← Book details Zumuntar Kenan Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 27 OF 98

Sashe 27

Zumuntar Kenan Part 1 Complete Hausa Novel · about 3 min read

“Ban san abin da ke damuna ba, amma kamar son Yaya Aliyu nake in na yi la’akari da yawan tunaninsa da nake da mafarkinsa cikin barcina, da kwadaituwa da son ganinsa akai-akai. Me kenen hakan ke nufi?

Sai na shiga bude sauran shafukan a gurguje. Duk yawanci abin da ya shafi kuruciyarmu ne. Sai wani da ya dauki hankalina wanda kwanan watan ya tabbatar min Zanirah ta yi rubutun ne ranar 10/10 wato ranar da muka je Area One ni da ita (Zaria).

“Dole ne in yi jihadin fitar da Yaya Aliyu a raina, domin ina son shi ne a yayin da na fahimci zuciyarsa, rayuwarsa, ruhinsa da gangar jikinsa sunyi nisa a soyayyar ‘yar’uwata (Fa’izah.) Fa’izah da zumunci basu cancanci in yi tarayya dasu a son komai a duniya ba. Yadda nake son Fa’izah bana son abin da zai sosa ranta. Na tabbatar da Fa’izah ta san ina begen Yaya Aliyu, babu abin da zai hana ta bar mini.... zan ci gaba da lallamin zuciyata har sai ta mance da Yaya Aliyu.... in har Fa’izah za ta iya yi min wannan halacci ni me zai hana na kasa? In anyi duniya don Rasulillahi daga yau na cire son Aliyu a raina domin Fa’izah.......”

Da na kawo nan sai na rushe da kuka sosai, hawaye na zuba a kan littafin. Dai-dai lokacin da Zanirah ta bude kofar toilet ta fito, kukan da ta tarar dani ina yi ya kara tsuma raunanniyar zuciyarta.
Ta tsuguna nan a bakin kofar ta shiga rera kuka ita ma, muka taru muka yi ta yi kamar akuyoyi. Cikin gunjin kuka Zanirah ta ce, “Fa’izah ki yafe ni...... wallahi ban ci amanarki ba.... Ban taba sanin Yaya Aliyu ne mijin da za a daura mana aure ba..... da na san shine wallahi da na bar garin da in zauna in ga wannan rana.... wallahi ban san cewa Yaya Aliyu bane ban sani ba Fa’izah.... ban san za a daura ba.....”
Na mike da azama da sassarfa na isa ga Zaniraha muka rungume juna muka ci gaba da rusa kuka tare ba mai jin na wani.
Na ce, “Zanirah kada ki ce haka, (waman qaddarralahu haqqan qadrihi.) Kada ki kara fadin haka Zanira, ban taba zargin ki da wannan ba, mune muka yi kuskure, kuskurenmu ne ni da Yaya Aliyu da muka yarjewa zuciyoyinmu muka basu fili a kan abin da suke so, alhalin muna da masaniyar ko in ce mun kwana da sanin cewa babu auren soyayya a zuri’ar A.B muka bi ta kai muka take. So we are to be liable for the outcome, ban zarge ki ba ko kadan Zanirah. Baki da wani laifi, babu wata amanata da kika ci. Addu’ata da fatana Allah ya karkato da son da Yaya Aliyu ke mini da wanda nake masa kanki, ya baku zuri’a dayyaba... Ya bani miji kamar naki Zaneerah...!”
Chapter 27 · 0% Book details