← Book details Zumuntar Kenan Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 5 OF 98

Sashe 5

Zumuntar Kenan Part 1 Complete Hausa Novel · about 7 min read

juyowa sannu a hankali ya dube ni na ‘yan dakikai, sannan ya sanya ma motar giya muka harba kan titi. Babban Super Market din wanda ke kan hanyar fita garin Giwa kusan duk garin babu kantin da ya yi girma da habakar ta. Babu abin da babu na bukatun yau da kullum. A nan Ali ya yi parkin duk suka fita, ban ko yi motsin dake nuna inada niyyar fitan ba, zuciyata da tunanina duk da karancin shekaruna sun sanya min ayar tambaya a yau a kan Yaya Fa’iz da kiyayyar da yake yi mun da kuma dangantakar kiyayyar da raini ga mahaifiyata wadda baya jin kunya ko haufin jan sunanta a gaban kowa ya aibata ko ya zage ta. Mintuna biyu Yaya Ali ya yi yana nazarina kamin ya rankwafo tagar da nake a tausashe ya ce, “Fa’izah ba a fitowa?” Sai na ji ya yi min wani kwarjini mai yawa yadda ya yi maganar. A hankali na bude murfin motar na fito. Ya yi dariya ya ce, “Yau dai da alama mulki kike ji Fa’iza, ko duk fushin Fa’iz ne har yanzun?” Ummi ta kulu da bata lokacin da nake yi musu da tarairayar da Yaya Aliyu ke min na yi banza da su, ta ce, “Don Allah Yaya Ali ka rabu da ita sai wani lallashinta kake tana basarwa sai ka ce mu muka kar zomon, ita wace ce?” Ya yi murmushi ya ce, “Ita Princess Fa’izah Bamalli ya ya ranki?” Zanirah ta ce, “Me kenan Pincess?” Ya ce, “Princess yana nufin Gimbiya”. Ta tabe baki ta ce, “Sunan da Ya Fa’iz ya ba ta ya fi dacewa da ita ba naka ba”. A kaikaice da baki ya ce, “Wanne suna ne Fa’iz ya ba ta?” Zanirah ta ce, “Impertinence Fa’izah watau Fa’izah mai tsiwa”. Ya dubi Zanirah sannan Ummi, ya ce, “Wadda ta sake kiran Fa’izah da wannan sunan ban yafe ba, kun ji ko?” Suka daga mishi kai muka shiga cikin kantin. Ko da muka shiga cikin kantin kujera na ja na zauna ina kallon su, dauki banza dauki wofi, wani zubin su juyo su kalle ni suyi kus-kus su ci gaba da dauke-dauken su. Shi ko Yaya Aliyu sayayyarsa daban ce da tasu, kwando uku suka cika da kayan zaki masu tsada, hatta biron da zamu yi rubutu basu bari ba. Muna shiga mota kafin Yaya Ali ya tada motar Zanirah ta ce, “Ummi baki daukarwa impertinence rice pudding ba”. Na yi kan Zanirah da duka, yakushi da cizo, dama kiris nake jira. Yaya Aliyu ya dakan tsawa ya ce, “Meye haka ne Fa’iza? Don kinga ina lallaminki shine kika koma hauka?” Idona cike da kuka na ce, “Amma ita ba ka yi mata fadan sake kirana da sunan Yaya Fa’iz ba don kaima ka tsane ni kamar shi, shi kenan....!” Sai a lokacin ne na samu hawaye suka zubo. A tausashe Yaya Aliyu yana ta da motar ya ce, “Lallai Fa’iza har yanzu shagwabar tana nan? Haka za a kwalejin ana musu?” Ummi ta ce, “Ta yi mana in siniyoyi basu lallasata ba?” Muguwar harara na rafka mata ta toshe bakinta da hannun damanta tana “Allah ya huci ran princess”. Mun kusa shigowa unguwarmu ya ce, “Fa’izah don Allah don Annabi ki dinga hakuri da ‘yan’uwanki kin ji ko? Ko harshe da hakori dole a saba wata rana, ki rage zafin zuciya, kina da zuciya mai zafi”. Na ce, “Amma shi Ya Fa’iz ba mai yi masa fada kan tsana da tsangwamar da yake yi min a duk lokacin da abu ya shafe ni? Laifina ma kake gani Yaya Aliyu?” Yana girgiza kai ya ce, “Ba maganar Yayanki Fa’iz nake ba, bana so in ga kina halin yara, you are no more a child now, dambe da kokawa na su Walida da su Badar ne”. Na zumbura baki ban ce komi ba. Ya ce, “Kin hakura Princess ko kina so na kasa barci saboda fushinki?” Sai na bude dukkan idanuwana na dube shi. “Yanzu Yaya Aliyu in ina fushi sai ka kasa barci?” Ya yi murmushi ya lumshe ido tare da daga kai sama. Cikin mamaki na ce, “To saboda mene?” Ya ce, “Saboda me? Saboda abin da kwakwalwarki ba za ta fahimta ba a yawan shekarun ki”. “Mene shi wannan abun?” “Wannan abun muhimmi ne mai girma da yaro baya jin shi sai ya girma”. “To ai Zanirah ta girma in ji Hajjah, tun ranar da jini ya ziraro ta kafarta Hajja ta ce ta girma, to ita ka gaya mata mana?” Ya yi dan dummm! Zanirah ta soma kumbura hanci da hurashi ta ce, “Yaya Aliyu wallahi karya take Ummi ce?” Ummi ta ce, “Wallahi ita ce”. A dai-dai lokacin da Yaya Aliyu ya shigar da hancin motar A.B Bamalli Estate, ya yi kyakkyawan horn yaran dake kusa a kofar flat din Baba Barau suka rugo suka fidda kayan a boot suka shigar mana dasu gida. Yaya Aliyu Boys Qtrs dinsu ya wuce bai kara kula mu ba. Su Abba na jidon kaya suna ihu wai za su ci cornflakes din ‘yan bording school. Na ce, “Wallahi duk wanda ya bude mana kaya sai na kabari ya fishi jin dadi”. Ina kwance gadon Hajja na ji shigowar su Ummi, suka shigo da kaya niki-niki, Ummi cike da tsegumi take ce da Hajjah, “Wai Hajja ki duba ki ga duk yawan kayan nan da muka shigo sai da Yaya Aliyu ya sake sayen kwatankwacinsu wa Fa’iza ita kadai ranta”. Zanirah ma ta ce, “Kuma Hajja baki gani ba, wai don dan fadan nan da Ya Fa’iz ya yi mata dazu kafin mu fita ya yi ta lallaminta tana masa wulakanci da kada ido, ita ba ta yarda ba babba”. Hajjah ta yi kamar ba ta ji su ba ta shiga duba kaya, ta ce, “Ya ban ga kwaki ba bayan kun ce bakwa son wanda na sayo fari kuke so?” Ummi ta ce, “Tab! Waye zai sha miki kwakin? Ki jimu da tsohuwa da neman ta da zaune tsaye”. Hajjah ta dauki mafici ta yi kanta ta runtuma da gudu. Hajjah ta ce, “Ja’ira, gobe dai kun barni da ‘yan jikokina mu huta bakinmu alaykum. Haba! Yara uku duk kun bi kun isheni kamar ina zaune da zaratan ‘yammata”. Ummi ta zo ta kwanta a gefena ina kwance rigingine na yi nisa cikin tunanin irin kulawar da Yaya Aliyu ke yi mani. Hakika shi dan’uwa ne mai matukar kirki da dabi’un kyakkyawar mu’amalar zumunci. A lokuta da dama ina kwatanta kirkin Aliyu da wani cikin yayyenmu, amma ban ga kwatankwacin shi ba. Halinsa daban, simplicity dinsa daban da dukkan mazan zuri’armu. To amma kulawarsa gareni ta zarta wadda yake yiwa kowa, babban misali su Zanirah da tare muke rayuwa yana fifitani a kansu. Sai a hankali nake jin Yaya Aliyu na kwanta min a zuciya saboda kyawawan halayensa da kulawar da yake yi mun. Tunani na ya gangara ga abin da ya fadi dazu na cewa, wai ba zai iya barci idan ina fushi da shi ba, saboda abin da yaro baya ganewa sai ya girma. Shin mene ne wannan abun? I’m quite curious.... Kamar Ummi ta san abin da nake tunani, ta yi murmushi sai cewa ta yi, “Princess har an soma tunanin Yaya Aliyu? Ayi hakuri dai muje kwalejin mu gama, in kuma auren za ayi sai a fada mana mu fara shiri”. Na mike a fusace na soma dukanta ina yakushinta ta sa ihu, nan da nan Hajja ta shigo za ni na zamewa kamar ta fadi. Ta ce, “Wai ke wacce irin masifaffiyar yarinya ce ne Fa’iza? Ke daya duk kin buwayi gidan nan, daga ki yi da wannan sai ki koma ki yi da wancan?” Na sa kuka na ce, “Hajjah cewa fa ta yi wai ina tunanin aure, ‘yar iska ta dauke ni ko me? Bayan ni tunanin su Walida nake yi”. Hajjah ta ce, “To yi hakuri wasa take miki, ke kuma Ummi kada na kara jin makamanciyar wannan maganar ta fito daga bakinki zan saba miki fiye da zaton ki”. Ta juya ta fita. Zanirah ta bimu da kallo kurum, sai dai na lura tun shigowar ta dakin akwai abin da ke damun ta.
Chapter 5 · 0% Book details