← Book details Zumuntar Kenan Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 62 OF 98

Sashe 62

Zumuntar Kenan Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

***
Da na baro Indoor Sport Hall Zaria na nufa a taxi bana ko ganin abinda yake gabana don tsananin takaici da tashin hankali. Fatana inga takardar sakin nan nawa da idanuna in karanta abinda ke ciki. Har aka zo kofar gidanmu ban sani ba ina sharar hawaye da dankwalin leshi na, sai da mai taxi ya ce.
"Hajiya, ba nan ne gidan ba?"
Na bude na fita na fiddo kudin da ban tsaya kirgawa ba na dai tabbatar yafi abinda zai nema na zube mishi a kujerar gaba nayi ciki.
Na danna kararrawa (door bell) Momi ta zo ta bude duka hannuwanta cude da fulawa ina jin alkubus take yi. Ganina haka hajaran majaran fuska babu alamun rahama ta tabbatar cikin ranta da kyar in ba (bomb) din ne ya tashi ba. Ta matsa min hanya na shige, ta koma kicin ta ci gaba da aikinta.
Gidan babu kowa sai Walid autan Momi, duk suna Kaduna cin biki. Na fadi nan bisa carpet na shiga kururuwa kamar na rasa iyayena biyu a lokaci daya.
Momi bata ce min cikanki ba, haka ko lekowa bata yi ba. Wannan ya kara kunna ni, na mike na shiga tamaula da kayan falon su filillikan kujera, flower rose. Ganin ina shirin yi mata ta'adi da kayan kallonta ta fito a fusace ta nuna ni da yatsa.
"Wallahi-wallahi ki kiyayeni cikin gidan nan, kinga dai babu kowa, babu mai kwatar ki don haka sai inyi miki dukan tsiyan da zai taimaka ya dawo dake cikin hankalinki, don da alama Fa'izah ke dabba ce, dabbar ma ta daji wadda bata san ciwon kanta ba. Allah Yasa Fa'izu yankan kai yake yi, ya yanke naki kowa ya huta wannan bala'in".
Na hade kaina cikin gwiwa bayan nayi fatali da goggoron.
"Momi bai kamata kice min haka ba, duk abin nan da nake yi saboda in kare mutunci da martabar ki ne daga idanun wanda bai san kina da su ba, don ni ta tawa mai sauki ce ban dauki kaina a bakin komai ba balle in dauki wulakancin da Fa'iz ya shekara yi mini abinda zai hana ni shakar numfashi a duniya.
Ba zan taba son shi ba Momi, ba zan taba ganin farinshi ba tunda ya wareki daga cikin iyayensa. Duk abinda yayi min a baya kin manta Momi...".
"...Na manta don ubanki, sai ki sani in tuna! Wallahi ki ka sake yi min kururuwa a gida sai na kakkarya ki, kin kuma koma inda ki ka fito kinji na gaya miki".
Sai na tura kai cikin kafafuna nayi ta rasgas kuka a hankali, babu mai lallashi balle wanda zan yiwa in huce. A kuma yanayin Momi na na tabbata zata aikata abinda ta fadi na sake na sake daga mata sauti.
A haka Babana ya taddani, ya zauna cikin kujera yana fadar.
"Kiyi kukanki mai dalili, yi kukanki da babbar murya Fa'izu bai sake ki ba! Da yake shi ya haifu cikin uwa da ubanshi ya san darajar iyayenshi da karfin ikon su a kansa. Allah Ya dawo dashi lafiya kafarki kafarsa, inda duk ya sanya kafa na rantse da wanda raina yake hannunsa".

***
Kwana biyu aikina kenan ina abinda naga shine rangwame a gareni wato (kuka) duk na koma jemammiyata ta baya a dakin Abdallah. A haka ne Ya Rabi da Ya Mufty, kan hanyarsu ta komawa Kano sai gasu a Zaria, Aunty Rabi ta shigo ta iskeni dakin Abdallah, ta aje mayafinta da babynta akan gadon Abdallah, ta ce.
"Kai! Fa'izah bakya gajiya, zuciyarki bata gajiya da kuntatawa kanta a banza a wofi alhalin hakan ba zai sa ba, kuma ba zai hana ba! Shin duka wannan na kiyayyar ne, ko na haushin Fa'iz dan albarka bai yi saki ba?"
Nayi banza da ita, can kuma na ce.
"Ki bani takardar in gani da idanuna".
Da murmushi fal a fuskarta ta ciro takardar a jakarta ta ce.
"Gata".
"Don haka in zaki hutar da kanki da zuciyarki to ki hutar, in kuma kina ganin kukan ki da tayar da hakarkari da hankalin ki shi zai sa Fa'eez ya yi saki to anan kam kinyi kuskure. Haka in ma duka da kwalba ne shima aikin banza za kiyi tayi don kuwa Fa'iz jinin Hajjah ne, rabin zuciyarta, magajinta. Idan ya ce 'eh' baya taba dawowa ya ce, 'a'ah'.
Shin don Allah in tambaye ki, meye abin ki ga Fa'iz?"
Na dago sharkaf da zufa, kashirban da hawaye da majina bayan na karanta takardar.
"Ai ba zaku taba gano aibunshi dani nake hangowa ba tunda danku ne, ba kuma ka taba ganin aibun danka komin muninshi ko munin halinshi. To tunda ba zaku gani ba da duk hujjar da na kawo to ni na tsane shi ne, bana sonsa, fakat! Da inyi zaman aure dashi gara min zama a dokar daji da bakin-kumurci. Allah da Ya halicce ni Shi Ya daura min kiyayyarsa da duk wani mai irin halayyarshi.
Yadda kuma ake ikirarin shi jinin Hajja ne baya magana biyu sai a gaya min in ni tawa uwar shege na tayi ta kawo muku".
Ya Rabi ta jinjina kai cikin kidima tana fadin.
"Babbar magana. Ni na kawo kaina, dama ba yadda Hajja bata yi dani ba kar nazo ke mahaukaciya ce amma banji maganar uwata ba dole naji wohoho! Sai ki mutu kuwa! Muddin Fa'iz ya dawo kafarki-kafarshi zuwa Russia, wallahi nima na daina lallaminki, mu zuba mu dake aga wanda ya haifi wani. Dabba kawai, shashasha, mara hankali".
Na ce, "Ko uwar Rasha ne ba zani ba, wallahi ba zani ba ko gunduwa-gunduwa za'ayi dani".
Rabi tayi dariya, "Ai har uwar Rashar ma zaki, tunda matukin jirgi kike aure ina ne ba za'a saka ki a jirgi a kaiki ba?"
Na ce, "Koda na rasa bawan Allah Dr. Nazir, mai ilimin da ya amsa sunan ilimi, banga me zanyi da direba ba Ya Rabi. Kamar ni in kare a mutumin da bai da ilimin komai sai na tuki? Direban tasha, wallahi na yi asara!!!".
Rabi ta ce, "Kin kuwa yi asarar. Yanzu ke ko babur zaki iya tukawa ne balle aje ga mota zuwa jirgi? Ke kinga shegen bakin ki baya mutuwa, ni na gaji da magana don ba malamar jami'a bace. Ranar da ki ka bi Fa'iz daga ke sai shi na tabbata murus bakin zai mutu mu don kin raina mu ne ki ka cika mana kunne da babatu. Don haka sai anjima, mijina yana jirana. Sai mun zo rakiya filin jirgi...".
Tamkar ta soka min mashi a kirji haka naji.
"Ko kuma an aiko muku da sakon mutuwar danku kunzo zaman makoki ba? Ki sani, ranar da duk Fa'izu ya yi gigin sake sako kafarshi cikin gidanmu kamar yadda na dauke kafata daga nasu gidan, wallahi sai buzunsa Ya Rabi!".
Ta ce, "Ko? Lallai kin fitsare, inama ina nan za'ayi wannan (BOXING)? Kai da na kadawa (Winner) tuta. In kuma kanwar ta kar tsamin ne sai kiyo min waya inzo jinyarki".

***
Zaman Zaria fa yayi min zafi, Walida, Abdallah duk suna makarantar kwana. Kausar da Walid makaranta suke zuwa safe da yamma. Babu Ummi babu Zanirah balle tsohuwa Hajjah mai samu farin ciki. Ko da yake Hajjah ni na gujeta don a ganina ita ce ummul-haba'isin sanya rayuwata cikin halin kuncin da take ciki bayan shafa min bakin jini da hakan ya yi a idanun iyaye da 'yan uwana.
Daga uwata har ubana kowa fushi yake dani, Walida kadai ke kula ni a gidan, haka nan kullum Baba zai fita sai ya ce.
"Tunda haka kike so, wato ga dakin uwarki ga naki, inta wuce dakina ki bita da ido kina kissime-kissime ai sai kiyi ta zama".
Wannan magana ba karamin kona min rai take yi ba, tun ina kuka har na saba. A zuciyata kuwa Allah Ya isa ga Fa'iz tafi dubu biyar.
Na rame, na fige, na zama 'yar firit dama jikin ba wani jiki ba. Nayi niyyar komawa Giwa amma na kasa saboda kurarin da nayi a baya cewa ba zan sake zuwa gidan Hajjah ba. Wuri daya ne nake tunanin idan naje zanji sanyi, wato wurin Maman Kaduna, to amma in ina da kunya ai bana dosheta ba alhalin kiyayyar danta na neman zauta ni. Ko babu komi ranar da Fa'izun ya ga damar dawowa me na isa nayi mishi akan idon uwarsa? Gara dai ya kwaso jiki ya kawo namu gidan.
Haka Zanirah da Aliyu suka yo min waya wai hakuri suke bani abinda suka yi min ranar bikinmu a Giwa su wasa ne suke min. Tsaki nayi na kife wayar nayi tagumi da hannu bibbiyu.
Bayan kwana biyu kuma, sai Ummi da Bashir suma suka bugo, amma su ba hakurin suke bani ba, korafi suke wai naki inje inga gidansu, to inzo in raka Ummi awo tana da ciki dan sati biyu.
Na ce, "Sai ku bari ya cika wata daya tukunna mu fara zuwa awo, kunji ko 'yan abu kazan uba marassa kunya".
Ummi ta ce, "Da fatan (this very big) ashar (is for me alone not with my husband) don mu albarkar miji muke nema ba ma zaginsa".
Watanni biyu suka shude tun ana zuba ido har kowa ya gaji babu Fa'iz babu duriyarshi, babu ko wayarsa. Don haka na yanke shawarar tunkarar Baba da shawarar da na yanke, wato komawa karatuna a Kano.

Da farko baban ya fara ne da zunduma min zagi bayan ya gama saurarona, kana ya ce.
"Sai dai in karuwanci kuma za ki sannan in barki, tunda kin ki zaman aure. Sannan ina mai tabbatar miki muddin ya kasance wani mummunan abu ne ya samu Fa'iz sakamakon raunin da kika yi mishi da kwalba, to ki tabbata sai na rotsa miki kwalbar 7up a wannan kodaddiyar fuskar da kike tinkaho da ita. Kazalika in Fa'iz yayi zuciya ne yaga cewa gara ya fasa auren, sai na dauke ki ke da kayanki na kai mishi sadaka, ko aikace-aikacen gida ne kiyi masa.
Chapter 62 · 0% Book details