← Book details Zumuntar Kenan Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 38 OF 98

Sashe 38

Zumuntar Kenan Part 1 Complete Hausa Novel · about 6 min read

****
Soyayyarmu da Dr. Nazir ta yi nisa da karfin da ta zama sananniya a tsangayarmu. Tsegumi kam iri-iri an kawo min a kan yawan ‘yammatan da Nazir ke dasu cikin makarantar. Na kan toshe kunnuwana ne kamar yadda ya ce, ko in yi hannun riga da duk wanda ya kawo min tsegumin.
Dr. Nazir ya ware muhimmin lokacinsa wurin yi min (extra class) bayan kowacce laccarsa. Nazir ya iya koyarwa. A dalilin koyarwar da yake yi min ‘points’ dina a jarrabawa ya kara karfi fiye da na baya. Nazir ba shi da karfin idanu (short sight), a dalilin hakan yake amfani da farin gilashi mai kara karfin gani (lenses) ya yin rubutu ko karatu, ko ba da lacca. Amma in ba fadi aka yi ba za ka yi zaton na kwalisa ne. Don yana mai kyau sosai.
Nazir mutum ne da ya iya tsara magana da hafizin harshen da Ubangiji ya hore masa. Iya maganarsa da kirkinsa ya taka rawa mai yawa wajen sanya zuciyata ta zamo kangararra, bana ji bana gani.
Da kaina in ban ganshi ba sai na bishi office, har sayayya mu kan fita wasu lokutan. Tun Ummi na hana ni har ta gaji ta rabu dani. Wai ni Fa’izah tsatso daga A.B House nice mai bin saurayi har office, nice mai fita da saurayi. Wannan ba karamin kona ran Ummi yake ba. Har ta gaji ta tseguntawa Aunty Rabi.
Aunty Rabi ta samu Yaya Mufty take sanar da shi, inda ya ce, “A kawo mishi sunan Nazir cikakke zai yi bincike a kansa. In mutumin kirki ne a kyale ni, kwana nawa ne zamu gama karatun mu koma gaban iyayenmu? Domin Hajjah ta soma fadan mu dawo gida haka karatun ya ishe ta. Abu ya ki ci ya ki cinyewa tamkar cin kwan makauniya”.
Aunty Rabi ta ce, “In kuma ba mutumin kirkin bane ba fa Mufty?”
Ya ce, “Zan san abin yi a kai”.
Ni kam duk surutunsu da harare hararen su basa damuna, na yi nisa a son Naziru.
Wani irin so nake dandana mai wuyar fassarawa, wanda ya zarta na Yaya Aliyu fintinkau! Idona ya rufe a son Naziru, lokutana baki daya na Dr. Nazir ne.
Tambayar da jama’ar dake tare damu ke wa Ummi shin Fa’izah ta san Dr. Naziru (use and dump) ne? Ta ya ya yarinyar ‘yar gidan mutumci wadda ta san ciwon kanta irin Fa’izah ta yarda cewa Dr. Nazir auren ta zai yi? Shin Fa’izah ta san yawan ‘yammatan da Dr. Nazir ya yaudara ya watsar a Kano? Shi fa dama duk inda kyakkyawar mace take nan idonsa yake, zai nuna mata so ya yi ta yi mata facaka, amma da an ce ya fito ayi aure ba kya kara ganin keyarsa”.
Ummi ta kan girgiza kai, don bakin ciki ta rasa me za ta ce, sai dai ta ce, “Fa’izah kam ta yi nisa ba za ta ji kiran ba”.
A yammacin wata talata mun dawo daga Ado Bayero Mall (Shoprite) ni da Nazir ya sauke ni dai-dai inda ya ga su Ummi a zaune a (seaters) na dalibai karkashin wata bishiyar dalbejiya mai inuwa, bai ko tsaya sun gaisa da su Ummi ba don ya san Ummi ba ta goyon bayan tarayyarmu daga ita har shakikiyarshi Haulatu, ita ma ta bi sahu don tsoronta na kar mutuncinta ya zube idon su Aunty Rabi dake matukar ganin mutuncinta, ranar da Nazir ya yi (dumping) dina.
Ko ba don wannan ba Nazir baya sakar ma dalibanshi fuskar da raini zai shiga tsakani. Ko mata da yake nema tamkar bunsuru ba dai cikin tsangayarmu ba can a wasu tsangayoyin ko waje yake neman abinshi.
Na yi musu sallama duka suka amsa min a sanyaye, na aje ledar hannuna gefen Haulatu ina fadin “Wash Allah! Na gaji da yawa. Dr. N (sunan da nake kiransa) ba dai yawo ba, shi dai a je shopping burinsa kenan”.
Suka dubi juna suka kau da kai. Cikin nutsuwar da ban san tana da ita ba Ummi ta ce, “Fa’izah rayuwar da kika zabawa kanki kenan? Tarayya da maza irin su Dr. Naziru? Yau da Hajjah za ta ji wannan mummunan labari ina kike tunanin za ta tsoma ranta? Da kin sa zuciyarta ta yi bugawar farat daya.
Wallahi-wallahi tun wuri ki sake hanya tun dare bai yi miki ba. Nazir ba dai-dai yake da tsarin rayuwarki ba, kuma aurenku ba zai taba yiwuwa ba. In kin manta kin fito daga zuri’ar A.B ne nake tuna miki”.
Haulatu ta cafke “Ina mai matukar jin kunyar ranar da Yaya Naziru zai yi dumping din ki, (as if you had never been in existance), shi yasa nake so ki kwaci kanki tun kafin zuwan wannan ranar, domin mai hali baya fasa halinsa, kuma sannu ba ta hana zuwa sai dai a dade ba a je ba.
Nazir dai dan uwana ne, karewa ma shi ya sha nono ya saki na kama, uwarmu daya ubanmu daya. Amma bana goyon bayan ki mallaka mishi soyayyarki. Abin dai da baki son a ta da to dole ne a fadi, ba auren ki zai yi ba”.
Na yi murmushi na ce, “Kun gama? Shin ina kaunar da kuke ikirarin kuna yi min din Haulatu da har ba za ku so abin da nake so ba don cikar farin cikina? Kuna kina da Dr. N ne don tsoron kada ya yi min yadda yake yiwa sauran ‘yammatan da ya nema a baya, shin ku Allahn musuru ne? Kun san gaibu? Kuma shin shi halin dan Adam baya canzawa ne?
Dr. N ba munafuki bane irin yadda kuke zato, tun ranar da muka hadu ya gaya min abin da kuke gudu din, ya kuma tabbatar min daga kaina ya daina, ina rokon Allah ya taimake shi ya dainan. Manzo mai tsira da aminci ya ce, ‘ku kyautatawa mutum zato domin zato zunubi ne ko da ya kasance gaskiya’.
Kuma duk iskancin da kuke tsammana mishi wallahi bai taba kai hannunshi jikina ba ko bisa kuskure. Bai taba ba. Wannan ya nuna Dr. N son Allah da Annabinsa yake yi mun, ba kuma zai gwada iskancin nasa a kaina ba saboda ba yaudarata yake da niyyar yi ba. Zancen mutuncina da kuke, kada Allah yasa a ga mutuncin nawa in har sai na bar Dr. N.
Ke kuma Haulatu yadda kike aibata dan uwanki don tsira da naki mutuncin wallahi kin bani mamaki, in kin yi ne don ki burge wallahi baki burge ni ba. Ai naka-naka ne komin lalacewar shi, hannunka baya taba ribewa ka yanke ka yar. Ku zuba ido tunda duk kun zama ‘yan adawa da yardar Allah kunya za ku sha”.
Na suri ledar shopping dina na bar musu wurin, na barsu suna kallon-kallo a junansu an rasa mai karfin halin musawa ko maida martani.

****
Abdullahi ya ce, “Ka rufa min asiri Naziru, Haulat ta zo min tana kuka in rokeka ka rabu da kawarta in ba auren ta za ka yi ba. Naziru ka yiwa Allah ka rabu da yarinyar nan ko don zumunci da sanayyar dake tsakani”.
Dr. Nazir Sani Galadanci sai ya yi murmushi yana harhada takardun daliban dake bisa tebirinsa. “Wata fuskar..... ta fi gaban mari. Za ka sha mamaki na Abdullahi”.
Chapter 38 · 0% Book details