Sashe 55
Zumuntar Kenan Part 1 Complete Hausa Novel · about 4 min read
su Baba ba za suyi fada ba?" "Akan me za suyi fada kai da abinka?" Murmushi yayi ya kalleni ya maida kai ya ci gaba da rubutu, ya kammala ya ninke ya maida bironsa aljihunsa ya mike ya iso har inda nake, ya miko mini. Hannu biyu nasa na amsa kamar wadda aka bawa damin kudi don rashin ta ido har da cewa. "Na gode". Ko da yake ni wannan ta fiye min gida da mota dole in gode in kara godewa. Ya yi murmushi ya dauki hanyar fita, har ya kai bakin kofa ya juyo. "To yanzu kin yafe mini?" Na ce, "Ni me kayi min? Dama auren ne bana so da kai". "Ba wannan nake nufi ba Fa'izah.. Na can baya nake nufi, shekaru goma da suka wuce a gidan Hajjah". Nayi shiru cikin TUNA BAYA...Wai TAKORI ta ce TUNA BAYA SHI NE ROKO. Fa'iz ya wahalar dani da yawa har yadda mai karatu ba zai fahimta ba. Ya ki ni, ya nunan kiyayya, ya nunawa uwata, ya yi mata izgili kala-kala da kalamai na raini a wancan lokacin wadanda 80% su suka rura wutar kiyayyarsa gareni fiye da wanda ya yi min ni kaina. Uwa tafi gaban wasa, haka ba'a hadata da komai, ni tawa mai sauki ce tunda na yar da kwallon mangwaro na huta da guda. Fa'iz ya cuce ni sosai, ya vata min sosai (he so much hurt me heart and soul) ya bata min baka da zuci ta yadda a wancan lokacin har nayi furucin BAZAN TABA YAFEWA FA'EEZ MUKHTAR ABUBAKAR BAMALLI BA! To amma mutumin da ya hakura da auren da yayi don yana so duk da mugun rotsen da ya sha ai ya cancanci yafiyar tunda dai daga yau shi kenan da kyar ma in wata hulda zata sake hadamu baya ga gaisuwar zumuncin da ta zama dole ko a lahira sai anyita. Sai na daga jajayen idanuna na dubi dan uwana Abubakar (Fa'iz) har zuwa lokacin idanunsa akaina yake. Wani irin yanayi ne cikin kwayar idanunshi mai nuna gajiya, damuwa da matsananciyar yunwa wadda ta ci karfin mutum ta nuna cikin kwayar idanunshi. Ban taba ganin Fa'iz ba tun bayan tafiyar shi ko a hoto sai yau, ya kara wani irin girma da kyau da haiba mai ban mamaki. Ya zama (giant) ma'abocin kwarjini da kamala da alamun samun (exposure) na rayuwa cikin kowanne fanni a fararen kwayan idanunshi. Fa'iz ba Fa'iz ba, in ba don halin ba me zai hana ni inso wannan kyakkyawan kammalallen matashi? Na kau da wannan bahagon tunanin na ce cikin taushin murya. "Ka je kawai, babu komai". Fa'iz ya tura duka hannuwanshi cikin aljihu, ya ce a tausashe. "Baki yafe din ba kenan?" "Abinda ya wuce ya wuce a wurina, bana son TUNA BAYA...". Ya lumshe ido, "Har yanzu baki fadi ba da bakin ki Fa'izah cewa kin yafe mini". Na ce, "To Ya Fa'iz, NA YAFE MAKA DUNIYA DA LAHIRA!". A hankali Fa'iz yake lumshe idonsa yana bude su, ya yi shiru ya kasa cewa komai. "Show me in another way... na kasa gasgata kunnuwana Fa'izah". “Like how? (Ma'ana, ta yaya?" Na tambaye shi. Sai ya zaro hannunshi na dama dake sanye cikin aljihun rigarshi kaftan na yadin (filtex) ya miko mini (yana nufin muyi musabaha). Abinda bana so din shi ne ya dawo min, wato TUNA BAYA..., "Ba don komai Baba ke son in tafi ba sai don Mama da ta tsane ni kan shegiyar yarinyar nan Fa'izah!!!" Ban iyawa! Hada hannu da Fa'iz Bamalli... Wani kwayan mutum guda daya da ya takurawa zuciyata a lokacin da bata da kwarin daukar kunci da kuntatawar. Wata zazzafar kwalla ta shiga tsatstsafo min. Fa'iz idanunshi suka kada, jikinshi ya soma dan shaking a sanda yake fadin. "Baki yafe min ba, wallahi Fa'izah yafiyar ki bata kai zuci ba. Akwai abinda baki sani ba, ban taba kin Momi ba, ban rainata ba, kuru... kuruciya ce da yarinta amma babu komi a raina a game da Momi ko da take (outsider) amma na yarda nayi kuskure kuma babu wanda ya san gobe sai Allah, kuma kana naka ne Allah Yana nashi. Yanzu babu lokaci, ina kan uzuri da na baki labarin abinda ya faru tun kafin a haife ki...". Ya tsuguna a gabana ya dora hannu bisa tafin kafata, amma ya kasa sake furta komi, wani ajin yana motsawa yana so ya maida shi Fa'izun shi yana so har gobe har gaban abada kada Fa'izah ta juya shi ko ta ga (week-point) dinshi. (Na yaushe kuma Fa'iz? TAKORI). [18/02 2:48 PM] Sumayya Takori: Sai ya mike a hankali yaja da baya ya juya ya doshi kofa, sai da ya kai bakin kofar sai ya juyo kadan cikin fadin. "Allah Yaji kan NAZIR S.".