← Book details Zumuntar Kenan Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 44 OF 98

Sashe 44

Zumuntar Kenan Part 1 Complete Hausa Novel · about 7 min read

Yadda ya shigowa Mama falo ya firgitata, sai dai kuma ba ta yi mamaki ba sam, habon ne da bacin da rigarsa ta yi da jini ya daga mata hankali, amma ba ta nuna ba.
Tozali na farko da Abubakar Fa’iz dinta bayan shekaru takwas. Amma ta ganshi cikin wannan halin mara dadi da kyawun gani. Ta yi tagumi ta zuba mashi ido sai zufa yake.
Daga bisani ya mike ya ware karfin A.C falon gaba daya da fanka, ya yi kwance rashe-rashe a tsakiyar falon yana lumshe ido yana budewa a hankali, shi kadai ya san abin da ke cin zuciyarsa, sai ko Ubangijin da ya halicci zuciyar ya sirrantata ya sanya mata hijabi don ta zama sirrin dan Adam da Ubangijinsa.
Ita Mama zato take ma Fa’iza ce ta fasa masa hanci, ta ce cikin ranta, ai tayi da sauki da ba kan duka ta rotsa maka ba. Ta shige kitchen ta sakar masa labule ta janyo masa kofa.

****
Karfe biyar na yamma agogon dake dakin asibitin ya nuna, wanda ya yi dai-dai da lokacin da na ja dogon numfashi tare da ware dukkanin idanuwana kan likitoci biyu dake kaina. Dr. Habib da Dr. Imoh suka dubi juna suka yi murmushi tare da zare na’urar da suka makala mini.
Kwata-kwata na mance komi, ban san abin da ya faru dani ba da har ya kawoni gadon asibiti. Dr. Imoh ya ce, “Ya ya dai Fa’ija?’
Na yi murmushi na ce, “Bani da lafiya ne na ganni a clinic?”
Dr. Habibu ya ce, “Of course Fa’izah! Za ki dinga fama da migraine (ciwon kan barin kai guda) lokaci zuwa lokaci. A duk lokacin da kika ji ya tashi, akwai kwayoyin da zan baki ki dinga hadiya kin ji ko?”
Na gyada kai. Suka juya suka fita suka jawo min kofar. Nurse ta shigo ta gyara min kwanciya ta fita.
‘Yan’uwa da iyayena suka shiga shigowa mutum uku-uku suna duba ni suna fita. Shigowar Ummi da Zaneerah daga karshe ya tariyo min abin da ya faru awanni shida da suka gabata.

“....... An daura aurena da FA’EEZ, FA’EEZ BAMALLI.!..... Fa’izun gidan Baban Kaduna...... Fa’iz Yayan Zaneerah, Fa’iz mugu, azzalumi, makaryaci, maketaci mai cin amanar ZUMUNCI da tozarta shi a gaban ko a bayan idon kowa... Munafuki, masharranci.... Fa’iz da na sani? Fa’izun Hajjah? Fa’iz da na tsana tamkar mutuwata...... Fa’izun da ya nuna min tsanar da a duniya babu wanda ya nuna min kwatankacinta, mai cin mutuncin mahaifiyata! Fa’iz! Fa’iz!! Fa’iz Mukhtar Abubakar Bamalli Giwa......!!!”
Na mike zaune sannu a hankali ina bin Ummi da Zanirah da kallo, wadanda bayan kalmar sannu da jiki basu kara ko tari ba. Na kai hannuwana duka biyu na rike kaina dake juyawa yana sarawa tamkar ya tsage. Idanuwana suka kada suka yi jajawur suka kankace, na dubi Ummi, Zanira, Yaya Aliyu da Babana da suka shigo daga baya.
A lokacin ne hawaye suka soma zuba min tarara! Na bude baki zan yi magana na kasa. Wani kunci da bakin cikin da ba zan iya fassarawa ba ke azalzalar tsakiyar kirjina, na kai hannuna na dafe kirjin na ce cikin rishin kuka, “Baba anya kana sona kuwa? Da hadin bakinka aka yi min haka? Da saninka aka daura min aure da Ya Fa’iz?
In kun hanani Nazir ku rasa wanda za ku lika min duk cikin zuri’armu sai Hafizin Hajjah? Baba kana sane da tsakanina da Fa’iz tun tali-talin kuruciya har girma! Baba Fa’iz fa ya tsaneni nima haka!! Makiyinka baya taba rikidewa ya zama masoyinka, har abada Baba.
Don me baku hada shi da Ummi dake son shi yake son ta ba? Ya ya kuke so na yi da nauyin so, kunya da alkawarin da na yiwa Dr. Naziru?”
Na shiga rurin kuka mai tsima zuciyar duk mai imani, balle MAHAIFI. Amma Baba bai ce komi ba, karewa ma fita ya yi daga dakin baki daya.
Su Aunty Hauwa duk suka sake shigowa, ashe suna kofar dakin basu tafi ba. Yaya Aliyu ya dubi Aunty Hauwa cikin bacin rai ya ce, “Gaskiya-gaskiya ba a kyauta ba”.
Aunty Hauwa ta harare shi ta ce, “Saboda me baka gayawa wanda ya fita ba? Ko kuma kana so ka kara da ta biyu ne?”
Ya yi tsaki ya girgiza kai ya ce, “Ki bar maganar wasa Aunty Hauwa, ko kadan babu wannan tsohuwar ajiyar a zuciyata, illa gaskiya duk inda take dole in fade ta, ba a kyautawa Fa’izah ba! Ko babu komi yanzu Fa’izah matar Fa’izu ce, kinga kuwa ai babu sauran zance”.
Aunty Hauwa ta yi murmushi, ban ga alamar ba a kyauta min din ba a fuskarta. Yaya Aliyu ya ce, “Fa’izah bani da ilimin (psychology) amma ina da tabbacin yadda kika ki auren nan haka Fa’iz yake kin shi ko ma fiye. Haka na dauka kafin ya dawo tun sanda iyayenmu suka fito da zancen.
Amma Fa’iz ya zo da wani sauyi mai ban mamaki da na kasa fassarawa, he’s completely a changed person, unpredictable. Hajjah kanta yanzu ba ta son zancen auren ganin halin da kike ciki, haka Baban Kaduna da Baba Barau.
Baban ABU da Baba Na’ibi da sauran hadin sune kawai, kuma su kadai ke son abin a yanzu. Yanzu Baban Kaduna ya gama fada da Baban ABU a kan a raba auren tunda yanzu ya fahimta abin da babu wanda ya fahimtar da shi a baya.
Don haka ki kwantar da hankalinki ki saki ranki ki koma cikin nutsuwa da walwalarki, babu inda auren nan zai je tunda kaso mafi rinjaye kuma (most powerful) yanzu basu so. Ki bisu da duk abin da suka umarceki da dadin rai, ki kwantar da kai ki roki Fa’iz in har baya sonki ya baki takardar saki, na rantse miki in har yanzun baya sonki zai baki ko don maslahar kansa, ni kuma idan har ya baki, ni kuma na yi alkawarin duk yadda zan yi zan yi in ga kin auri zabin ranki, wa ma kika ce yake da suna?”
Maimakon kalaman Yaya Aliyu su faranta mini ji na yi sun bakanta mini kamar akwai rainin hankali a cikinsu, musamman da na ga Aunty Hauwa ta bamu baya tana danna waya, ba shakka dariya take.
Na dubi Yaya Aliyu a hankali da rinannun idanuna jage-jage da hawaye. Akwai wani irin yanayi a tattare cikin kwayar idonsa wanda ban saba gani ba in yana magana. A duk sanda Yaya Aliyu ke magana, kwayar idanunsa kan nuna gesture wanda ke tabbatar da abin da yake fadi. Amma a yau, ina shakka, Ali Na’ibi ya ki mu hada ido in hango wancan gesture din dake cikin kwayar idanunsa, ya juya wani bangaren ne daban baya kallon idanuna, kuma fuskarshi ta yi jawur abinki da farin mutum, farin Bafillace, Bamalle. Tsagin Mallacin ya fito rada-rada a gefen fuskarsa, kamar wanzamin A.B ya tisa.
Idona a kanshi bana ko kiftawa na ce, “Yaya Aliyu ka rantse min da Allah ba da yawun Fa’iz aka daura mana aure ba”.
Yaya Aliyu ya dan rikice kafin ya ce, “To Fa’izah me ya kawo rantsuwa, baki yarda dani ba kenan? Za ki dora min kaffara a kan abin da bani da tabbacinsa”.
Na ce, “Duk ba haka bane Yaya Aliyu.....”
Aliyu ya dubi su Ummi da su Aunty Hauwa kowacce sai ta sunkuyar da kai aka rasa mai yi min rantsuwar da nake so ya yi min din, duk da na san basu da masaniya a kan komai, musamman Ummi.
Aunty Hauwa ta ce, “Fa’izah ki saurare ni, duk kin bi kin ta da hankalinki a kan abin da bai kai ya kawo ba. Fa’izu dan’uwanki ne ko babu aure tsakaninku ba zai cutar dake ba, ko baya son naki aure Ibada ne ba don biyan bukatar rai ake yinsa ba ko soyayya kadai.
Ki dubi girman zumunci da nonon da iyayenku suka tsotsa tare ki kwantar da hankalinki ki manta da kuruciya..... daban take da GIRMA! Dukkaninku jiya ba yau ba!! Babu wanda bai mallaki hankalinsa ba, abin da kuke yi a da duk kuruciya ce.....”
Wani irin kallo na yiwa Aunty Hauwa wanda ita kanta ya tsoratata. Ya kuma ba ta mamaki a yadda dai matsayinta yake a gare ni da yadda muke girmama su.
Na ce, “Uhm! An daura fa! Nima shaida ce a kan hakan. Sai dai wallahi yadda aka daura haka za a sunce. Wallahi-wallahi in har ina numfshi babu inda auren nan zai je daga kaina ba zaku sake ba A.B. Da in yi zaman aure da Fa’iz na gwammace in kare rayuwata haka nan single! Da in zauna da Fa’iz gara min zamana a kabarina, gara na ga mutuwata, gara min zama da bakin kumurci.... gara na rasa rayuwata dungurugum!!!”
Wani irin juyi da barin kaina ya shiga yi ya tabbatar min (migraine) da likita yake magana ya tabbata. Na dafe kaina na shiga kuka sosai. Na ci gaba da fadi cikin gunjin kuka.
“Ya ya ma hakan zai taba faruwa? Wallahi ba zai yiwu ba!” Ni kadai kamar mahaukaciya nake ta wannan sambatun sun yi min shiru. Wannan ya kara tunzura zuciyata.
Tunanin halin da bawan Allah. Dr. N zai kasance a ciki idan ya tsinkayi wannan labarin ya kara sanya ni tsandara kuka da kara duka a tare.
Chapter 44 · 0% Book details