Sashe 2
Zumuntar Kenan Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
haihuwar fari ba ta yi ba. Allah ya albarkaci wannan family da nutsuwa da biyayya ga mahaifiyar su Hajjah, babu mai zartar da hukunci a gidansa ko a kan iyalinsa face da sanin ta, da amincewarta. Haka igiyoyin auren da take kukkullawa a tsakaninsu basa ganin bekenta, domin duk wanda ya bi ko ba da son ransa ba, daga baya sai ya ga amfaninsa. Don haka duk cikin samarin da ‘yammatan da suka tasa babu mai tunanin yin budurwa ko nuna ga wanda yake so, sai wanda Hajjah ta ga ya yi mata dai-dai ta hada su. A halin yanzu dai yara uku ne mata a gabanta da basu haura shekaru bakwai zuwa takwas ba, duka jikoki ne, Ummi, Zanirah da Fa’iza. Samarin maza ‘yan sakandire da na jami’a sune Allah ya yi yawa dasu a gidan. Duk sun baro gidajen iyayensu sun tare a baskwata din Hajjah. Ba ta nuna damuwa sam, kamar yadda ba ta takura da zaman su, ita dadi ma take ji duk inda ta juya ta gansu, tana bari-bari ko suna hirarsu ta jika da kaka cike da kauna da fahimtar juna. Dadi take ji ta ga jikokin nan nata sun zagayeta, wannan ya tsokani wannan, wancan ya tsokani wancan, ta yi ta shari’a, ta yi ta bari-bari ko ta kai musu duka da mafici. Sai dai Hajjah ta raini jikokinta da kyakkyawar tarbiyya ta yadda babu yadda za ayi ka ga karami ya kawowa babba raini, ko ka ga da wuya macen da ta tasa ta zauna kusa da mazan ko kokaye-kokaye, haka nan duk motsin da dayansu zai yi, to a kan idonta ne. Yanzu kam hankalinta duka yana kan ‘yan matasan jikokin nan nata mata guda uku da suka saura a gabanta ta dage wurin tarbiyyar damu. Wato ni, Ummi (Khadija) da Zanirah. FA’IZ, Da ne ga babban dan Hajja Alh. Mukhtar, kuma rayuwarshi ta dawo gidan Hajja ne tun daga shekarun yaye ba kamar mu ba. Kaunar Hajjah da Fa’iz daban ce da duk sauran jikokinta, saboda shi kadai ne me sunan marigayi A.B wato (Abubakar), kuma a cewar ta kullum Yaya Fa’iz shine photocopy na A.B Giwa, daga kamanni har halayya. Fa’iz ya shiga ran Hajja fiye da duk ‘ya’ya da jikokinta. A cewar Hajjah, Fa’iz yaro ne mai shiga rai, kuma mai nuna mata kulawa fiye da kowa a zuri’ar. Komi Fa’iz ya samu na Hajjah ne, baya kyashin kadar da komai nasa wajen faranta mata, musamman kasancewarta ma’abociyar cin farin goro da mu’amala da man zaitun, habbatus-sauda da turaren miski a jiki da tufafinta. Tun yana karami ya san yadda yake samar dasu gare ta baya bari ta neme su bayan sun kare sai dai wani ya tadda wani, daga Abubakar-Fa’iz da take kira (Hafizi), kasancewar shi mahaddacin Alkur’ani a shekaru na goma sha biyar. Zai kuma iya karya harshe ya karanta shi tiryan-tiryan da dukkan kira’ar Hafizan da muke dasu a Saudiyyah, irin su Abdur-Rahaman Sudaith, Jabir da Abdur-Rahaman Bn Marwan Al-Juhainy da Khusairi. Fa’iz ne kadai ya yi karatun sakandire a birnin Madinah Al-Munawwarah, daga aljihun Gwamnati. Yana da shekara goma ya yi musabakar izfi talatin daga jihar Kaduna ya samu sponsorship zuwa wata sakandire a Madinah. Ya dawo gida yana da shekaru goma sha bakwai, ya kuma zabi gidan Hajjah a matsayin gidan zamansa maimakon gidan mahaifinsa Alh. Mukhtar a cikin Kaduna. Daki guda Hajjah ta ware ma mijinta Fa’iz a Boys Quaters da duk abin da zai bukata, sannan in ta ji shi shiru kullum kafarta na hanyar dakinsa don ganin “ko lafiya Hafizi baka shigo ba?” Sai ya ce, “Akwai abin da nake yi ne Hajja, zan shigo anjima kadan”. Haka suke a kullum. Zanirah kanwa ce ga Fa’iz, wato ita ma diyar Baba Mukhtari ce, zamanta gidan Hajjah ya samo asali ne tun wata tafiya da mahaifiyarta Mama ta yi aikin Hajji tana shekara hudu ta kawowa Hajja ita. Bayan dawowar Mama kiri-kiri Zanirah ta ki gidansu. Ita da Jabi Road sai hutu, shi din ma ba kowanne ba, sai wanda ta ga dama. Babban Yayansu shine Bashir wanda ke karatu a matakin farko na jami’ar Ahmadu Bello, sai Fa’iz wanda a bana ne ya kammala sakandire, Abdulhakim ke bin Fa’iz, sannan Shu’aib, Yahaya, sai Zanirah da autansu Abbas da muke kira (Junior). Khadija (Ummi) ita kadai ta fara cin sunan Hajja a cikin mu. Diya ce ga Aunty Hauwa dake Kaduna. Ummi tun tana shekara biyar Aunty Hauwa ke kawo ta hutu wajen Hajja su hadu ita da Zanirah suyi ta wasa, zuwan ta ya zama akai-akai duk hutun makarantar boko. Da dai Ummie ta gane irin dabdalar da yara sa’o’inta ke yi a gidan Hajja sai ta yiwa uwarta tawaye ta shiga ihu da tirjiya duk lokacin da aka zo tafiya da ita gidansu. In kuma aka takura mata tafiyar, to a ranar duk gidansu ba mai barci da shesshekar kakanta har da shidewa. Dole iyayenta suka hakura da kulafucinta suka bar ma Hajja. Ni FA’IZAH AHMAD ABUBAKAR GIWA, ina daya daga cikin jikokin A.B Family, kamar yadda na fada a baya, mahaifina shine da na biyu a ‘ya’yan Hajjah wato Professor Ahmadu Bamalli na jami’ar Ahmadu Bello. Auren zumuncin Bamalli shi ke tsakaninshi da Mamana Maimunatu da muke kira Momin ABU, shi kuma Baban ABU. Nice ta fari, sai Abdallah, Walida ke bin Abdallah. Yayin da Kausar ta kasance autarmu. Momi ma’aikaciyar jinya ce ita a asibitin koyarwa na Zaria (ABUTH). Tsananin rashin kulawarta gareni wai don nice diyar fari, kunya da kawaici mai sawa a hantari yaro ya sanya Babanmu ya dauke ni daga gabanta tun ina shekaru biyar ya bai ma Hajjah. Nima dama na fi son gidan Hajja, ko don su Zanirah. Sai muka dunkule mu ukun nan muka bude rayuwar da ta caza kwakwalen iyayenmu a gaba da kakarmu Hajjah. Ta yadda babu ranar Allah da za ta fito ta fadi bamu bar abin fadi ba, domin dukkaninmun nan kowacce da halinta, muka kuma hadu da maganinmu Ya Fa’iz ta yadda babu ranar Allah da ba zamu barta ba tare da Hajjah ta yi shari’a ko rabon fada a cikin ta ba. Ba zan manta ba, a ranar da zan koma Giwa ban iya na yi barci ba saboda doki da murna, da asubar fari kuwa na shiga bubbugawa Babanmu kofa ya fito mu tafi Giwa kafin su Zanirah su tafi makaranta. Don haushi Momi fitowa ta yi ta mammake ni ta kuma ce ba za a tafin ba sai sha biyun rana. Haka na wuni ina duba agogo ina zumburar baki, domin dai har sai da Baban ABU ya shiga cikin makaranta ya fito sannan muka taho Giwa (makyankyasarmu). Muna zuwa kuwa na gayawa Hajja abin da Momi ta yi min, ta ce (ya yin da ta rungume ni) “Ki barta daga yau ganinki ma sai ta cike form, tunda ba ta sonki ni ina sonki. Da kafarta za ta zo neman ki, ki zuba ido”. Ni kam na san abin da ba zai taba yiwuwa bane Momin ABU ta wanko kafa ta zo Giwa domin ni, sai in tata ce ta kawo ta. Na ce, “Hajja ina su Zanirah ne? Tunda na zo ban ji duriyarsu ba”. Ta ce, “Suna Islamiyya yanzu za ki gansu, kema in Allah ya kaimu gobe Babanku na Giwa (Baba Barau) zai amso miki form daga boko har Islamiyyar ku dinga tafiyar ku tare”. Na shiga tsalle ina murna. Daga nan na shiga kitchen din Hajja na soma bude kuloli da kwanuka ina tsame namomin dake kan abincin ina cinyewa, Hajjah na falo ba ta sani ba. Ni Allah ya halicce ni da shegen son nama kamar mage, Momin ABU kan ce kamar mayya. Don haka ko da nake Zaria Hajja kan sa ayi mani dambun nama mai yawa ta aike mani cikin samira duk sadda Babanmu ya zo gaishe ta. Dai-dai sanda na bude wani madaidaicin (food flask) ruwan kasa Hajja ta shigo. Na kai hannu zan dauke cinyar kazar dake kai Hajjah ta rike hannuna tana murmushi, ta ce, “A’a, an cinye na kowa to ban da na Hafizina, haba Fa’iza? Don ya ga naman nan tun kafin a dafa shi ba zai zama haramiyarsa ba, dole ne ya ci cinyar kazar nan”. Na dube ta rike da murfin flask a hannu daya, daya rike da cinyar kaza cikin mamaki na ce, “Hajja waye kuma Hafizi da ya fi kowa da za a sawa kowa abinci a kwanon samira shi a zuba mishi food flask?” Hajja ta ce, “Fa’izu mana, dole ne a girmama Hafizin Qur’ani. Balle Fa’iz da duk ya fiku sona, ku baku yi min sai dai in muku, Fa’iz fa? Naman nan ko idan kika sake kika ci in dai Fa’iz ne sai kin amayo shi”. Na soma yagar cinya ina ci abuna, na ce, “Hajjah ai dama ke kike daure masa yake cin zalin mutane, don bakya ganin laifinsa, kina fifita shi a kan kowa”. Hajja ta ce, “Ba na gani din, na fifita din”. Na cinye nama na bi lafiyar gado, ba jimawa barci ya kwashe ni, Hajja ta shiga harkokinta. Hayaniyar su Ummi da Zanirah ce ta tada ni.... “Ehu! Fa’iza? Don Allah Hajja da gaske? Da gaske kike Hajjah ta dawo nan da zama?” Ban ji amsar da Hajja ta basu ba, Zanirah ta fyallo a guje ta daka min duka a baya, na tashi wurgigi a firgice, sai kuma muka dafe juna muna kyalkyatar dariya. Bayan sallar isha kowacce ta bude kwanonta za ta ci abinci, Ummi ta ce, “Shegiya Fa’izah dama tunda na ga kwanukan nan lami na san kin zo garin”. Zanirah ta ce, “To meye don ta ci namanmu bayan kin samu ma ta zo? Da kafin ta zo ba cewa kike dama Fa’iza ta zo hutun nan muje muyi shi gidan Baban Kaduna ba? Wai inda ita tafiyar tafi daxi? Amma yanzu daga zuwan ta kin fara yi mata korafin cin nama?” Ummi ta harare ta, ta ce, “Ka ji ta kamar gaske sai wani kakkare ta kike, dama ban san halin bane, gobe ne zuwa jibi za a fara rabon dambe tsakaninku”. Dai-dai lokacin Fa’iz ya shigo yana sanye da ruwan madarar jallabiya da carbi a hannunsa, farin yaro tas kamar haifaffen Da’ifah,