← Book details Zumuntar Kenan Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 32 OF 98

Sashe 32

Zumuntar Kenan Part 1 Complete Hausa Novel · about 1 min read

bakin ciki ce da duk wani ci gaban FA’IZ GIWA kamar yadda yake a gare shi shima. A daren Ummi hanani barci ta yi da labarin hirarta da Fa’iz. Da hanzari na taka mata birki.... “Excuse me please. Shin Ummi ina ruwa na ne? Me ya shalle ni cikin wannan al’amarin naki? A duk lokacin da za ki yi hira, ki yi wadda ta shafe ni ban da ta Fa’iz! Na tsani Fa’iz!! Na tsani duk wani abu da ya shafe shi ban da iyayen da suka haife shi da ‘yan uwansa wannan (Individualistic matter) ne (sha’anin mutum daya). A duniya bani da abin ki, abin tsana, abin neman tsari da kariya daga sharrin sa bayan shaidan, sai Fa’ezz Bamalli”.
Chapter 32 · 0% Book details