← Book details Zumuntar Kenan Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 40 OF 98

Sashe 40

Zumuntar Kenan Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

(na gani ina so) cikin zuri’armu. Balle auren bare, wanda ba a taba ko da wasan kwatantawa ba. Tun bayan na mahaifiyarki wanda ko shi tunda ran A.B ne. Shin abin da ya faru a baya ni dake bai ishe ki ishara ba? Ki guji mu’amalar soyayya da kowa ki baiwa Allah zabi cikin al’amuran rayuwarki baki daya?” Idona ya cicciko da kwalla kadan ya rage su shimfido a kundukukina, na ce, “Yaya Aliyu ka taimake ni ina son Naziru, ina tsoron halin da zan shiga in na rasa shi. Fadar A.B ba fadar Allah ba! Bani da wanda zai taimaka min ya shige min gaba idan ba kai ba. I cannot afford losing him...” Yaya Aliyu ya zuba min ido na san mamakin halinmu na mata yake yi, a raina na ce, “Har an fika Aliyu Haydar?’ Ya saukar da kai bisa yatsun Fa’izah karama dake bisa cinyarsa, ya ce, “To ni dai Fa’izah babu abin da zan iya a kan wannan rigima da kika je kika jajibo. Zan yi dai iya kokarina in ga cewa ba a yiwa dangin Nazir wulakancin da za su tafi damu a baki ba idan sun zo. That is all. Ki jira hukuncin Hajjah a gobe”. Tun daga nan jikina ya kara yin la’asar. Na tashi na bar Yaya Aliyu don a ganina ba shi da abin da zai iya yi min din da gaske kamar yadda ya ce. Karfe tara na dare na kira Maman Kaduna nake sanar da ita zuwan dangin Nazir a gobe, don na manta ban sanar da ita a Kaduna ba. Na kare da cewa (cikin murya mai ban tausayi) “Mama na san ko da kowa bai goyi da bayan in auri Dr. Nazir ba, to ban da ke don ke uwa ce mai son duk abin da ‘ya’yanta ke so. A ganina lokaci ya yi da za a kawo CANJI a kan auren zumunci da ake tilasta mu yi, domin ZAMANI YA CANZA. A duk lokacin da zamani ya canza, dolen al’umma ne ta tafi tare da canjinsa in har tana so ta ci gaba. Auren zumunci ba laifi bane amma idan akwai son ran ma’auratan, in ko babu na daya daga cikinsu ya zama auren MUGUNTA, domin dole za a zalinci daya. Ke kadai kika rage min da zan kawowa kukana ki share min hawaye...... ki taimake ni Mama su amshi maganar Dr. Naziru da muhimmaci da karramawa. Wallahi ina sonshi Mama ba zan iya hakura haka in barshi ba a kan tsarin Hajjah... Ki taimake ni Mama don Allah, he’s the stranger that I’m always praying for!” Mama shiru ta yi na lokaci mai tsawo, kamin ta aje wani gwauron numfashi wanda ya kara samun suspence ya sagar da gwiwoyina. Domin numfashin da Mama ta sauke na nufin ba za ki taba cin nasara a soyayya ba Fa’izah. Ba za ki cimma ko daya cikin burarrakinki a rayuwa ba. A karshe ta yi tashin gwauron zabi ta murje jin nauyi da kawaici ta ce, “Fa’izah! Sai dai ki yi hakuri kam. Amma wannan yaron BA ZA KI AURE SHI BA! An riga an yi muku mazaje ba tun yau ba”. Da maganganun Mama na kwana zuciyata jagule ta kasa sukuni. Wadanne irin mazaje Mama ke ikirarin an mana? Mu bamu sansu ba? Mama na nufin ba zan auri Nazir ba? Mama na nufin ba zan taba cimma burirrikan rayuwata ba? Ya ALLAH ka sa kada shima in rasa shi kamar yadda na rasa Aliyu-Haydar. Ya Allah kada ka nuna min wannan ranar..... ranar da za a ce shima Dr. N na rasa shi. Ni sai yanzu ne ma na san ina son Dr. N, hankalina ya yi matukar tashi da al’amarin dake shirin faruwa dani. Ya ya zan yi iyayena su amshi Dr. N? Na yi tunani iyaka tunani bani da mai mara min baya cikin dangina kakaf, kowa tsoro yake kada in shafa mishi kashin kaji. Na yi kuka na yi kuka har na ji babu dadi, idanuwana suka shiga yin wani yaji-yaji saboda kuka. Tunanin halin da Dr. N zai kasance in ya tsinci labarin ba za a bashi ni ba, da wanda nima zan kasance da abin da iyayena ke nufina da shi, shine babbar damuwata. Shin me ya mantar dani matsalar gidanmu tunda fari? Na yi zurfi a son Naziru? Me ya mantar dani rigimar gyatumar mu mai ran karfe? Babu ko tantama SO ne, SON NAZIRU ne. Ya makantar dani ya kurmantar dani har bana iya tunanin me zai je ya zo, har bana tuna baya balle abin da gobe za ta haifar. A wannan rana na yi fatan a ce ina ma ban fito daga A.B family ba! Ina ma ban kasance cikin zuri’ar Abubakar Bamalli Giwa ba [14/02 3:41 PM] Sumayya Takori: **** Karfe goma na safe su Ummi suka yi shirin tafiya taren su Bashir a filin jirgi. Tun asuba da na yi sallah fuskata babu walwala, kallon kowa kawai nake zuciyata a cunkushe da bakin ciki da bacin rai maras dalili. Hajjah yau ko gaishe ta ban yi ba, babu wanda na yiwa magana. Na zubawa allon talabijin ido kuri kai ka ce program din nake saurara, amma ina! Zuciyata ba ta tare da gangar jikina, abubuwa masu ban al’ajabi da ban tsoro kawai take wassafa min masu shirin faruwa dani. Kafin karfe goma na safe gidanmu ya cika ya batse da dan Adam, sai busa algaita ake ‘yan daurin aure suka fara layin shigowa gai da Hajjah suna fita, ‘yan’uwa ne da abokan arziki. Kafin Babanninmu su shigo sun sha ankon farar shadda (getzner) sai sheki suke. Suka zube a falon Hajjah suka kwashi gaisuwa suka fita. Ina daga uwar daki ina hango ficewarsu ta taga daya bayan daya. Mintina talatin bayan fitarsu na ji gabana YA FADI! A dai-dai lokacin da dakikar agogo ya nuna karfe goma sha daya na rana, a lokacin ne aka daura aurarrakin masu ban mamaki, da suka ajiye kundin tarihi da wani aure bai aje ba cikin zuri’ar Abubakar Bamalli Giwa. Wani maroki mai zakin muryar tsiya yake fadi da murya mai karsashi da kwarzantawa cikin babatun magana “ALHAMDULILLAHI! ALHAMDULILLAHI!!” Sai da ya fada har sau uku. “An daura auren FA’IZAH AHMAD ABUBAKAR GIWA da FA’IZU MUKHTAR ABUBAKAR GIWA. HADIZA da MUHAMMADU BASHIR, a kan sadaki lakadan ba ajalan ba. Allah yasa anyi a sa’a, yasa anyi sai bakin rai, Allah ya sanya alkhairi ameen.....”da sauran babatu irin na maroka. Maimakon in kira yi sunan Allah sai na kwarara ihu da iyakacin muryata na zube a wajen a sume. Ban kara sanin me ke faruwa a duniyar ba. *** Jirgin Boeng 708 ya sauka a filin jirgin saman Mal. Aminu Kano da misalin karfe daya na ranar da ta kasance Asabar, wato awanni biyu da daura auren. Jirgi ne da ya taso daga Ukrain zuwa Nigeria bayan shafe awanni masu yawa yana keta hazo, kafin ya wulwulo kasa ya tsaya a cyprus ya sha mai sannan ya keto kasarmu mai dimbin albarka. Sai da passengers kaf suka gama fita kafin Pilots din su fito cikin fararen uniform dinsu. Shine na karshe a saukowa. Fari sol! Mai madaidaicin jiki, zai fi kyau ka ce ba shi da kauri sai fadin kirji wanda da ka kalla za ka san gym ya samar da shi. Ma’abocin wasu ilhamomi da nasibobi da dama da ba duk maza Allah ya mallakawa ba. Ya saya fararen idanunshi cikin gilashi mai duhu ainun samfurin ‘KAREN MILLEN. Sajen da ya zagaye gefe da gefen fuskarsa baki sidik kwantacce wanda a da baya da shi bai boye tsagin mallacinsa ba. Sai ya kara fiddo ilhama da cikar zatinsa ya fiddo cikakken Bamallen sa, kuma Bafillace. Dan kimanin shekaru talatin da hudu, wanda ya dama, ya kutsa cikin ilmummukan zamani daban-daban. Dogon hanci gare shi kamar ruler aka sa aka ja shi aka daidaita shi a tsakanin idanunsa. Idanunsa dara-dara wadanda suka dan shige loko kadan farare tar masu sheki da maiko (oily eyes) wadanda duk cikin zuri’arsu maza da mata shi kadai aka ya yiwa wannan ilhamar. Idan lissafin da yake yi dai-dai ne yau shekarunsa takwas da barin gida ba tare da ya sake ko da waiwayarta da sunan hutu ba. A zubin halitta da kirar jiki ya fi kama da Ahmadu A.B, a halayya kacokan Abubakar Giwa ya kwaso ba wani cikin zuriyarsa ba. Don haka, ka ce ga hakikanin halayyar FA’EEZ MUKHTAR ABUBAKAR BAMALLI GIWA, abu ne mai matukar wuya. Za ka san halinsa ne kadai idan ka zauna da shi, zaman ba na kwanaki ko watanni ba, sai dai shekaru. Shekarun ma sai idan kwana kake tare da shi daki daya ka kuma tashi tare da shi, halin da ake kira halin MAZAN JIYA ba na YAU ba, and difficult to be studied by sociologists and psychologists. Idan aka ce su karanci irin pilot Fa’iz za su yi placing dinsa ne kawai (upon hypothesis) but not a dependent variable. Daga fitowar shi daga jirgi har shigewar shi wani ofishi (pilots changing room) idanun Khadija-Ummi na kansa, tana mai yiwa Allah tasbihi da godiya mara iyaka da wannan miji da Allah ya ba ta wanda ke ninkaya cikin zuciya da mafarkinta, ba ta taba tsammanin akwai ranar zahirantar mafarkin nata ba. A hankali ta ji danshi a kan fuskarta, wanda ba ta ko tantama hawayen farin ciki ne. Har zuwa lokacin da ya gama shige da ficensa a (airport) din tare da abokan aikinsa, ya canza kaya zuwa kaftan na farar lallausar shadda (Hilton) da ruwan kasar hula a kansa, takalmin fata dake kafarshi shima ruwan kasar ne. Ya janyo trolley dinsa zuwa inda ya hango fuskokin masu kama da tasa fuskar, wanda komai daren dadewa suna gilmawa cikin idanunsa, wato fuskar zuri’ar Abubakar Bamalli, wanda ya fi so da gani shi ya fara ganin, wato Aliyu Na’ibi. Da sassarfa Aliyu ya karaso suka rungume juna shi da Fa’iz, rayuwarsu ta baya ta dinga dawo masa tar-tar kamar a majigi. Abubuwa da yawa ba zai manta dasu ba. Cikin taron nan kaf na mata da mazan Bamalli, manya da yara, wadanda ya sani da wadanda bai sani ba, musamman kananan yara, ya hanga ya duba bai ga Zahrar cikin taurarin ba. Ya ga Zanirah, ya
Chapter 40 · 0% Book details