← Book details Zumuntar Kenan Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 30 OF 98

Sashe 30

Zumuntar Kenan Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

**** Yau wata guda kenan da tafiyar su Zanirah in har na lissafa dai-dai, amma babu ko duriyarsu. Aliyu dai ya yi waya wa Hajjah cewa yana bakin aiki a Ibadan, don haka ba zai samu zuwa gida karshen watan nan ba sai na sama, suna tare da amaryar a Ibadan. Uhm! Namiji kenan. In ji Umma Sulaiman Shu’aibu ‘Yan Awaki. Kudan zuma, indararon roba ta ko ina zuba kake. Allah ya gyara. Takurawar da Mansur Modibbo ke min a gida Giwa da Zaria yasa duk garuruwan suka fice min a rai. Domin dai ni tunda na rasa Yaya Aliyu bana jin zan iya wata aba wai ita soyayya nan kusa. So dai guda daya ne, na sha shi na warke, bana fatan Allah ya kara maimaita mini. Ko ina fatan hakan ba cikin garuruwan nan uku ba, Zaria, Giwa da Kaduna. He must be a stranger! Very far away!!! Ban gama jinyar wancan ciwon ba yake nema na da in dasa wani, “Shin shi wannan bai ma da tausayi ne Ummi?” Na tambayi Ummi a yammacin wata asabar. “Wai da me zan ji ne? Yeah! I would love to marry a stranger, but he must be from far..... and he’s a stranger but not from far....” Don haka na rika yin baya-baya da shi da kora da hali wanda ya fi kora da sanda, duk da mahaukacin son da yake min kuwa. Ba wai don yana da wata makusa ba, dukkan halayen shi ababen yabo ne. Ni da Ummi mun kasance cikin kewar Zanirah, kullum kamar wadanda aka yiwa mutuwa. Hajjah kanta daurewa take tana sabgoginta, amma rashin Zanirah a gidan ita ma yana dukan ta. Daga mu yi tagumi, sai mu kwanta. Mun daina barin yara su kunna T.V a gidan balle radio. Sai mu ce sun dame mu. Mun dai mai da gidan kamar gidan mutuwa, farin cikinmu ya takaita, ba Zanirah ba Aliyu. Muna cikin kewar da ba za ta misaltu ba, ko yaushe muna kwance a daki kamar tsumma. Don haka na ji dadi da Hajjah ta kawo shawarar wai mu tafi Kano gidan Yaya Rabi mu huta gajiyar baki kafin fitowar takardun karatunmu mu ci gaba da karatu. Dukkanmu ba karamin mamakin wannan magana ta ci gaba da karatu muka yi ba. Na yi tunanin ko Hajjah ta yi hakan ne don ta samu na manta da Yaya Aliyu gaba daya. Abin da ba ta sani ba shine, tuni na bude kundi na sanya Aliyu a ciki (as a past tense). Wallahi ko da zan mutu babu aure, babu huldar da za ta shiga tsakanina da mijin Zanirah (other than) ta ‘yan uwantakar da ta hada. Muka shirya tsaf sai Kano. Yaya Rabi mutum guda har da rabi don zumunci da son dan uwa. Zan iya cewa duk ‘ya’yan Hajjah babu wanda ya kaita kirki. Zama da ita da raha irin ta mijinta Yaya Muftahu ya wanke mana damuwa kakaf. Don sai ya zamanto Yaya Rabi ta cike mana gurbin Zanirah, Yaya Muftahu ya cike mana gurbin Yaya Aliyu. Sai muka kwantar da hankalinmu muka bude sabuwar rayuwa mai dadi. A irin hirarrakin da muke yi da Yaya Rabi ta kan so a sako hirar su Zanirah, ko da wasa Yaya Rabi ba ta taba sanin mun so juna ni da Yaya Aliyu ba. Irin maganganun da take sakin baki tana fadi a kansu a gabana ya kan kona min rai ya tado wani kwantaccen ciwo da na riga na samu ya warke. Akwai sanda za ta ce, “Allah kadai ya san irin soyayyar da suke barzaa yana muzurai yana cewa baya so din” Ko ta ce, “Uhm! Su Zanirah ana can Ikko ana romansewa”. Ko ta ce, “A gaskiya Zanirah ta caba miji. Ga kyau ga kuma kyawun hali. Aliyu Mutum ne wanda zai shagwaba matarsa, ya bita da duk yadda yadda ta yi da shi, ba irin Bashir, Fa’iz da Mus’abu bane”. Na kan kau da kai ne kamar ban ji ta ba. Ummi ta yi dariya kawai. Haka nan ban taba tankawa ba sai Ummin. Tsakanina da Ummi yanzu mun koma mun dinke kamar da. Domin ta lura in har tana son hulda dani to fa sai ta ajiye zancen makiyina Fa’iz a gefe. Ba ta zancen Fa’iz a gabana kamar yadda duk hotunan shi da ire-iren kayan da yake aiko mata ta tattara su ta aje a wata katuwar jakar Hajjah a Giwa. Amma dai ai na ji TAKORI ta ce, “ZUCIYAR MUTUM, BIRNIN SA!” [12/02 6:09 PM] Sumayya Takori: Daki guda Yaya Rabi ta ware mana mai dauke da bayan gida, kananan gadaje biyu, sai jar kilishi da ta malale ilahirin dakin da jan labulaye. Karamin bed-side fridge, sai mudubin dogon yaro mai sheki da kayan shafe-shafe da feshe-feshe, da kwabar adana suttura (wardrove) ta jikin bango. Kamar yadda mazan Kano samari da magidanta basa ganin kyawawan ‘yammata su kyale, to haka fita ta gagaremu ni da Ummi. Har suna aka sakawa gidan Aunty Rabi a layin wai Gidan Mallawa. Kiri-kiri muna gani za a gayyaci Yaya Rabi biki ko suna amma mu haramtawa kanmu zuwa muna ji muna gani, domin muddin muka fita, to kuwa la-shakka ba zamu dawo mu kadai ba maza basu biyo mu ba. Kofar gidan Yaya Muftahu baya rabo da mota da vespa, wanda mu bamu saba hakan ba sam a namu garin sai hakan ya dame mu ya zamo mana sabo ya takurawa walwalarmu. A hankali na soma fuskantar Ummi na canjawa, ta fara saurararsu. Da na yi mata magana sai ta yi murmushi kawai har mulmulallun kumatunta suka lotsa, ta ce, “In mun koma inda muka fito ba shi kenan ba? Abu ne na dan lokaci. Namiji abokin rayuwar mace ne ba za ta taba rabo da shi ba”. Cikin watanni hudu a gidan Aunty Rabi jikina ya soma wani irin canzawa, tsayina ya fito na mike sosai. Yawan kaimu (Zaynab Saloon) da Ya Rabi ke yi a (Mukhtar Mohammed Link) yasa gashina ya ware ya yi tsayi da taushi duk da ba (relaxing) muke ba wankewa ne da (steaming) kawai. Haskena ya dan fito duk da bani da haske. Kamannina na Mallawan usli ya fito sosai, na yi kumatu subul-subul, saboda kwanciyar hankali. Kugu da kirjina duk sun canza kiyasi, tabbacin budurwa matashiya ‘yar shekaru goma sha takwas. Shin ma na taba gaya muku ko wace ce Fa’izah Ahmad Abubakar Bamalli Giwa??? Ban taba ba, illa kawai kun jera ni a sahun kyawawan Bamalli. To eh, ba zan yi musu ba a nan, sai dai akwai wasu ‘yan bambance which I didn’t clarify (da ban farrake ba) ga masu karatu na. Ni kaina ban san ina da wadannan qualities din ba sai da na shiga shekara goma sha takwas da zamana a Kanon Dabo. Duka A.B Family ni kadai ce mai duhu (choculate). A yau, kaina na tsurama ido cikin mudubin dogon yaron gidan Aunty Rabi bayan fitowa ta wankan la’asar. Ina da madaidaicin tsayi, wato ba doguwa ba ce ni, ba kuma gajeriya ba. Doguwar fuska mai dauke da mulmulallun kumatun hutu subul dasu masu nuna bana cikin wahalar rayuwa ko kadan, wadanda Allah bai halacci kwayar kurajen (pimples) ko daya a kansu ba. Idanuwana farare sol da bakin zanen ido mai walainiya na daukar hankali. Madaidaicin baki wanda ba kankani bane can-can ba kuma kato bane, jerarrun hakora farare sol, jere reras a cikin shi. Karan hanci siriri kamar an saka ruler an daidaita mata shi a tsakanin idanunta. Tunda ya taho daga sama a mike yake bai lankwashe ba ya dire kyam saman bakinta. Tsagin Mallanci 2-2 dake gefen fuskar Fa’izah su suka fitar da Mallancin ta sosai da an ganta babu tambaya zuriya’ar Abubakar Giwa ce. Sumar kaina kan sakko har bisa kafadu, ya kwanta lamban. Wanda kitson shi kwararriyar ma sai ta hada da dabara. Duk da haka kuma cikin kwana hudu ya warware da kanshi ba tare da ta sanya kibiya ta warware shi ba. Don haka ta hakurewa kanta yin kitso kullum sai dai ta kalmashe shi cikin ribbons (bound). In Aunty Rabi ta daddage ne take kalbace shi yar-yar ta kama bakin ta matse da dutse da roba sannan yake zama. Ba ta taba tsugunnawa wata mace ta kama mata kai da sunan kitso ba tun tasowar ta baya ga Hajjarta. Yalwar gashin kanta shi ya taimaka wajen inganta gashin ido da na girarta. Hakan bai ishe shi ba sai da ya bi ya kwanta a fatar jikinta kafataninsa. Irin wadanda Sadanis basa yiwa (halawa) ya yin aure. Don haka a kullum Fa’izah cikin (shower-shaving) take duk sati biyu zuwa uku don fitar da kyan fatar jikinta da kwantaccen gashi ke boyewa. Idan tana tafiya kai ka ce rangaji take, komai ya yi masha Allah, komai nata danye ne sharaf. Jikinta kamar mai shiga wankin fata a inji, domin jikinta ya fi fuskarta haske. Ga zazzakar murya kamar diyar Shata, Fa’izah mace ce mai tsiwa, don in ta fara tsiwarta da mitarta har hacinta tsattsafar da gumi yake yi. Ba a yi mata ta kyale. Tana da kafiya da taurin rai, ba kankanin abu ke sanyata kuka ba. Tana da wuyar lankwasuwa a kan abin da ta kudurtawa zuciyarta. Watanni hudu kenan muna zaman garin Kano, ko in ce zaman jiran fitowar jarabawa, zama mai dadi da ma’ana. Hankalinmu a kwance, rayuwar baya duka ta zama tarihi, komai ya zamanto kamar bai faru ba. Don yanzu har na kan iya zama ayi hirar su Zanirah dani ayi dariya ba tare da na ji komai a raina ba. Zan iya cewa, soyayyar Yaya Aliyu babu ita ko kadan ta bace daga raina. Zamanmu da Yaya Rabi (accounter) a bakin G.T na Gyadi-Gyadi (branch) mun karu da abubuwa masu yawan gaske. Ga dai girke-girke na zamani muna koyo, kwalliya kala-kala, tattalin miji da nuna masa soyayya mai tsafta mai tafiya da ZAMANI da CHANJE-CHANJEN sa, tsafta, kissa da tarairaya, duk mun nade su cikin kanmu daga gidan Yaya Rabi. Wai yanzu ma kokari muke Hausar mu (accent) dinta ya yi dai-dai da na ‘yan Kano, domin masana luggogin Nigeria sun tabbatar da cewar Hausar Kano ita ce mafi karbabbiyar Hausa a Nothern Nigeria baki daya. Domin a lokuta da yawa in muna magana Yaya Rabi
Chapter 30 · 0% Book details