← Book details Zumuntar Kenan Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 19 OF 98

Sashe 19

Zumuntar Kenan Part 1 Complete Hausa Novel · about 4 min read

****
Tun daga ranar na fita harkar Ummi, na ma tattara kayana na koma hostel din su Naja da muka fi dasawa. Ummi ba ta gaya min Fa’iz ya ba ta hankici ta bani ba, kawai na tsinci kyakkyawan farin hankici cikin kayana mai dauke da kalmomin Larabci guda (7) ‘AHUBBIK’.
Na kai hankicin karan hancina na sunsuna, sassanyan kamshin turare dan gidan (Philips Lumea) da hakincin ke yi ya haifar da wani takaitaccen nishadi a zuciyata, ya gusar da duk wani bacin rai na Ummi da nake fama da shi a cikin ranakun da bama ga maciji. Haka nan Allah ya sanya mani kaunar dan kyakkyawan hankicin a raina.
Sai dai kamshin Philips Lumea da hankicin ke yi na kan so in san inda na san shi amma Allah bai bani ikon tunawa ba. Na tura shi cikin jakar littattafaina ko cigiya ban yi ba. A raina na ce “Ina zaune ai ya zo ya tadda ni. In mai shi ta yi cigiya na ba ta”.
Kullum bana iya barci ba tare da na shaki kamshin daddadan hankicin nan ba, haka in na fito aji ana rana, na kan rufa shi ne a fuskata zuwa hostel, bana ko tsoron mai shi ta gani. Kuma abin mamaki har kwanaki suka ja, aka debi wata kamshin da hankicin nan ke yi bai gushe ba.
Wannan ya tabbatar min da ba karamin turare ne a jikinsa ba. Duk sanda zan wanke uniform sai na wanke shi, amma babu abin da ya ragu na daga kamshinsa kullum kamar ina kara fesa masa turare dan gidan (Philips Lumea) ne.
A karshen watan Yaya Hauwa ta zo ganinmu, ta bani letter daga Yaya Aliyu, kuma wai lallai-lallai in rubuta amsa in ba ta a take. Don a satin ya zo gidanta ya fi a kirga yana tambayar amsar wasikar tana cewa ba ta zo ba, yana ta yi mata mita.
Na yi dariya na ce, “Yaya Hauwa kyale Yaya Aliyu kawai, rigimar shi yawa gare ta. Yanzu haka duk zancen in bar rubutu in yi karatu ne bai san tuntuni na ajiye shi a gefe ba”.
Ta ce, “Ah toh! Sako-makoko na dai isar don haka ragowar can ta matse muku kun fi kusa, wai harshe da hakori. Ban tambaye ki me ke cikin wasikarku ba”. Na rufe fuska da tafukana ina dariya cike da jin kunya.
Ban bude wasikar Yaya Aliyu ba sai a washegarin talata da daddare bayan na gama komi da ya zamo min al’ada kafin kwanciyar barci. Na saka (nighties) na saki net (gidan sauro) na shige ciki. Sannan na bude wasikar Aliyu;

“A gida, Giwa-
Fa’izah, ko kin san mene ne abin da na dade ina cewa ba ki yi girman da za ki fahimta ba? To ba wani abu bane strange. Abu ne da ya zamo (known) ga kowa a Giwa, Zaria, Kano da Kaduna. Idan har zuwa yanzu shekaru goma sha bakwai baki yi kwakwalwar da za ki fahimtar ba sai in ce zan yi A BARI YA HUCE.....
Yayan is in love! Fa’izah Aliyu is in love!! Please save a soul..... ki taimaki “tuzurun” yayan ki ki zama zabin Hajjah gare shi nan da watanni uku wato bayan kammala jarrabawarku ta karshe. Hajjah ta yi rantsuwa nan da watanni uku ko na shirya ko ban shirya ba za a daura min aure, ta gaji da karatun da ba shi da karshe. Don haka ne na ga tunda wuri gara mu fito fili mu bayyana kanmu maimakon hannunka mai sanda. Babu zancen fahimtar juna sai cika burin zuciyoyin da suka dade suna ragaita.
-Aliyu-Na’ibi.

Wata irin murna marar misali na shiga yi tare da dariya-dariya da ni kaina ban san irinta ba. Abin da kunnuwana suka dade suna jiran ji daga bakin Yaya Aliyu. Gaskiyar Mama Asma’u ne da ta ce, “Sannu-sannu ba ta hana zuwa, sai dai a dade ba a je ba”.
Sai na kwanta a rigingine zuciyata da ruhi cike taf da begen Aliyu-Haidar. Kwakwalwata ta shiga wassafo min irin kyakkyawar rayuwar da zamu shimfida ni da Yayana Aliyu, irin kyawawan yaran da zamu haifa kasancewar Aliyu fari tas Fa’izah choculate colour. Na tabbata za suyi kyau, kyau mai suna kyau da babu irinsa cikin zuri’ar Abubakar Bamalli Giwa.
Watanni uku kenan da kammala masters din Yaya Aliyu a jami’ar Legas a kan (Agricultural Engineering), cikin lokacin kuma ya samu aiki da ma’aikatar gonaki ta kasa. Sun aje shi reshen jihar Legas matsayin mataimakin M.D. Gida cikin lekki da motar shiga ta zamani da matasa masu matakin rayuwa dai-dai da tashi suke hawa.
Chapter 19 · 0% Book details