Sashe 26
Zumuntar Kenan Part 1 Complete Hausa Novel · about 4 min read
Hauwa na hankalce da duk motsina da na jajayen idanuwana, tana bina da kallon tausayi da karfafa gwiwa. Fuskarta cike da tausayi ta ce, “Fa’izah duk wannan ramar ta mecece?” Ta fada tana taba kasusuwan wuya da suka bullutso min da hannun damanta. Na yi murmushi na ce, “Kai Ya Hauwa kin manta daga kurkukun jarabawa na fito?” Ta yi murmushi kawai irin nasu na manya. Ba zato Baba Na’ibi ya ce, “Na yi zaton Fa’izah ce za ta zamo matar Aliyu?” Duk sai kowa ya yi tsit, yana mai jinjina maganar. Sai Hajjah ta bude baki a hankali ta ce, “Na’ibi!” Ya dago ya dube ta cikin amsawa. A nutsenta ta ce, “Ta ina Fa’iza ta dace da Aliyu?” Baba Na’ibi a dan daburce ya ce, “Ban gane ba Hajjah?” Ta yi murmushi ta ce, “Abin nufi a nan, shin Fa’izah ba mace ce mai tsiwa, taurin rai, ginshira, dagewa bisa duk abin da ta kudurtawa ranta (dertermination) kekasasshiyar zuciya a kan duk abin da ta tsana ko mutumin da ta tsana ko halayyarsa. So wanda ya wuce hankali ga duk abin da take so? Shin Aliyu da Zanirah ba mutane ne masu sanyin rai ba da saukin zuciya? Saboda haka sun dace da juna, za su zauna da juna lafiya, za su ji dadin zama da juna babu hayagaga. Amma halayen Fa’izah ba kowanne namiji ne zai iya zama da ita ba sai NAMIJIN DUNIYA, mai halaye irin nata ba mai sanyin rai irin Aliyu ba. Ma’abocin juriya da karfin jiki da na zuciya baki daya. Amma in an hada Aliyu mai sanyi da Fa’izah mai tsiwa da jumurda, bakwa tunanin Fa’izah ce za ta zama mijin, Aliyu ya zama matar saboda matsanancin son da yake mata? Wato ya zamo sai yadda ta yi da shi kenan saboda gudun fitinarta da bacin ranta? Kasancewar shi mutumin da bai son tashin hankali da hayagaga ko kankani? Kuna gani fa tun yanzu duk abin da Fa’izah ta gindaya mishi baya iya tsallakewa duk ya lalace a gindinta, bini-bini yana binta kamar bita-zai-zai wace kalar rayuwa kuke tunanin za su shimfida a gidan auren su? Baya iya musa abin da ta ce, baya iya tsawata mata in ta yi ba dai-dai ba, tun suna yara nake hankalce dasu. Ina rayuwar aure za ta yiwu tsakaninsu ba tare da raini ya shiga tsakani ba? Aliyu da Zanirah kuwa da wuya za a ji kansu, za ku ga irin rayuwar da za suyi ta namijin da ya isa da gidansa, za ku ce dama na gaya muku ne”. Gaba daya suka yi shiru suna masu jinjina maganar, haka nima ina mai gaskata kowacce kalama a cikin zancenta. Tuni na gane hikimar hada auren Zanirah da Aliyu da tsohuwar mai tarin hikima da fasaha ta yi. Wato muddin na auri Yaya Aliyu ba zai iya lankwasa ni ba ko kadan, saboda matsanancin son da yake min. Tana masa gudun zama mijin ta-ce ne kawai gara ta ba shi wadda zai iya da ita don son zamar da shi mai kima da karfi a gidansa. Amma Zanirah halinsu daya (simple personality) wadda ba ta zafafawa cikin al’amuranta. Tabbas halayen Zanirah baki daya irin na Yaya Aliyu ne, hakuri, sanyin rai da sanyin zuciya. Abin da babba ya hango yaro ko ya hau ganuwa da Dala da Gwauron Duste ba zai hango ba. Sai dai ta wani bangaren Hajja ta yi (underestimating) dina. Ni ina son Yaya Aliyu ne saboda kirkinshi, halayensa da mutuncinsa da son addini. Ban taba tunanin in yi amfani da son da yake mini in mun yi aure in mai da shi sahoramin miji ba (mijin-ta-ce). Sai na bude baki a gaban Babannina duka na ce, “Hajjah kina da gaskiya. A da kam mun so juna da Yaya Aliyu so ba na wasa ba. Sai dai daga yau wallahi na hakura, na barma Zanirah da zuciya daya, zan kuma ci gaba da binsu da kyakkyawar addu’a Allah ya karkatar da son da yake mini kanta. Ban ga laifin ki ba Hajjah, Allah ya basu zaman lafiya.....” [12/02 6:09 PM] Sumayya Takori: Hawayen da suka shimfido min su suka sanya na mike na yi daki aguje ina kuka wiwi. Yaya Hauwa ta taso za ta biyo ni ta rarrashe ni amma Hajjah ta ce ta kyale ni kawai in yi kukan zuciyata za ta yi min sanyi, kukan sabo ne da fitar SO. Na ci kuka na a gado na share hawaye, na jiyo zubar ruwa a (toilet) wanda ya tabbatar min Zanirah wanka take yi. Idona ya kai ga abin da na jima ina fakon Zanirah don in dauka sai yau na hange shi cikin kwabar kayanta wato ‘DIARY’ dinta. Na yi hamzarin daukowa ban yi nawa ba wajen bude shafin farko. Kwanan watan ya nuna Zanirah ta yi rubutun nan ne tun muna JSS (karamar sakandire).