Sashe 50
Zumuntar Kenan Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
*****
A GIWA
Acan Gida babu wanda ya farga da rashina a gidan har garin Allah Ya waye, duk jama'ar gidan baqi da 'yan gidan kowa harkar gabansa yake yi, ana ta shirye-shirye. Musamman kasancewar ranar ta Alhamis a matsayin ranar buxar kai.
Aliyu ne ya shigo falon Hajjah tare da xan uwanshi kuma babban abokinshi, wato Muftahun Yaya Rabi da ya zo a lokacin don su gaisa da Hajja, isowar shi Giwa kenan.
A babban falon dake shaqe da A.B family maza da mata, Muftahu ya zo ne da labarin rasuwar Dr. Nazir Sani Galadanci, manemin auren Fa'izah.
In banda Salati babu abinda Yaya Aliyu keyi yana mai qara jinjina wannan mummunan labarin, tare da qara tsinkewa da al'amarin Ubangiji.
Muftahu ya nemi ganina don yi min bayani, Ummi dake kokawa mutuwar Naziru haiqan har kamar ta shixe ta yarfe hawaye da majina, ta ce.
"A wannan halin da Fa'iza ke ciki ne zaka ba ta labarin rasuwar Dr. Nazir Yaya Muftahu? Ka rufawa kanka asiri, idan Fa'izah bata ce kai ka kashe mata Nazir ba, la-shakka zata ce haxa baki ku kayi aka kashe Naziru don ta yarda da auren Ya Fa'iz".
Muftahu ya ce, " amman dole ne ta ji?"
Ummi ta ce, "Ji kam ya zama dole ko ba jima ko ba daxe, amma ba yanzu ba, kuma ba daga bakin kowa ba sai na wanda zai iya ma haukar Fa'izah tamkar Yaya Aliyu ko Ya Rabi, amma ba kai ba".
Da sauri Aliyu Na'ibi ya ce, "Wallahi babu ruwana, ba a bakina ba nima, indai har ka dage sai ka faxan Muftahu ga hanya, tana uwar xakinsu tana neman kashe kanta don bala'i da qin auren Fa'iz ko falo ba ta fitowa".
Muftahu ya ce, "Bari inje, inji dai ba zata bugeni ko ta zage ni ba?" Suka ce a tare, "Uhm!".
Hajja ta ce, "Muftahu ka qyale Fa'izah don Allah, shin Fa'izar da ta rufe ido ta zageni tas kan Naziru kai waye da bazata zage ka ba, zaka je mata da labarin mutuwar Nazirun?"
Muftahu bai tsaya ba a yayin da ya danna kanshi a xakin bakinsa xauke da qatuwar sallama.
Ya yi dube-dubenshi ya fito, ya ce.
"Au, ai ma bata nan".
Ummi ta ce, "Ko dai ta shiga bayan gida?"
Ya ce, "Ga bayan gidan nan a hangame, ai babu kowa a ciki".
Ta ce, "Duba sosai dai can qarshen gado ko ta naxe cikin bargo".
Muftahu ya yi dube-dubensa har da duba qasan gado ya kuma haxa da kira.
"'Yar Zaria a Kano!!!".
Shiru ta ziyarce su, sai ma amsa kuwwar muryarsa da ta dawo cikin kunnensa.
Ya ce, "To wataqila dai idona ne, Aliyu zo ka duba".
Baki xayansu suka miqe suka shiga xakin inda Fa'izah ta ce xaukar ni inda ku ka ajeni.
Zaneera sai da ta qara shiga (toilet) ta duba bayan qyaure da cikin baho, ta ce.
"Kai! Tikisa!! Da qyar fa idan Fa'izah na cikin xakin nan".
Leqa nan leqa can cikin A. B Estate baki xaya babu Fa'izah.
Hajja ta tuna kalaman Fa'izah.
"Daga yau ba za ki sake ganina cikin gidanki ba balle ki yi iko da ni...".
Hajja ta fashe da kuka tana faxin.
"Ni Dijah na shiga uku, wace irin zuciya ke da yarinyar nan wadda babu ahuwa da rangwame a cikinta? Tabbas Fa'izah ta gudu ne, ba ta gidan nan, ba ta garin nan".
Zaneerah ta ce, "Ina! Babu inda Fa'izah za ta iya zuwa da ya wuce Kaduna, Kano ko Zaria. Bayan waxannan wurare na tabbata Fa'izah ba zata yawon banza ba, kuma ba zata kai kanta mahalaka ba duk rintsi duk kuwa abinda ke damunta".
Aliyu ya zaro waya daga aljihunshi, haka Muftahu.
Muftahu Aunty Rabi ya kira, ya ce.
"Maman Abdul 'yarki wurin ki ta iso ko?"
Ta ce, "Wacce 'yar tawa Mufty? Kasan 'ya'yan nawa yawa ne da su".
"'Yar rigima mana matar Fa'izu!".
Da fari Rabi kam dafe qirji tayi kafin ta ce.
"Ni Rabi'atu, rabona da Fa'izah tun ranar da suka haura qafa suka bar Kano, amma gani nan tafe. Nima shirin kayana nake yi yanzu haka".
A sanyaye Muftahu ya zura wayarsa a aljihun gaban rigarshi, ya ce.
"Fa'iza ba ta Kano fa".
Zanira ta fashe da kuka, "Ni kam wannan aure dole ne? Me ya yi zafi ne haka da ba za a haqura ba? Wallahi ni nasan Fa'izah da kafiya da taurin zuciya, tunda ta ce bata auren nan wallahi bata yi xin ne, babu wanda ya isa ya tanqwasa ta".
Cikin alhini Aliyu ya ce, "Haka Fa'iz Giwa, tunda ya ce bai sakin auren Fa'izah yanzu ya saka xamba a aurenta, na tabbata ko duniya zata taru akansa ba zai saketa ba, sai dai mutuwa ta raba su
A wannan gava ni na saduda Hajjah, dabarata da tunanina sun qare wajen tanqwasa Fa'izah tunda har anzo gejin da Fa'izah ta soma zartarwa rayuwarta hukunci ba tare da shawara dani ba, ya tabbata cewa nima ta sanya ni a rukunin sikelin da ta xora kowa. Sai ki yanke hukunci na qarshe, in har bata Kaduna ko Zaria".
Yana faxi yana kiran Maman Kaduna.
Ita xin ce ta xaga suka gaisa cikin matsananciyar girmamawa ta 'ya'yan A.B ga iyayensu maza da mata, Aliyu nauyin Mama ya dabaibaye shi, shin yaya zai yi ya tambayeta yarinyar da ta bar gida domin qiyayyar xanta? Jikinshi na bashi yaqinin ba yadda za ayi Fa'izah taje Kaduna, shin giyar wake ta sha ma?
Ya yi ta maza jin shiru ta ratsa a tsakaninsu, ya ce.
"Shin Mama ina Pilot ne?"
Ta ce, "Yana vangarensa yana shirya kayansa, wai shirye-shiryen tafiya yake yi jibi can Russia, anyi masa kiran gaggawa kan wani muhimmin aiki. Yaya Fa'izar? Ince ko ta ware?"
Gaban Aliyu ya bada damm! cikinsa ya ba da sauti, ya ce.
"Don Allah Mama yi min magana da shi yanzun nan ko Yaya Bashir".
Mama ta ce, "Na ce lafiya dai? Bashir yana kan hanyar tahowa na san ma ya kusa isowa yanzun, ka gaya mini mene ne? Me ya faru Aliyu?"
Tausayin Mama ya kama Aliyu, daga jin muryarta kasan ta daxe bata cikin nutsuwa da kwanciyar hankali duk akan Fa’iza. Aliyu ya rasa yadda zai yi don ta wuce ya yi mata qarya, ya ce.
"Wallahi Mama Fa'izah ce bata kwana gidan ba, gamu nan a Giwa kowa hankalinsa a tashe".
Mama tayi murmushi mai fitar da sauti, ta ce.
"Ina da kyakkyawan zato da shaida akan xiyata, ba zata iya wuce Zaria zuwa Kano ba duk nisan da zata yi".
Ya ce, "Wallahi bata Kano, yanzu Ya Rabi ke faxa".
Mama ta ce, "Ka jarraba Zaria mana. Yanzu kam bai kamata mu faxawa Fa'izu ba tunda Zariyan yake shirin zuwa gaida Maimuna wataqila ya tadda ta can".
Aliyu ya sake neman gidan baban ABU, momi ce ta xauka suka gaisa tana tambayar Little F. Aliyu kam duk gaisuwar ta gundire shi, ya ce.
"Shin momin Walida, please Fa'izah Zaria ta kwana?"
Da farko Momi Maimunatu shiru tayi sakamakon mugun faxuwar gaban da ya dirar mata. Ta samu ta haxa sauti wanda zai ba da ma'ana, ta ce.
"Ko da zancen nan bai shafeni ba Aliyu da Fa'izah ta zo gidan nan da tuni na sanar daku ko don gudun tashin hankalin ku. Rabona da ganinta tun zuwansu daga Kano da suka zo suka kwana biyu nan ita da Ummi".
Aliyu ya ce, "Ya Salam!!".
Tare da tura wayarsa a aljihun baqin wandon (jeans) mai matuqar qwari dake jikinsa.
Ummi ke tambayar, "Bata je ba ko?"
Sai kuka, kazalika sauran 'yan uwa da 'yan buxar kai da suka ci kwalliya kyawu na bugun kyawu, duk hawaye ya vata kyakkyawar fuskar Bamallin su. Muftahu kam girgiza kai yake.
Ali Na'ibi, ya jingina da bango, yayin da maganganun da suka yi da Fa'iza ke nausar kunnensa tamkar a lokacin ne take yi.
"...ko yankani za kuyi A.B bani auren nan... na gwammace in bi YAWON DANDI... da dai in qarashe rayuwata a matsayin matar FA'EEZ BAMALLI!!!".
Aliyu ya kama kai, ya ce, "Kash! Kinyi kuskure babba Fa'izah, ko masu yawon dandin basu da aure akansu, kada kiyi kuskuren da ba zaki iya gyarawa ba mana...".
Ya fisgi hannun Miftahu suka yi waje inda ya xauki motarshi aguje suka bar garin Giwa.
Allah Sarki Aliyu xan uwa na gaskiya, gidan karuwai ya riqa bi kala-kala da Miftahu wai yana neman Fa'izah, yana mai suffanta musu ita tare da nuna hoton ta. Amma babu wanda ya ce ya ga gilmawar ko mai kama da Fa'izah, amma babu alamar gazawa a tare da shi.
Miftahu kam ko fitowa daga mota bai yi ba, tausayin Aliyu kaxai ya ishe shi.
Haka ya zage gidajen karuwan garin Kaduna da Zaria kaf yana cigiyar Fa'izah har duhun dare ya shigo, ya ba da cigiya a ofishin 'yan sanda da kafafen yaxa labarai masu yawa.
Ya ja birki dai-dai titin Sir Kashim, ya xaga waya ya kira Fa'iz Giwa, a fusace Aliyu ya ce.
"Ka ji daxi ko xan gata! To tunda baka fasa auren nan ta ruwan sanyi ba, zaka fasa in an kawo maka gawarta. A yanzu Fa'izah kwata-kwata bata a Kano, Giwa, Zaria ko Kaduna, sai ka san inda zaka nemo ta".
Bai bashi damar yin magana ba ya kashe wayarsa, shi kuma bai kira shi ba.