Sashe 43
Zumuntar Kenan Part 1 Complete Hausa Novel · about 11 min read
GIWA
Ban motsa daga inda nake ba, tun daga lokacin da na fadi na suma. Karar da na yi ya janyo hankalin Hajjah da sauran mazan dake zarya a tsakar gidan. A guje Hajjah ta shigo har tana tuntube da kofar daki tare da su Baba Barau da suka shigo a lokacin da ‘yan kanzaginta su Inna Kubra.
Hajjah ta tsugunna da hannuwanta biyu ta girgiza ni tana kirana “Fa’izah...... Fa’izah!!” Baban Giwa (Barau) shi ya fita ya zo da ruwa a kofi ya shiga yayyafa min amma ban motsa ba, ga idanuna a bude ina kallon su tarrr!
Hajjah ta shafi fuskata zuwa idanuna shima ban motsa ba, ta kama hannuna ta ji shi sanyi kalau, jijiyar ta saki. Ta dubi fuskata babu alamun rai a tare dani sai ta rushe da kuka.
Inna Kubra ta soma karanto addu’a tana tofa min a fuska. Ya yin da Baban Giwa ke tofawa cikin kofi, ya kammala ya shara mini duka a kaina, sai na kwanto sharaf jikin Hajjah kamar matacciya. Ko dan yatsana na kasa dagawa, babu wata gaba dake motsi a jikina. Wannan ya tabbatar musu da cewa dogon suma na yi, irin wanda shock ke sanyawa, mai wuyar farfadowa.
Hajjah ta rungume ni tana kuka ta ce, “Na shiga uku ni Hadiza, me ya yi zafi Fa’izah? Muddin kika mike Hafizi na isowa za a warware auren nan, ba zai yiwu garin neman gira a rasa ido ba. Wayyo ni Hadiza, wallahi na manta shaf da kiyayyar Fa’izah da Fa’izu da ba a yi auren nan ba”.
Baban Giwa ya zauna gefe ya zuba min ido duk sunyi tsuru-tsuru, ya ce, “Uhm! Ai na fada Hajjah babu wanda ya saurare ni, yanzu in ta mace ai shi kenan hankalinki ya kwanta. Tun lokacin na Aliyu na gaya miki kada a kara aurarrakin nan kin ki ji. Yanzu ai an dau darasi ko?”
Baban ABU wato mahaifina ya daga labule ya shigo yana cewa, “Zancen banza kake Barau, ba suma ba, ko mutuwa Fa’izah ta yi babu mai karya dokar Abubakar Giwa ko bayan ran Hajjah, mu zamu tsaya a kan wannan principle har karshen rayuwarmu. Tashi ka fita ka baiwa mutane wuri sakarai matsoraci girman wofi tun ranka bai baci ba wallahi”.
Baba Barau ya kwantar da murya ya ce, “Nima ban ki hakan ba, amma a dinga duba soyayya tsakanin yaran nan kafin a kara kulla kowanne aure tsakaninsu. Fa’izah da Fa’izu basa ga amciji tun tali-tali har zuwa girmansu. Baban ABU rai! Yana gaba da komai, sai da shi ake komai”.
Fa’izun ne ya bankado labulen dakin ya shigo a sukwane kamar an jefo shi tare da Yaya Aliyu, don tun fitowarsu mota Khalid yaron Baban Giwa ya ce dasu wai Fa’izah ta yi kara ta mutu!
Bai iya ya ce komai ba duk da ya ji kadan daga abin da suke tattaunawa, illa bin Fa’izar da ke yashe a kasa mushe ko mai rai da kallo. Manyan fararen idanuwanshi gaba daya sun fito waje sun yi jawur, har wani brown-brown suka koma. Jikinsa sai mazari yake bakinshi na motsi, amma ya kasa magana.
Aliyu ya ce “Shin Baba me kuke yi haka dukkanku tun dazu da aka rasa mai kaita asibiti? Fa’izah ba mutuwa ta yi ba!”
Sai ya sunkuya ya ciccibe ta gaba daya, Fa’iz ya hade girar sama da na kasa ya ce, “Ko da ban karanta ba na san maganin wannan suman...”
Da sauri Yaya Aliyu ya dire ni gefen gado ya yi baya, ya ce, “To likita mai mata Bismillah”
Ya yi waje abinshi. A ranshi kam dariya ma abin ya ba shi yana ta yin ta ciki-ciki, wai matar dake tsakanin rai da ajali ake ma kishi? Bai san gara ta dauwama a suman ba da ta farfado ta ganshi. Ya karbi diyarshi da ke ta tsala ihu hannun Ummi a falo ya yi waje.
A hankali su Baban ma suka shiga ficewa daya bayan daya ba tare da kowannensu ya sake tofawa ba.
Hajjah ta share hawaye ta ce, “Yanzu Hafizi ya za ayi Fa’izan ta farfado?’ Fa’iz cikin jin haushinsu duka ya ce, “Ban sani ba Hajjah”. Ita ma a fusace ta ce, “Amma ka hana a kaita asibitin?”
Ya fiddo ido ya ce, “Hajjah bakya gani daukarta ya yi ne?”
Hajja ta hasala ta ce, “Zancen banza zancen wofi, yau ga sakaran kawai. Sannu mai mata, hala gawa za ka aura? To in gaya maka gaskiya auren nan kunce shi za ayi ba zai zama sanadiyyar rasa ran Fa’izah ba. Da na san haka abin zai zama tun farko da ban saurare ka ba.....”
[14/02 3:41 PM] Sumayya Takori: Surutun Hajiya kara kular da shi yake. A kufule ya ce, “To na ji Hajjah, in ta farfado din sannan ki san abin yi ko ba yanzu ba da lafiyarta ake nema ba komai ba”.
Hajjah ta wuce tana fadace-fadacen ta da mita wanda Fa’izu bai saurari ko daya daga cikinsu ba.
Pilot Fa’iz Giwa babu abin da ya gama shi da asibiti. Amma tsabar kishin kada Aliyu ya daukar mishi mata ya gwammace kada a kaita asibitin. Shi kam yanzu ya fara son Fa’izah ma da damarar rayuwa da ita. Sai dai ta mutu su je lahira suyi aure su zauna tare, amma Hajjah ta canza masa farat daya kamar ba Hajjar shi ba wadda ta fi kowa son shi a duniya including iyayenshi, ta fi shi son duk abinda yake so, ta fi kowa farin ciki da ya ce a aura mishi Fa’izah ba. Ta yi murna, ta sa mishi albarka har da kukan farin cikinta. Amma da ya dubi halin rai kwakwai mutu kwakwai da Fa’izar ke ciki sai ya yi mata uzri.
Firjin dake gefe ya bude ya fiddo ruwa mai sanyi ya zuba a kofi ya tsugunna ya karanto Ayatul-Kursiyyu, Falaqi, Nasi da Ikhlas. Ya karanto karshen Suratul Al-Imran wato daga (Rabbana faghfirl lana wa af-anna) ya karanto ayoyin karshe na suratul Hashri tare da addu’ar Yusuf (A.S) a lokacin da ya shiga kunci a kurkuku, da addu’ar Yunusa (A.S) duka ya tofa a cikin ruwan, duk wata addu’ar yayewar kuncin zuciya da ta zo bakinshi ya tofa a ciki.
Ya shafe min fuska da ruwan har cikin kirjina dai-dai santar zuciyata. Na lumshe ido a hankali amma ban motsa daga yadda nake ba, Fa’iz ya samu kanshi cikin tsananin rudewa da firgita, bai san sanda ya kwalawa Ummi da Zanirah kira ba.
Dama suna falo suna ta tsuma. Zanira a guje Ummi da sassarfa suka fado dakin. Ya ce, “Shi kenan da gaske ne ta mutu, ku ce da su Baba su zo su binneta....” Fa’iz kuka yake sosai da hawaye da zuciyarsa. Haka Ummi da Zaneerah. Ko kusa da Fa’izar sun kasa karasawa.
Aunty Hauwa ta shigo dakin da saurinta, da alama zuwan ta gidan kenan. Tana ta fada kamar ta ari baki, “Wane irin hauka ne wannan Fa’iz? In ka hana Aliyu kai Fa’izah asibiti me kenan ka yi? Ko meye ribar ka cikin hakan? Wai ma tukunna Fa’iz da na sani ne kuwa? Crying for the sake of Fa’izah’s unconsciousness?”
Ta yi murmushi, duk ita daya ta ciccibeni gaba daya ta yi waje. Fa’iz bai ce komi ba, illa rakamu da kyawawan idanunsa dake cike da hawaye sun kuma kada sunyi jair. Sai kuma ya tashi da hanzari ya bita. Aliyu ya yi dariya ya aje little Fa’izah ya bisu ya ja motar zuwa asibitinsu wanda ke bayan gidan duka cikin A.B Estate wato A.B Clinic and Maternity.
Likitoci biyu ne suka rufu a kaina suna kokarin ceto numfashina. Fa’iz ya shiga kai kawo tsakanin gabas da yamma, kudu da arewa. Ya yin da Aliyu ya jingina da kofar (Emergency Room) da nake ciki yana hango fuskata cikin (oxygen) da aka makala mini.
Aunty Hauwa ta yi tagumi a kan kujera ta rasa abin da yake mata dadi. A haka jama’ar gidanmu da ‘yan daurin aure duka suka taddamu wannan ya harari Fa’iz wannan ya tausaya mishi, babu wanda ya iya ce masa ko da sannu da zuwa bayan shekaru masu dama da suka kwashe basu sanya shi a idanunsu ba. Shi kam Babana kujera ya samu ya kame yana kallon kowa daya bayan daya.
A lokacin Baban Kaduna wato Alh. Mukhtar ya iso asibitin. Da Dr. Habib ya fito ya nemi son ganin daya daga cikinsu Baban Kaduna ne ya shiga.
Ya ce, “Muddin Fa’izah ba ta farfado ba nan da awanni uku, to zai yi wuya in ba coma bane ta shiga. Sannan jininta ya hau, mugun hawa kuwa, zuciyarta ta tabu. Kokarin da muke yi yanzu shine na jininta ya sauka, numfashinta da bugun zuciyarta su dawo dai-dai. Na roke ku idan an samu Fa’izah ta farfado ku guji gaya mata awkward incidence ba ta hanyar da ta dace ba. Domin sudden unpleasant shock ya kan harbi kwakwalwa har ya haifar da depression’.
Baba Muntari ya shiga sharar zufa, babu shakka ya shiga tashin hankali. Ya ce, “Ba komi likita, shi kenan ai in an samu ta farfado din shi kenan. Kuma ni ban san abin da aka gaya mata na tashin hankali ba, aurenta kawai aka daura da dan’uwanta yanzu-yanzun nan, bayan wannan ban san komai ba, dama can tana da makamancin ciwon hawan jini ko (something associate) ne bamu sani ba?”
Dr. Habib ya ce, “Lafiyarta kalau. Sudden shock ne wanda zuciyarta ta kasa karba kawai. To ko auren ne ba ta so?”
Baban Kaduna ya ce, “Mai yiwuwa. Biri ya yi kama da mutum, domin wasu daban sun zo neman auren ta. Bari in je in same su in ji”. Ya mike ya firto fuskarshi babu annuri sam.
Barau ya kira gefe suka yi magana don da shi ya fara cin karo, ya kuwa gaya masa komai a gurguje cewa, Fa’izah ba ta son Fa’iz tun tana kankanuwa, Fa’iz ya tsani Fa’izah, tunda aka haifeta basu taba zama a inuwa daya ba dai-dai da sakan daya. Aliyu ta so ta aura kuma da bata samu ba ta dangana saboda Zaneerah. Tun sanda Hajjah ta fara fito da zancen ya same ta cikin sirri ya ce kar a soma wannan kada gyara zumunci ya zama bata zumunci.
Su da aka yi musu haka suka zauna lafiya, to fa in babu soyayya a tsakani haka babu kiyayya, kuma su na jiya ne ba na yau ba, zamani kullum canzawa yake yi. Zai fi kyau a dinga karbar canjin da ya zo da shi idan babu sabon Ubangiji ko halaka a cikinsa”.
Jikin Baba Muntari sanyi kalau kuma ransa ya baci domin shi ba haka Fa’iz da Hajjah suka gaya mishi ba kafin ya karbi waliccin auren nan. Ya dauka cewa ko da hakan (doctrine) din su ne kuma umarnin Hajjah ne, to babu wani abu makamancin wannan tsakanin Fa’izu da Fa’izah.
Ofishin Dr. Habibu ya koma ya dauko takarda da biro ya fito ya doshi Fa’iz wanda ke tsaye gefe yana kallon su cikin dimuwa, don ya amince ba ALHERI Baba Barau ke gayawa Baban Kaduna ba, ganin yadda fuskarsa ma’abociyar kamala ke tattarewa tana yamutsewa.
Don haka ganin ya nufo shi da takarda da biro fuskarshi babu alamun rahama, sai ya ji hanjin cikinsa suna dunkulewa wuri guda.
Fa’iz ya daga dara-daran idanunshi da suka kada suka yi jawur ya dubi Baba kallon rashin fahimta, ya motsa baki zai yi magana amma ya rasa me zai ce ne.
Baba ya ce, “Karbi ka rubuta min saki uku yanzun nan Fa’izu”.
Fa’iz ya ja da baya ya soma hawaye ya ce, “Baba Fa’izah za ta farfado ne, amma ni ba zan yi saki ba....”
Baba ya ce, “Fa’iz har ka yi kaurin wuyan in fadi ka musa min? In ka kashe ta za ka auri gawarta?”
Fa’iz ya shiga girgiza kai ya ce, “Shin Baba a kan me za ka yanke wannan danyen hukuncin gare ni? Ka sani muddin ka takurani na rubuta takardar nan shi kenan, in na tafi ba zan kara dawowa kasar nan ba, kuma ba zan.....”
Wani irin mari Baba ya share shi da shi, sai ga habo ta hancinsa. Ya kai hannu zai sake sharara mishi Babana ya rike hannun tamau.
Suka juyo suka fuskanci juna su biyun, kowanne zuciyarshi na tafasa, inda Baban Kaduna ya yi amfani da gadarar shekaru biyu da ya tserewa Baban ABU da su ya ce, “Ni sa’anka ne Ahmadu? Ko ko akwai irin wannan wasan tsakaninmu?”
Babana ya ce, “Babu ko daya, amma a nan kam ka yi zalunci in ka takurawa daya don amfanin daya. Aure kuma Fa’iz ba zai saki ba in dai a kan don kar wannan yarinyar ta mutu ne. Mutuwa lokaci ne kuma tana kan kowa, sannan lazim ce baka isa ka kara mata dakika daya daga wanda Ubangiji ya riga ya rubuta mata ba.
Ni dai ni na haifi Fa’izah in kuwa ni din ne to in ta mutu na yafe, zan dawwama da farin cikin cewa da igiyar auren Fa’iz ta mutu cikin cika burin mahaifinmu Abubakar Bamalli.
Sai dai fa abin bai kai da duka ba, Fa’iz ya wuce duka! Sai dai in Fa’izah ta kashe kanta a kan shirmen banza ta mutu kafira ba ruwana, amma aure ko ka kunce sai na sake daurawa. Ba a haifi dan da ya isa ya ki bin umarnin A.B Family ba, ba a haifa ba in dai ina da rai, ba kuma za a haifan ba. Fa’izu jeka abinka sai na neme ka, kada ka kara wahalar da kanka zuwa asibitin nan”.
Fa’iz ya juya da sauri ya fita duk gaban rigarsa ya baci da jinin dake fita daga hancinsa. Ya dauki motar Aliyu da suka zo a ciki ko rufewa bai yi ba ya yi ribas da gudu ya fita daga estate din baki daya ya bar garin Giwa baki daya ya nufo Kaduna.