← Book details Zumuntar Kenan Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 8 OF 98

Sashe 8

Zumuntar Kenan Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Na ce, “Ni dai na ce ka tsaya ko? Baka ganin hannunka yana jini ne?” Ya ce, “Babu komi wannan, kina so mu yi kwanan hanya ne?” Na ce, “Eh, mu yi ba komai”. Maimakon ya tsaya sai ma ya kara ware speed zuwa (200), kada ki ga yadda ‘yan idanuwana suka yo waje, suka yi kwala-kwala. Cikin kuka na ce, “Yaya Aliyu baka da lafiya.... you are bleeding....” Ya ce, “Don Allah don Annabi Fa’iza ki saurara min, da me zan ji ne? Insha Allahu lafiya zamu je gida babu abin da zai faru sai wanda Ubangiji ya riga ya kaddara”. “To ka tsaya in cire maka allurar...” “Na ce ki barshi ko dole ne?” Yadda ya yi min maganar cikin tsawar da bai taba yi min ba ya sanya hantar cikina kadawa, ban kara tankawa ba don na lura yana cikin wani irin yanayi (tension) mai wuyar fassaruwa. Bai tsaya ba sai a Giwa, harabar adana motocin A.B Bamalli Estate. Tsakar dare muka iso gida, yadda na ga mazan Estate din duka a tsaye cirko-cirko manyansu da samarinsu a kofar gidan hajjah ya tabbatar min babu lafiya. Baba Barau ya hau shi da fada, cewa yake, “Baka da hankali ne iye Aliyu? Halaka kanka kake so ka yi? Wannan wace irin wauta ce ka cizge karin jini da na ruwa ka bar gadon asibiti, ce maka aka yi duk cikinmu an rasa mai zuwa dauko Fa’iza daga makaranta?” Aliyu zai wuce su kwayar idonshi na neman rufewa, ya yi kokarin yin magana amma ya kasa. Ganin yana neman shan kasa Baban Giwa ya kama shi, shi da Baba Salisu suka mai da shi cikin motar da ya fito bai samu ya rufe ta ba. Baba Salisu ya ja motar aguje suka fice da shi asibiti. Ni dai na shige cikin gida sai kuka nake saboda halin da na ga Yaya Aliyu a ciki a dalilina. Hajjah ta taso ta rungumeni ta ce, “Baki kyauta ba Fa’iza, don me za ki tafi yawo a neme ki a rasa? Ga shi kin ta da hankalin dan’uwanki yana kwance asibiti amma daga jin labarin nan ya tsinke karin ruwan da ake masa ya dauki mota kamin kowa ya farga ya fice ya biki”. Na dubi Ummi dake zaune da mamakin sabon sharrin Ya Fa’iz, ta sunkuyar da kanta. Na ce, “Ni Fa’izar ce na tafi yawo Hajjah?” Muryata kamar na aro, kamar ba tawa ba. “Kyale ta kawai Hajjah, babu inda ni da malaminsu bamu duba ba cikin makarantar nan amma yarinyar nan kamar aljana sama ko kasa an rasa ta”. Hajjah ta ce, “To ai shi kenan zancen ya wuce tunda dai an zo lafiya alhamdulillahi, sai a kiyaye gaba. Ke Fa’iza jeki ki watsa ruwa ki ci abinci kafin asubahi ta karasa”. Na juyo da idanuna a hankali na dubi Fa’eez dake tsaye jikin bangon falon sai murmushi yake yi mai taushi, da idanuna da suka jawur na ce, “Kwarai, baka ganni ba Yaya Fa’iz, amma rabbil samawati wal’arshi shi yana ganinmu, kuma shi ya san abin da ke boye da wanda yake a sarari. Wata rana na zuwa da zai bayyana shi fili kowa ya gani”. Na wuce toilet abina yana fadin “Me kike nufi? Karya nake miki kenan?” Ko juyowa ban yi ba na shige toilet na rufo kofar da karfi. A zuciyata tausaya mashi nake kan halin da ya jefa kanshi a ciki, shin meye amfanin wannan kiyayya da yake nuna mini? Ya san girman ZUMUNCI a cikin addinin Islma kuwa? Me kiyayyar da yake yi min da hakan da yake yi min za su amfane shi da shi? A ce mutum sam-sam baya tsoron Allah a al’amarinsa sai Hajjah mutum ‘yar adam? Ni kam gani nake in an boye ma Hajjah da sauran mutane abu ko gaskiyar abu ba za a boyewa Allah ba, Allah ka shirye shi, ka ganar da shi illar karya da cin zarafin dan’uwa musulmi ba ma dan’uwa na jini ba. Na kwanta barci a wannan daren amma sam na kasa, tunanin shin wane halin Yaya Aliyu ke ciki a asibiti shi ya addabe ni? Me ya same shi? Me yasa ya boye min cewar ba shi da lafiya? Me ya tunzura shi ya yi fushi haka irin wanda ban taba gani daga gare shi ba? Na san dai ba zai wuce abin da Fa’iz ya yi mani a yau ba. A zahirin gaskiya ina tausayawa Fa’iz idan Yaya Aliyu ya fahimci cewa da gangan ya gudo ya barni. A wasu lokutan Yaya Aliyu na (acting according to) sunansa (mafadaci ne kamar kowanne mai suna Aliyu zakin Manzo). A duk lokacin da ya shiga irin wannan tension din babu mai iya tausasa shi sai Baban ABU wato (mahaifina). Tsorona Allah tsorona kada na zama silar wargaza zumuncin dake tsakanin Yaya Aliyu da Yaya Fa’iz (Mai sona da mai ki na). Don haka ya zama dole in kare Fa’iz albarkacin ZUMUNCI. In boye abin da ya yin wanda ba Aliyu kadai zai batawa rai ba har Hajjah dake matukar girmama shi da iyayenmu maza. Dan’uwa kowanne iri dan’uwa ne wanda na sani na kuma tabbata cikin family dinmu babu irin wannan hatsaniyar, ba zan so kuma in zamo silar ta ba. Na juya ga Zanirah dake gefena tana barci, sai na ga ashe ba barcin take ba sharar hawaye take yi. Na ce, “Ba ki yi barci ba Zanirah?” Ta ce, “Eh”. Na leka fuskarta sosai na ce, “To shin Zanirah me kike wa kuka?” Cikin dasasshiyar murya ta ce, “Yaya Aliyu? Shin ko a wane hali yake yanzun?” Na ce, “Wai me ke damun shi ne Zanirah? Wane irin ciwo ne ya cucemu haka ya kwantar mana da Yayanmu Aliyu?” Ta share hawaye da bayan hannunta ta ce, “Yana da (ulcer) ne ba tun yanzu ba, ba ta tashi kada shi ba sai a ‘yan kwanakin nan muna makaranta, nima da Hajjah ta je mun (visit) take gaya mani. Ya dade a kwance, domin ta ci karfinshi sosai. Ana i gobe zamu dawo Hajjah ta ce numfashi ma sama-sama yake yinsa da taimakon oxygen a asibiti. Sun samu sun fara shawo kan matsalar aka daura mishi ruwa da jinin da kika gani, lokacin ni Yaya Sani ya dawo dani gida kowa da kowa yana asibitin, wurin azahar Fa’iz da Ummi suka shigo, mu duka muna waje suka shige ciki wurin Hajjah. Babu abin da Yaya Aliyu ya soma tambaya sai ina ka baro Fa’iza? Ya ce, “Wai bai ganki ba....!” Wallahi sai ya tsinke jinin da ruwan ya dauki flask din abincin da Hajjah ta kawo mishi a lokacin ya fizgi mukullin motarshi hannun Ya Fa’iz, bai hana shi ba, shima sai ya yi ficewarsa. Abinki da taron mata babu wadda ta yi tunanin hana shi (tsai da shi), musamman a cikin yanayin fusatar da yake. Ya yi waje, Hajjah na kira da su Inna Kaltume amma bai ko waiwaye su ba, kuma babu mai ilimin kiran likita ko nurses a cikinsu balle kiran security na bakin gate. Ya tashi motar suka bude mai ya fita ya tafi dauko ki, shima Ya Fa’iz tafiyar sa ya yi......” Ta ci gaba da kuka, nima haka. Cikin kuka na ce, “Yanzu Zanirah a ganinki abin da yayanki ke yi a kaina, ko in ce nau’in zumuncinsa gareni yana kyautawa? Zan rantse miki da sarkin sarakuna Fa’iz da niyya ya taho ya barni a Gusau”. Zanirah ta zaro ido, ta ce, “Shi Yaya Fa’iz din?’ Na yi mata alamar ta yi a hankali kada Hajjah ta ji. Na ce, “Kin san Allah ina tsaye gabansa ya ja motar suka tafi, wannan meye in ba kiyayya ba? Me na yiwa Yaya Fa’iz ya tsane ni a dangi Zanirah? Fa’iz ya nuna bai damu da rayuwata ba, ko da na bi wasu can sun sace ni ba asarar shi ba ce, ko da na fito daga cikin makaranta na bata bai dame shi ba, ko da yunwa za ta kashe ni ba ruwansa bane. Amma don Allah don Annabi Zanirah kada ki fadawa kowa tunda na kudurta zan rufa masa asiri wurin Hajjah da Yaya Aliyu to zan yi, bana so a samu kuskure daga gare ni kan kiyayyar da Yaya Fa’iz ke mani, na tabbata wata rana Allah zai bayyanawa duk dangi cewa, Ya Fa’iz bai dauke ni ‘ya a cikin gidan nan ba a kan dalilin da ban sani ba”. Sai na ga Zanirah na hawaye, muka yi ta kukan tare. Daga bisani da muka ga kukan ba zai amfanemu da komai ba, Zanirah ta ce, “Mu tashi mu yi sallar nafila mu rokawa Yaya Aliyu sauki”. Washe gari su Hajjah za su tafi asibiti da safe na marairaice na ce, “Hajja don Allah?” Ta ce, “Mene ne?” “Don Allah zan biku”. “Ki bimu ina?” “Asibiti wurin Yaya Aliyu”. “Ki yi me? Kai Fa’iza da rigima kike, to shige mu je”. Ba abin da na dauka illa hijabi da report-sheet dina muka tafi. Mun samu Yaya Aliyu yana shan tea da kaninshi mai binshi Mus’ab, ya hada mishi yana mika mishi bired da yankakken dafaffen kwai da (mayonnaise) yana ci. Hajjah ta washe baki ta ce, “A’a, Aliyu lallai jiki ya yi kyau lafiya ta samu. Mus’abu an iya jinya, sai a dage da cin abinci a kan lokaci kuma yadda ya kamata yanzu ko? Tunda an ji kamshin kofar lahira”. Shi da Mus’ab suka yi dariya, ya sauko daga gadon da yake an cire mishi karin ruwan, ya gai da Hajjah. Abin da na fahimta duka hankalinshi kaina yake, na tsuguna na ce, “Yaya Aliyu ina wuni?” Ya ce, “Ko dai ina kwana Fa’izah?” Hajja ta ce, “Jiya ai Fa’iza da Zanirah basu yi barci ba ina jiyo shesshekar kukansu. Kai, tsakanin Fa’izah da Zanirah ban san wa ya fi son Yaya Aliyun nan ba, ko mi.... Hajja Yaya Aliyu, Hajja Yaya Aliyu ne ya bamu, Hajja Yaya Aliyu ya ce yana gaishe ki.....” Na rufe fuska da tafukana cikin jin kunya na ce, “Hajjah ai shima yana son mu ne, yana mana kirki, kuma ya damu damu shi yasa muke son shi”. Hajjah ta ce, “To Allah ya bar zumunci, yasa a daidaita da Hafizina tamkar hakan”. A zuciyata na ce, “HAR
Chapter 8 · 0% Book details