Sashe 33
Zumuntar Kenan Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
****
Washe gari karfe goma na safe Queen Amina College ta yi mana, inda muka hadu da malamanmu da muka jima bamu gani ba. ALHAMDULILLAH, takarduna sunyi kyau har fiye da na Ummi, na tashi da Credentials a gaba dayan ( 9 Subjects) dina. Ummi tana da seven credits, sai dai tana da A a Fine-Art.
A shekarar duka muka samu gurbi a jami’a, inda Yaya Aliyu ya samarwa Zanirah gurbi a jami’ar Lagos (UNILAG), inda za ta karanci likitanci (Medicine). Daga Baba na har mahaifin Ummi babu wanda bai yi mamaki da umarnin Hajjah ba na ta amince a nema mana gurbi a jami’ar Bayero ni da Ummi mu koma Kano da zama wajan Aunty Rabi, sai hutun karshen kowanne zango ta amince mu je Giwa da sauran garuruwan Zaria ko Kaduna.
Yaya Muftahu shi ya shiga ya fita ya samar mana gurbi a fannin da kowacce take so, inda aka bani B.A Arabic, Ummi kuwa B.A Hausa. Duka a Faculty daya wato (FAIS) sai dai tsangaya (Department) da suka bambanta.
BAYERO UNIVERSITY KANO
Rayuwar mu cikin jami’ar Bayero, sabuwar rayuwa ce a garemu da ta zo da sabon salo irin na kowanne JJC (Joiny Just Come) a jami’a. Abubuwa da yawa (which are normal) ga sauran daliban jami’ar (is abnormal to us), irin su shan hannu da maza da wasu matan marasa kamun kai ke yi da sunan jami’anci, shan taba sigari da samari da matasa ke yi wanda ba a yi sam a A.B Estate. Shan lemo a shago a tsaye ga matan aure da ‘yammata, ko saka wando ga wasu matan Hausawa duka abin kallo da waiwaye ne a gare mu kafin mu saba.
Mu kam bamu saba gani ba a inda muka taso, don haka muka shiga dari-dari. Sannu a hankali idonmu ya zo ya bude tangarau muka fahimci (reality) na rayuwar jami’a ba (peer group infuluence) bane (koyo abokan karatu ko tsararraki) kawai (imitation) ne wato (kwaikwayo) ‘to fit together’ (a zama iri daya).
Akwai wadanda karatu ne ya kawo su ba (imbibing) wato kwaikwayon abubuwan da canjin zamani ya kawo ba. Akwai kuma ‘yan ‘imitation’ din ko da a ce ransu bai so don kar a ce musu kauyawa. Irin wadannan su nake gani a matsayin kauyawa ba wadanda suka kalla a kauyawan ba. Su kuma ina kallon su ‘yan ra’ayin rikau. Irin wadannan mutanen a duk inda suka tsinci kansu basa canza ‘doctrines and principles’ dinsu kuma da wuya a rinjaye su daga kan abin da suka riga suka yarda da shi.
Yau bamu fito lacca da wuri ba sai wurin karfe biyu na rana, in ban da kururuwa ba abin da cikina ke yi, don ko karin kumallo ban dauka ba. Babu yadda Yaya Rabi ba ta yi dani ba don in zauna in karya amma na ki, saboda sanin halayyar Dr. Ramadhan Alkali, muddin ya riga ka shiga aji to ka rasa laccar sa kenan. Ni kuma ba zan so in rasa laccar ba, don a cikinta ne zai fadi (exam concentration area) din kwas dinsa.
Tafe nake a hanzarce don kokarin isa ga ‘coke village’ in samu abin da zai warware min hanji. Idanuwana sun rufe saboda yunwa ban kula da budurwar dake tsugune tana goge takalminta da ya yi kura da tishu don ganina ya dushe tsabar yunwar dake addabata, muka yi karon ba zato da budurwar saura kadan ta kifa.
Ta mike a hanzarce za ta yi bala’i. Wa zan gani? Haulatu Shehu, kawarmu (Head-Girl) a Queen Ameena, Haulatu S. Shehu. Na ce, “Haulatu Sani?”
Ta ce, “Fa’izah Ahmad?’
Na ce, “Ya Jamilal Munzar! (wato ya mafi kyawun masu gani)” A guje muka sheka muka rungume juna tare da juyi rikija-rikija muka rankaya coke village tare. Hirarraki da tambayoyi tamkar su kashe mu. Kamin wannan ta kai aya wannan ta antayo tata tambayar.
Ta ce, “Fa’izah kuna cikin garin Kano amma ko ki neme ni?”
Na ce, “Ayya Haulatu, ban san gidanku ba, kin ganni nan bayan unguwar su Aunty Rabi Gadon Kaya (Yarda Avenue) ban san ko ina ba, ban da kantuna da muke zuwa sayayya”.
Ta ce, “Ina address din da na baku tun muna makaranta da phone no?”
Na ce, “Mun baro su cikin littafinmu a Giwa”.
Daga nan hira ta barke. Ta ce, “Lallai ne Ubangijinmu ke nufin mu da zumunci tunda har ya sake hadamu a nan. Allah abin godiya. Ina Ummi?”
Na ce, “Ummi tana makarantar nan ita ma a Hausa Department”.
Ta ce, “Ni ina Mass-Communication, kai ni Haulatu na zo jami’a a sa’a tunda na kara haduwa daku. Tun rabuwarmu babu ranar Allah da za ta fito ta fadi ban tuna ku ba”.
Na ce, “Duk kin canza Haulatu, kin yi kiba kin kara kyau da haske, ko kin yi aure ne?”
Ta ce, “Har da albarkarsa na like jikina. Matar Abdullahi Yakasai ce. An daura min aure bayan candynmu. Bikin ne dai ba ayi ba har yanzu Abdullahi ya tafi (Law School) sai ya kare nan da wata shida”.
Na ce, “Sunan kanina, Allah ya sanya alkhairi Haulatu. Sunan kanina mai bina kenan”.
Ta ce, “Kwarai, kin taba gaya min kina da kani Abdallah, yanzu ajinshi nawa?”
Na ce, “Abdallah ai an zama samari, yana SS I, Walida na JSS 2”.
Ta ce, “Me kike karanta?”
Na gaya mata harshen Larabci. Ta ce, “Kin burge ni Fa’izah, Allah ya kara fahimta, ya kara mana kaunar Manzo (S.A.W)”.
Kai hirar da muka kwarara ni da Haulatu a ranar tana da yawa. Duk tarihin mijinta Abdullahi wanda ya kasance dan’uwanta ne ta bangaren mahaifiyarta sai da ta gaya mini. Sai da muka yi (missing) lacca guda saboda dadin hira, dama Haulatu uwar surutu ce barin in sun hadu da Ummi. Haduwar Ummi da Haulatu sun kusa shidewa don murna.
Daga ranar amintarmu ta ci gaba da Haulatu daga inda muka tsaya a sakandire school. Naja’atu na ABU Zaria in ji ta. Duk inda ka ga Zarah ka ga wata wato ni, Ummi da Haulatu. Mun je gidansu a ‘Yankaba ba sau daya ba, ba sau biyu ba, ita ma ta zo mana, har kwana take in lokacin jarabawa ne mu yi karatu tare, musamman da gidan Aunty Rabi ya fi kusa da makaranta. Ta saba da Aunty Rabi sosai.
Albarkacin Haulatu babu inda ba ma takawa a cikin Kano, daman an ce sai da dan gari a kan ci gari. Ummi ta yi manema har ba adadi, ni kuwa rashin sakin fuska da kora da hali wanda ya fi kora da sanda shi ya sanya duk wanda ya zo wajena da sunan so baya marmarin sake dawowa.
Ummi kan ce lokaci ne, lokacin abu ayi shi. Ni ba auren su zan yi ba kawai suna rage min lokaci. Sai in kama baki in yiwa Ummi kallon mamakin yadda jami’a ta sauya ta lokaci guda.
A haka muka kare 100 level bayan jarrabawar da ta kusa tsaga mini kwanya muka fara 200 level. Idon mu ya kara budewa sosai a sanadiyyar ratsawar ilimi da cudanya da masu shi. Hausar bakinmu ta dai-daita da ta ‘yan Kano, kai ka ce nan ce mahaifar mu.
Mu muna using N a muhallin R, wannan shi ke sa Haulatu da sauran abokanan karatunmu ke cewa muna Hausar Giwa. In Haulatu ta tashi tsokanata sai ta ce, “Kin tuna Ummi ranan nan a anguwan sarki? Ba za ku bar wannan maganan ba? Yaya Rabi kin ga Ummi na tsokanana ko????”
****
[13/02 6:26 PM] Sumayya Takori: Ranar litinin din nan rana ce da ba zan taba mantawa da ita a tarihin rayuwata ba, domin wani dan karamin bangare da ta taka cikin tarihin nawa. Na shigo aji a makare ainin domin sai da muka biya muka ajiye Yaya Rabi a asibitin Malam wajen awon tsohon cikin da take dauke da shi, muka kuma mai da ita gida sannan Yaya Mufty (sunan da Yaya Rabi ke kiran mijinta Muftahu) ya kawo mu ya ajiye ya koma (office).
Jikina har bari yake domin na ji jiya ‘yan ajinmu na fadin anyi sabon lecturer mara daukar wargi, madadin Farfesan dake daukarmu darasin. Sanye nake da shudiyar danyar atamfa (exculusive) mai ratsin ruwan hoda da mayafi launin sararin sama mai haske. Bayan wannan babu komai a fuskata sai farar powder da na muttsika da vaseline (lip balm) a siraran labbana wanda ya kara musu taushi da kyalli.
A rayuwata bana rabo da zizara kwalli a idanuna, kwallin (kajal) baki yana kara lafiyar ido, yana kuma kara fiddo min da gazar-gazar din gashin idona.
Ina kokarin zama a kujera ya ce, “Get out please..... (fita waje don Allah)”.
Wata kunya ta taso ta lullube ni ganin yadda idanuwan maza da matan ajin ya dawo kaina. Malam ya sake daga murya ganin na yi kasake! Na kasa zama na kuma kasa fita. Ya ce, “Get out I said (fita na ce)”.
Na daga ido cike da kwalla a hankali na dube shi. Baki ne mai kyau na a buga a kalanda ko ayi tallan advertisement board da fuskarsa. Bai da tsayi can-can, yana tsaka-tsaki. Fatarshi goge da zuzzurfan ilimi a kananan shekaru. Gwiwoyina suka sage tamkar an rarrade su da murfin kwano haka na cira kafa kamar kazar da kwai ya fashewa a ciki na yi tattaki a hankali na bar ajin.
Wani abin mamaki sai ya kasance ban ji haushin mutumin nan ba a bisa korar karen da ya yi min a kan lattin awa daya. Sai ma haushin kaina mai tsanani da na bar Yaya Muftahu ya fara kai Yaya Rabi awo maimakon ya fara kawo ni.
Haka nan na samu kaina da gwada yadda yake magana a sarke “get out.... get out I said!” Na yi murmushi na kwashi takarduna na yi (main library) don in yi assigment maimakon in zauna zaman tunanin malami mara daukar wargi, mai magana a sarke da in’ina.