Sashe 89
Zumuntar Kenan Part 1 Complete Hausa Novel · about 5 min read
***
Mun wayi gari yau da gingimemen hadari, mai dauke da sassanyar iska, wadda ke kadawa tare da yayyafin ruwa kadan-kadan yaf-yaf akan rufunan gidajen unguwar Malali GRA, wanda hakan ya tada kamshin kasa mai dadi da dadin shaka a hancin kowanne bil'adama.
Dai dai lokacin da nayi wani juyi akan gadona domin gyara kwanciya don karin jin dadin kwanciyar tawa, naji ban zunguri Kausar ko Walida ba wadanda suke kwance gefe da gefe na. Hakan ya sanya ni bude ido sosai tare da tashi zaune. Can na hango su jikin gado suna shirya kayansu kaf a cikin (troller) din da suka zo da ita.
Sosai na wartsake na dube su cikin mamaki, a lokacin da suka gama kintsa kayan suka ja zip suka zuge jakar. Na tashi zaune sosai na ture bargon na ce.
"Ku, lafiya? Ina zaku je?" Walida ta mike tsaye tana gyara lullubin da tayi da mayafin Abaya baka.
"Lafiyar kenan, tafiya zamuyi".
Na ce, "AMma ba haka muka yi da Momi ba, munyi da ita zaku kara sati daya, na rantse daga shi ko kwana daya ba zan ce ku kara ba. Kuji tausayina Walida, kuyi hakuri mu zauna".
Idona ya raina fata, ya kuma cicciko da kwallah.
Kausar ta ce, "Allah ko minti daya ba zamu kara ba, balle yaya Fa'iz yazo ya taddamu a gidan nan ya sake korarmu. Tunda yau zai dawo zaman me zamu yi?"
Da farko ban fahimci me Kausar take nufi ba, abinda na fahimta shi ne Kausar yarinya ce mai riko kamar ni, har yau haushin korar Yayan nata take ji. Don haka cikin lissafina ban lissafa da abinda ta ambata ba sai fahimta nayi kawai bata so ta ci gaba da zaman. Ina wannan harhaden ma'anar ne, Walida ta dora da bayanin da ya warware maganar Kausar.
"Tun karfe bakwai ya kira wayarki, ni lokacin na tashi sai na dauka, Ya tambaye ni yaushe muka zo na ce da shi yau watanmu guda a gidan nan. Ya ce in sanar dake yana bisa hanyar dawowa karfe hudu na yammacin yau. A gayawa Yaya Bashir yaje filin jirgin saman Kano ya dauko shi ta can zai sauka.
Ya ce ina kike? Na ce baki tashi ba, ko in tashe ki in baki? Ya ce in kyaleki kiyi baccinki, amma in gaya miki sakon".
Jina nayi kamar ina yawo akan gajimare, cikin wata alkarya ta madara da zuma saboda dadi, farin ciki, godiyar Ubangiji, murna. Sauran abinda naji a cikin zuciyata a lokacin (unexpressable) ne. Ciki kuwa har da faduwar gaba da bugun zuciya. Wanda suka fito a tare da farin cikin, murna da godiyar Ubangijin suka saukar da wata irin nutsuwa da salama cikin zuciyata.
Na lumshe ido a hankali. Ina rokon Allah a zuci idan mafarki nake kada Yasa na farka sai nayi tozali dashi din. Koda cikin mafarkin ne. Sai kuma na soma jin motsi cikin kaina, mai cewa in tashi in taka rawa, inyi juyi, in kuma rungume 'yar uwa shakikiya da ta kawo labarin, in bata tukuici da duk abinda na mallaka.
Maimakon hakan, sai na mike na sanya hijabin sallah ta dake bisa darduma, wanda nayi sallar subhi dashi dama da alwalata, na sauko na dungura goshina gaban Subhana, na tsarkake shi, na tsarkake tsarkin mulki da iyawarsa!
Duka walidar da Kausar suna kallona, sai suka kama yi min dariya suna tambaya.
"Duka farin ciki ne Yaya Fa'izah?"
Ban iya na tanka musu ba. Na lula a wata sabuwar duniyar ta daban, ta tunanin wacce irin tarba zan shiryawa Hafizin Hajjah? Fa'izun gidan Baban Kaduna? 'The one that is always hunting my dream?' Wanda tunanin ranar dawowar tasa ke zuwa min a farke, wato (ido biyu), cikin barci, ranaku da darare guda casa'in da nayi ba tare da na sanya shi cikin idanuna ba? A yau ga ranar tazo, 'so it will be a hectic and busy day; that needs planning and coordination'.
Na daga ido a hankali na dube su ina murmushi wannan karon, wani irin murmushi da bana jin na taba yin ni'imtaccen sa a rayuwata.
"To ai tafiya bata ganku ba, ajiye mayafin za kuyi ku tayani aiki ko? Mu gyara gidan, mu yiwa maishi girkin sannu da zuwa. Kuyi min kwalliya irin wannan da kuka caba, mai 'eye-shadow' da mascara, jambaki da lip gloss, ko 'yan matana?"
Walida ta saki dariya, Kausar kuwa zumburo baki tayi da ya sha AVON lipstick yayi jajawur, Walida na fadin.
"Kin burgeni Yayata, baki taba sa ni farin ciki irin na yau ba. Allah Yasa ki dore da hakan, Yasa ki cigaba da hakan har zuwa karshen rayuwar ku, ko mu ma 'yan baya ma yi koyi dake ko?"
Murmushi nayi cikin matsanancin nishadi, "Sai kuyi ta addu'a ya yarda ya amshi tuban nawa, ba kwa ganin yadda yayi 'deleting' dina 'from the screen of his sight and mind?"
Walida murmushin tayi itama, “Ni na gaya miki zai yafe miki, yana sonki yadda ba kya zato. Idan daso kuma ba aibi, sai dai 'FUSHI' wanda ba inda yake zuwa. DOn baki san me ya ce min dazu ba".
Na kamo hannunta da sauri na zaunar a kusa dani.
"Me ya ce miki Walida? Eye, gaya min? ".
"Cewa yayi "Gyara mata bargon rufar garin da sanyi, tunda ruwa ake". Da na duba sai naga da gaske bargonki ya yaye daga kafafunki, na gyara miki. Ya ce, "Kin gyara?" Na ce, "Eh". Sannan muka yi sallama. Don haka zai fi kowa farin ciki da kika gane kuskurenki, ki ka amshi laifinki. Ki ka kuma yi dammarar gyarawa.
Na lumshe ido a hankali ina mai gasgata kowace kalma dake fita daga bakinta.