← Book details Zumuntar Kenan Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 47 OF 98

Sashe 47

Zumuntar Kenan Part 1 Complete Hausa Novel · about 4 min read

****
A washe garin ranar idanuwana na bisa kofa, yinin ranar zungur ban ko leko falo ba, illa kunnuwana da na kasa suna zuko min duk mai shigowa da mai fita a gidan Hajjah ko zan ji muryar Fa’izun? Shiru! Har yamma. Kafin in ji Aliyu na ce da Hajjah “Fa’iz ya je Kano dauko Yaya Bashir”.
Hajja ta shigo dakin da nake kwance hannunta rike da kwano shake da gasasshen nama da ruwa-ruwan shi, an kuma barbade shi da yajin daddawa wanda ya ji kayan kamshin gargajiya mai dadi, ta zauna gefena a hankali da gani a darare take.
Allah sarki Hajjah! Duk zagin da ta sha bai sa ta yi fushi dani ba don ina ji da safe tana gayawa bakinta ‘yan taya murna da suka zo mata daga Zaria, kada wanda ya shigo ya ta dani barci nake a barni na huta.
Ita kanta ta fada fiyat! Kamar wadda ta tashi daga zazzabin kwana biyu. Ta ce, “Fa’izah ki yiwa Allah ki bude ido ki ci naman nan, na san kina jina ba barci kike ba, tun asuba nake aikin gasa miki don na san shi akdai za ki iya ci tunda kin ki cin komi tun jiya, shin baki tsoron irin ciwon Aliyu ne?”
Na yi mata banza na kara cusa kaina cikin filo na bude sabon kuka. Hajjah ta yi zugum da kwano a cinya, daga bisani ta aje shi a kasa ta ce, “In kin kin cin abinci wanka fa Fa’izah? Rabonki da wanka yau kwana hudu. Shin Fa’izu ya san wainar da kike toyawa ma, in don shi kike yiwa kanki wannan ukubar?”
Ban san sanda na zaro kai daga cikin filo ba na yi kutubal da shi na mike zauna, na ce, “Hajjah don na yi kyau, don na yi haske na daina kazanta na zama abin gani har a so ayi sha’awa Fa’iz ya ce miki yana son aure na ko? To daga yau duk wani abu da ya shafi gyaran jiki zuwa wanka na barshi har abada! Na koma Fa’izar da ya sanni a baya, kazama ‘yar Maimuna!!! In ce dai in na shiga warin hammata da warin baki ya ce baya so, ya je ya auro ‘yar Rasha ni kuma a barni da mai sona tsakani da Allah ba don wani abu da na mallaka ba....” Na ci gaba da kuka na gasken-gaske.
Hajjah ta ce, “Ayya Fa’izah, kin yi kuskure babba, zato zunubi ko da ya kasance gaskiya. Daga ranar da Hafizi ya bar Najeriya bai kara ganinki ba ko a hoto sai ranar da ya dawo bayan an daura muku aure”.
Da hanzari na tari numfashinta, “Tunda haka ne ki kwance auren mana ko dole ne? Na ji ko da ban auri Dr. Nazir ba na yarda na amince ki hada ni aure da Malam Hassan maigadin gidan Baban Kaduna, ko Isa direban gidan nann....”
Hajjah kam ta koma yi min dariya, ta ce, “Yo ai shi kenan, wannan abu mai dan karen sauki. Sai ki je wurin Hafizin ki amso takarda ki kawowa Ahmadu da ya kulla auren ku, ni kuma na yarda ayi aure da Malam Hassan maigadi tunda ai mutumin kirki ne bawan Allah, ko ba jinina bane na san asalinsa da tushensa, na zauna da shi tun ba a haifeku ba, babu cuta ba cutarwa”. Ta mike ta fice ta bar kwanon naman a wurin yana ta turiri da kamshi.
Na dade ina juya maganar Hajjah bayan fitar ta. Don me kowa na ce ya rabani aure da FA’IZU ABUBAKAR sai ya bude baki ya ce in amso takarda wurin sa? Bayan suna da masaniyar cewa ba zan taba iya rokon Fa’iz wani abu ba, ko kalma ta hadani da shi a kafatanin rayuwata?
Ni na kai masa auren da zan je na karbo ba su suka kai ba? Don me su ba za su je su karbo ba in har da gaske suke suna son gyara kuskure da laifin da suka yi mini wanda ba zan iya taba yafe shi ba ko in amince da shi? Don me sai na karbo takardar aure zai warware ina ce in an maidawa Fa’iz sadakinshi shi kenan aure ya warware?
Cikin kuka na fitar rai mai soya zuciya na ce da Hajjah, a lokacin da na mike na bita har uwar dakin barcinta tana shirin ta da sallar walha.
“To ki bani sadakin mana ki gani in ban mayar mishi ba?”
Tana kokawar sanya hijabin sallarta ta ce cikin alamun nuna gajiyawa da magana daya, “Shin ni Hadiza meye nawa ne cikin lamarin nan Fa’izah? Sadaki dai Barau ya karba, bayan daurin aure kuma ya dankawa ubanki na Zaria. Saboda haka su za ki je ki yiwa wannan tijarar da kike yi mini amma ni in kika sa min hawan jini Allah zai saka mini....”
Ta soma kokarin fashewa da kuka. Na juya na fice da gudu na bar mata dakin tun Allah bai jeho wani cikin ‘ya’yanta ya aika dani lahira ba tare da na kara sanya N.S a idanuna ba.

****
Chapter 47 · 0% Book details