Sashe 10
Zumuntar Kenan Part 1 Complete Hausa Novel · about 2 min read
gaki nan ba, sai an miki dabara za ki gun iyayenki”. Ta ce, “To ke kuma fa?” Na ce, “Ai ni dole ce tasa na barsu kema kin sani”. A gidanmu Momi na kicin tana girki muka yi mata sallama, ta washe baki tana yiwa Ummi sannu da zuwa ban da ni. Na ruga na rungume kugunta na ce, “Momi ni bakya nemana ko?” Muryata kamar zan yi kuka Ta yi ‘yar dariya dauke da wata irin matsananciyar kauna cikin kwayar idanunta, ta ce, “In neme ki in miki me? Su Walida basu ishe ni ba kenan?” Sai a lokacin na ga cikin Momi ya zama kato ya turo zani har baya kulluwa, na ce, “Momi haihuwa za ki yi?” Ta ce, “Me kika gani?” Na ce, “Cikinki na gani ya kumbura suntum”. Ta yi tsaki ta fice ta bar min kitchen din tana cewa da Ummi ta kashe mata heater din ruwan zafi mu fito mu rufo kofar kicin din. Walida ta zo kunnena ta rada min cewa, “Baba ya ce kanwa ko kani Momi za ta haifowa Kausar”. Muka kyalkyale da dariya. Dariyarmu ce ta sata juyowa ta dube mu, ta girgiza kai tana murmushi, na san sha’awa muka ba ta. A kullum ni da Walida kamar ‘yan biyu muke, domin Walida akwai manyan barage, sai dai ita fara ce tas ni kuma ina da duhu. Da ganin Walida ka san za ayi babbar mace mai babban jiki nan da ‘yan shekaru, ba mai cewa Abdallah ya girme mata da shekaru dai-dai har uku, don ni kaina ta dara ni jiki da tsaho. Haka yadda muke kaunar junanmu duka abin sha’awa ne wurin Mominmu da ta haife mu ma balle ga sauran al’umma. Duk kawaici irin na Momi a wannan hutun na fuskanci ta ji dadin zuwana, domin ban taba kai wa irin tsahon wannan lokaci ban je ba. Kwananmu biyar muka juyo Giwa da tarin tsarabarmu na tafiya makarantar kwana. A can muka tarar da Zanirah ta riga mu dawowa tuntuni. Washe gari Yaya Aliyu ya mai damu makaranta, amma duk da kayan da muka samo bai rage komai ba a sayayyar da ya saba yi mana, bai fasa komi ba. To haka rayuwa ta ci mana gaba tsakanin gida da makaranta. Duk burin iyayenmu ya ta’allaka ne a kanmu mu ukun nan da burin gina mana ingantacciyar rayuwa, kasancewar mu ‘yammata matasa kadai dake gabansu. Kauna ce muke gani daga kowanne bangare na iyayenmu, gata na duniya babu irin wanda bana gani daga iyayenmu, da kakarmu Hajjah da babban Yayanmu Aliyu Haidar.