Sashe 46
Zumuntar Kenan Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Muryar Yaya Aliyu daga tskar gida ya tabbatar mani ya shigo gidan. A yayin da Ummi ke fadi mashi cikin kuka........ “YAYA ALIYU FA’IZA TA HAUKACE!”
Wadannan sune kalamai mafi firgitarwa da Aliyu Na’ibi ya taba ji a tsayin rayuwarsa. Baya ga dogon salati da ya ja ya dire ya tsarkake Ubangiji ya yiwa Annabi salati, sai ya sanya hannu ya zare hularsa da takalmi ya ce, “Tana ina?”
Hajjah dake sharbar kuka zaune a kofar kicin ta yi mashi nuni da hanyar store. Aliyu ya shigo a hankali ya kunna fitilar da na kashe ya zauna gefena a hankali, ya dubi yadda na yi jina-jina, face-face cikin hawaye, jini da majina, ya matso kwallar da ta tarar masa cikin ido.
“Shin wane ne da wannan danyen aikin haka Fa’izah?”
Na ja shesshekar kuka cikin dusasshiyar muryar da ta dushe gaba daya, “Kadan kenan tun yanzu kan DAN DA KOWA KE SO. Nan gaba in na batawa Fa’iz mai yiwuwa a nakastani ko a hura wuta a babbaka ni Aliyu? Ba dukan kawo wuka ba, ko yankani A.B za ku yi gunduwa-gunduwa ba ni auren nan. Na gwammace in bi yawon dandi, da dai in yi karashen rayuwata a matsayin matar FA’EEZ BAMALLI!”
Aliyu ya kaskantar da murya ya ce, “Fa’izah! Abin bai yi zafin haka ba ai. Kash! Ki bar furta kalmar nan ta “DANDI” ba don ni ba, ba don halina ba, ba don halinsu ba su duka iyayenmu. Sai don darajar da Allah ya yi miki ta ‘ya mace mai cikar mutunci ‘yar manyan mutane, kuma ‘yar gidan mutunci kamar A.B.
Su wadannan da kika bi kika tadawa hankali meye ruwansu ne? Me ya shafe su? Aure dai sun yi kuskuren daurawa. Amma igiyar warware shi da kwance shi ba ta hannunsu balle su kwance ko su warware. Duk wannan kakabi da zagi da tashin hankali ba nasu bane, ba su ya kamata ki yiwa ba tsakaninki da Fa’iz ne can. Amma ina ruwan Ummi, Hajjah ko Zanirah?”
Na galla masa harara na ce, “To shin ina na ganshi balle in yi mishi Yaya Aliyu? Ni kam yadda nake ji a zuciyata baki dayan A.B nake jin haushi. Har kai din wallahi”.
Murmushi ya yi, ya rausayar da kai, “Ta ina laifin wani ke shafar wani? Har da Yaya Aliyu? Fa’izah” Fa’eez shi ya nemi aurenki da kansa domin gyara zumuncinku da ya gurbata a baya”.
Ban san sanda na lailayo ashar ba na ce, “ZUMUNCIN me? In dai wannan shi ake kira gyara zumunci to ba shi bane, sai dai kara lalata shi. Na ji zan iya yafewa Fa’iz dukkan abin da ya yi mani, amma ba ta hanyar aure ba. In dai har an yarda a raba auren nan in auri Dr. N na YAFEWA FA’IZ DUK ABIN DA YA YI MANI A BAYA!”
[15/02 4:13 PM] Sumayya Takori: Aliyu ya ce, “A da har an tayar mani da hankali da aka ce dani wai “Fa’izahna ta haukace! Ashe lafiyar kanwata lau. To share hawayenki ki bar ta da hakarkari tunda kin ce haka shi kenan. Yanzu abin da za ayi Fa’iz za ki yiwa wannan bayanin ta lallama da salama da kwantar da kai. Kin san an ce..... mai nema shine a kasa har kullum.
Don haka kada ki ji komai don kin roki Fa’iz wani abu wannan hakkinsa ne a yanzu. Shi ke da ikon yi ko ki. Don haka dole ki aje rawanin kiyayyar gefe ki roki Fa’iz.
Yanzu Fa’iz ya canza, ba shi da wannan muguwar azzalumar fuskar da kike fadi, ke tsoronki ma yake ji! Kin san an ce abin da ya baka kuka wata ran shi zai baka dariya. Haka abin da ya baka tsoro wata ran shi zai baka dariya. Baki ga ya kasa zuwa ba? Amma ina ruwan su Zaneerah, Ummi da tsohuwar Allah HAJIYA HADIZA?”
Na girgiza kai hawaye na zuba na ce, “Yaya Aliyu kai kadai ke sona a cikin gidan nan tunda har ka goyi da bayana ka gane abin da nake so su gane suka kasa ganewa, wato Fa’iz ba mijin aure bane, ba masoyi bane abin neman tsari ne. Don haka na dauki shawararka, ka je ka baiwa su Hajjah hakuri domin na zage su sosai”.
Aliyu ya yi murmushi ya ce, “Har na ji dadi, ni Aliyu Baban Fa’izah! Allah yasa nima tawa Fa’izar ta yi min biyayya haka tamkar mai sunan ta. Share hawayen nan duka A beg...”
Nasa habar zanina na share hawaye tas, duk jikina rawa yake da karkarwa. Aliyu ya ce, “Kada ki damu da su Hajjah, su tunaninsu kin samu motsi a kanki ne. Don duk kuka suke miki na tausayawa. Ni kam na san babu yadda za ayi Fa’izata ta haukace a kan Fa’iz, faruwar hakan na nufin kenan FA’IZ ya yi galaba a kan FA’IZAH!”
Na ce, “Never. Idan har na yi hauka saboda Fa’izu na ji kunya na fadi babu nauyi, kuma ban haifu cikin Maimunar da yake zagi ba tunda ban rama komai ba, tunda na bar Fa’iz cikin nasa hankalin. Wata ma zai je ya auro wadda ta fini ya ci gaba da rayuwarshi normal ni ko in kare a pyschiatric da Asylum”.
Cikin murmushi sosi Yaya Aliyu ya ce, “Yauwa, ashe dai kin gane. Amma in ya baki takarda kika yi auren ki da Dr. Nazir kinga ai kin tusa mishi haushi ko baya sonki zai ji kishi, tunda akwai igiyar aure da ta taba gittawa a tsakanin ku, ko ya ya ne. In hakan ta faru da kyar ma zai iya zaman kasar ko ya kika ce?”
Na yi murmushi da kumburarriyar fuskata na ce, “Shin Yaya Aliyu ina zan ga FA’IZ BAMALLI?”
Yaya Aliyu ya ce, “Fa’eez na cikin kasarmu mai dimbin albarka yanzu haka. Za ki ganshi yau, gobe, jibi ko gata. Muddin ranakun nan suka wuce baki ga Fa’eez ba, to kirayi auren ku da suna tabbatacce na muddin rai. Domin sune ranaku na karshe da za a kammala bikinku a kai ki gidansa kina so ko bakya so. Don haka ki yi duk kokarin da za ki yi ki ga Fa’iz cikin kwanaki uku”.
Na yi zugum ina kallon sa, na ce, “Shin don me ka boye min tun a daren ranar Yaya Aliyu? Wallahi-wallahi da duk yadda za ayi ba zan bari a daura auren nan ba......” Na ci gaba da kuka.
Aliyu ya rasa me zai ce mini? Shi kam dabararsa ta kare kuma. Sai ya ce, “Ni kaina Fa’izah yanzu ba na ce miki ga hakikanin inda Fa’iz yake ba, rabona da shi tun ranar da ya dawo”.
Da lallami da ban baki gami da dabara irin na Yaya Aliyu yasa na tashi daga store na je na kwanta a gadon Hajjah. Daga Ummi har Zaneerah babu wanda ta yi gigigin shigowa don kam su tsorona ma suke ji. Yarinyar da za ta bude baki ta zage Hajjah cikin A.B ai abar tsoro ce, balle nasu iyayen karan-kada miya. Yau da Baban ABU ya ji kalaman nan da na kade har ganyayyakina.
Cikin daren na dinga shesshekar kuka ni kadai ina watangaririya a kan gadon Hajjah, daga wannan gefe zuwa wancan. Na turza na turza cikin kowanne lungu na zuciyata wurin bin shawarar Yaya Aliyu ta ki amince min da hakan, wato in kwantar da kai in roki Fa’iz Allah-Annabi amma na kasa.
Ya ya zan iya zub da mutuncina ga Fa’iz in nemi wani abu daga gare shi, ashe ma ya isa kenan! Never (fau-fau). Dole ne ma ya bani, in ba ta tsiya ba ta tashin hankalin da bai taba gani a rayuwarsa ba! Shima ya sani ko a lahira ba zamu yi makwabtaka ba balle zaman inuwa daya a duniya ko a lahira!!!
Wai ta ya ya ma Fa’iz zai nemi aurena, kamar yadda Yaya Aliyu ke cewa? Ni fa Fa’izah da ya tsana? Ni kazama dakikiya ‘yar Maimuna? Uhm! Ko don yanzu na yi idon gani na zamo abar kwatance cikin mata? Da da nake a ‘yar’uwarsa kankanuwar yarinya mai rauni da bukatar kulawar yayyu irin sa me ya hana ya kauna ce ni?
Ta ya ya yake tunanin ni Fa’izah zan mance kiyayyar da Fa’iz ya nuna mini tun ina ficiciyata har na kawo yanzu? Sanda yake aikowa su Ummi kayayyaki BAN DA NI. Ya tambayi lafiyar kowa BAN DA NI. Ya nuna banbaci kiri-kiri da fifiko tsakanina da sauran ‘yan’uwana...... Ya yabesu ni ya kushe ni..... ya zagi uwata a duk sanda ya so, ya dauko Ummi daga makaranta ni ya barni a jeji ko in mutu ko in yi rai ba damuwarshi ba ce. Ba don komai ba sai don saboda tsabagen tsana da kiyayya! Shin meye dalilin auren yanzu?
Don na yi girma na yi kyau na zama kyakkyawa..... Don na yi kwakwalwar karatu wadda a da bani da ita..... Don na yi kyawun da duk cikin A.B babu kwatankwacina balle tsarana! Kaico da masu halin son zuciya irin Fa’iz Giwa.
Wani da shan wahalar raino, ilmantarwa tare da real kauna ga Fa’izah shekara da shekaru bai samu ba sai shi. Wani da kwashe shekaru yana hidimtawa Fa’izah da inganta rayuwarta positively ba a bashi ba sai shi.
Ga masoyi na gaskiya irin Dr. N mai wuyar samu a wannan lokacin, mai sadaukarwa so da kauna dukkan hakkokin da Allah ya ce a basu bai samu ba sai shi. Tabbas muddin na yarda na zauna da Fa’iz ko na saurari wata kalma daga gare shi ko da guda daya ce na tabbata wadda ba ta san ciwon kanta ba, ba ta san darajar kanta ba, ba ta san darajar wadda ta dauki cikinta wata tara ta haife ta shayar cikin wahala da kakani-kayi. Muddin ban auri Dr. N ba na cika butulu duba da tarin kauna da soyayyar da ya mallaka mani, na zama mayaudariya.
Ya zama dole kenan in kaskantar da kaina ga Fa’izu ya warware igiyar da aka zarga a tsakaninmu? Juyawar da barin kaina yake yi ya tsananta cikin ‘yan dakiku, a yayin da zuciyata ta halarto min da cewa, rokon Fa’iz a bisa abin da bani da iko a kansa wannan dole ne! Kaskantar da kai ya zama dole gare ni, tunda durkusawa wada ba gajiyawa bane. Amma ba don ni ba illa don farin cikin Dr. Nazir Sani Galadanci.