maimakon kalamaina su sanyaya mata domin kukan nawa mai zafi ne irin na kauna da tausayin DA ga MAHAIFIYARSA, yafi karfin ace akan fadan da tayi min nake yinsa. Wani irin kuka ne mai fitowa tun daga karkashin zuciya na wani abu mai nauyi da ya taba rayuwar mahaifanka. "Don Allah don Annabi Momi kiyi hakuri, ba zan kara ba... ba zan sake ba... Na tuba na bi Allah na bi ku... Zan bi Fa'iz sau da kafa kamar yadda kike bin Baba, ba zan sake tada muku hankali ba... Ni kaina na gaji, na gaji da wahalar da kaina, ina son mijina yanzu. INA SON SHI Momi...". Banga Momi ba, amma nasan murmushi tayi, (a very deep smile) kasancewarta mai yin murmushi mai fidda sauti. Ta jima bata yi magana ba, daga baya kuma ta yin. "Ki yiwa Abubakar waya, ki nuna nadamarki gareshi. Wannan zai sa shi watakila dawowa nan kurkusa. Amma in ba haka ba, mawuyaci ne yasan hakan, har ya yi marmarin dawowa gareki. Babu kunya tsakanin mace da mijinta, akwai inda ya dace aji kunyar, amma ba a irin nan ba, musamman idan baya ganin ki". Na ce, "Ba zan iya ba Momi, wallahi bazan iya ba, ina jin kunya, ina jin nauyinshi sosai domin sai a yanzu na fahimci abubuwa da yawa wadanda ada ban fahimta ba. Tsiyar dana tsula tana da yawa, tijarata gareshi mai yawa ce, da kyar in zai yarda ya kara hada rayuwa dani...". Na ci gaba da kuka mai tada tsigar jikin mai kaunar ka, musamman UWA! A sanyaye Momi ta ce, "Ai sai kiyi tayi, tunda kinga shi zai fisshe ki. Ki tsaya jin kunya ya dawo da matar dake son shi, ina ce shi kenan ko? 'It's not too late for you to correct your misdeed' ba'a tsufa da tuba muddin ana raye. Mutuwa ce kadai shinge ga tuba da nadamar bawa. 'Atleast ya san kinyi, koda ba zai karba ba... Walida da Kausar duka na nan zuwa". Jikina duka ya saki a yayin da Momi ta kashe wayar. Na kifa kaina cikin kujera na rasa me yake min dadi. A yinin ranar baki daya, na kare shi ne cikin tunanin ceto kima ta a idon Fa'iz da sauran son, in akwai. Yamma lis misalin karfe shidda na yamma, direban Bababn ABU ya sauke Walida da Kausar a harabar gidan. Walida tayi sallama ta aje (trolly) dinsu, ta dube ni duk nayi firgai-firgai dani, tun safe banyi wanka ba ga yunwa, tun kofin ruwan lipton dana zuba ma cikina da safe. Da yake yarinya ce mai hankali bata yi magana ba, gaisheni kawai tayi ta aje mayafinta ta shige (kitchen) ita kuwa Kausar wai wanka zata yi. Uffan na kasa ce masu, ashe Walida girki take yi, sai bala'i kamshi mai tada tsohuwar yunwa naji yana bugun hanci na kafin ince wannan ta aje min (tray) a gabana, (fried-rice) da taji kayan lambu tayi sharr da farfesun koda na tiriri da tashin kamshi. Nayi ajiyar zuciya na dubeta cike da kauna a raina, na ce. "Dan uwa rabin jiki". Na sa cokali na soma ci hannu baka hannu kwarya. Rabona da su tun ranar da Fa'iz ya kore su. Kausar ta fito ta dau wanka ta dau gayu da tirare dai-dai sanda na kammala cin abincin. Ta samu kujera ta hakimce ta kunna t.v tashar 'Bollywood' na galla mata harara na ce. "Inda Walida ta fiki kenan, hankali da sanin ya kamata. Wawuya kawai, kashe talbijin din nan bana son hayaniya". Kausar ta zumburo baki, "Ni fa hutawa nazo yi ba aikatau ba. Tun ranar da maigidan ya koremu ban kara marmarin zuwa gidanku ba. Yanzun ma ba don Momi ce ta takura min ba da banzo ba". Na kama baki na ce, "To yi mana rashin kunya ke da aka turo ki taimakeni mu sada zumunci. Tashi maza-maza ki wanke (plates) din da aka yi amfani dasu da tukwanen, kiyi 'mopping' (kitchen) din ko mu raba gari yanzu-yanzun nan har bakin 'gate' a jiyo mu". Ta mike tana kumburi kamar zata fashe tayi (kitchen) din Walida na yi mata dariya. Na ce, "Lallai Momi tana fama da wannan yarinyar, Allah Yan shiryeta". Walida ta ce, "Ai in tana yi Momi cewa take gadon Fa'izah". Nayi murmushi sosai cikin raina na ce, "Fa'izar da". Da daddare muna kwance a gado daya, Walida Kausar nata barci abinsu cikin kwanciyar hankali amma ni sai juye-juye nake daga wannan gefen zuwa wancan. Na kasa barcin magan-ganun da muka yi da Momi ke cina ta ko’ina, suna babbaka ni. A karo na farko nayi tunanin jarraba shawarar Momi na. To amma in kira Fa'iz ince masa me? Ince Fa'izu Abubakar, yanzu ina son ka? Da wane baki? Da wane harshe? Da wacce siga? Na ciza na hura na kasa samo sigar. Ina cikin rukunin mutanen da basa iya fadin abinda ke zuciyarsu a fatar baki, sannan ni mutum ce mai tsananin kunya da kama kaina. Wata zuciyar ta ce, "Fa'izu ba matsayin miji kadai yake takawa a gareki ba. Dan uwa ne na jini. Ba lallai sai kince sonshi kike ba, 'actions show feelings atimes...". Da wannan shawarar da wannan tunanin na kira Ummi, cikin barci mai nauyi ta daga bayan wayar ta sha (ringing) ta gode Allah. Har bana jin abinda take fadi sosai sai da na harhada na gane cewa take. "Waye?" Ajiyar zuciya na saki mai nauyi, tattare da jin nauyi, na ce. "Ni ce, kiyi