← Book details Zumuntar Kenan Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 41 OF 98

Sashe 41

Zumuntar Kenan Part 1 Complete Hausa Novel · about 4 min read

ga Ummi, Mus’ab, Junior Yahya, Shu’aib, Walida, Abdallah da wata karamar yarinya mai tsananin kama da Fa’izah (Khausar), da sauran kannensa ‘ya’yan Baba Barau, Sadi, Salisu, Sani da Na’ibi. Mutum daya ce kawai babu, wato KANWAR kuma abokiyar fadan da a yau ta juye ta rikide zuwa matarsa ta sunnah. Ko da wacce irin fuska za ta karbi al’amarin? Ko da wace irin fassara za ta fassara shi? Ko da wanne irin hannu za ta karbe shi? Abin da ya sani ya kuma kwana da da sani ne cewa, Fa’izah! Ba ta da makiyi a duniya irin sa!!! To amma ai shi sonta yake yi tun can din ma. Har kuma gobe son ninkuwa yake yi irin kaunar da bai taba yiwa kowa a duniya ba, in ka dauke Mama da Baban Kaduna wato iyayensa. This is his own style of love! To amma da wane language (yaren) zai yiwa Fa’izah bayanin hakan har ta yarda ta fahimce shi, ta karbe shi a matsayin miji a gareta? Ya kuma wanke wancan dattin da ya dade yana yabawa kansa a idanunta? Don haka kallo daya za ka yiwa pilot Fa’eez ka karanto matsananciyar damuwa cikin fararen kwayar idanunsa. Duk da yaken da yake yiwa Aliyu da sauran ‘yan’uwansa. Yasa hannu ya karbi little Fa’izah hannun Zanirah ya dora a kafadunsa yana murmushi, kallo daya ya yiwa Ummi ya bude baki yana mamaki, ganin yadda kibarta ta zaizaye gaba daya, abin da babu wanda ya taba tsammani. Shi da ita murmushi suka yiwa juna, wanda ga Pilot Fa’iz murmushin ‘yan’uwantaka ne. Kuma ba annuri a fuskarsa har suka shisshiga motocinsu, yana motar Aliyu ne, Aliyun na tuki shi yana gidan gaba, Ummi da Zanirah da ‘yarta a baya. Sai dai tunda suka hau titin Zaria Road dodar wanda zai sada su da garin Zaria, kowa ya fahimci Pilot Fa’iz Bamalli cikin matsananciyar damuwa yake. Ya sanya fuskarsa cikin tafukansa Allah kadai ya san me yake tunani a zuciyarsa. Ummi ta yi tagumi a kujerar owner side da take zane. Wane irin mutum Fa’iz ya koma? Wane irin ango ne wannan babu wani alamar kulawa ko kwayar murmushi ga amaryarshi da aka daura musu aure yanzu-yanzun nan? Wane irin mutum ne shi da zai bar kasar haihuwarshi shekaru har shida da wani abu ya dawo babu alamun farin ciki a fuskarshi? Me ke damun shi? Anya Fa’iz na farin ciki da dawowar sa cikin ‘yan’uwansa? Anya Fa’iz lafiyarshi kalau? Anya Fa’iz na murna da auren su kamar yadda take tsammani? Ta jerowa kanta duka wadannan tambayoyin lokaci guda, ba ta da amsar ko daya, don haka ta sunne kanta cikin cinyoyinta ta soma kuka a hankali. Daga Aliyu, Zanirah da sauran kannensu dake cikin motar zuwa uban gayyar, babu wanda ya tambayi Ummi dalilin kukanta. Ga Aliyu shi kam abin ne ya zo mishi wani irin banbarakwai cikin sarkakiya. Bai san irin bayanin da zai ma kowannensu ba. Babbar fargabarshi yadda Fa’izah za ta karbi zancen aurenta da Fa’iz. A karo na farko ya ji haushin kansa kan munafuntarta da ya yi jiya, don me bai gaya mata gaskiya ba? Don me ya rufe mata? In kowa ya rufe mata shi bai dace da hakan ba. Ita kuma Ummi tunaninta da Fa’iz aka daura mata aure amma ganin halin ko in kula da ya nuna mata ya sanyata kuka. Shin da wane yare zai yi mata bayanin cewa da Bashir ne? Ya ya Ummi za ta tallafi maganar bayan yana da masaniyar cewar ta tsani halayyar Basheer fiye da kowa? Ta ya ya nitsattsiyar yarinya ‘yar kauyen Giwa ta cancanci tantirin dan duniya irin Yaya Basheer? Kaico da tunanin Hajjah! Kaico da bahagon tunanin iyayensu wurin hada irin wannan rikitacciyar auratayyar zumunci ko bata zumunci? Su kam sun haye! Yanzu na ‘yan bayansu yake ji. A zuciyar Zanirah cewa take yi, “Ina ma ban zo garin ba kwata-kwata balle in ga wannan rikitacciyar rana......!” A dai-dai lokacin da Aliyu ya karya kan motar cikin tafkeken (gate) din ABUBAKAR BAMALLI HOUSE.....”
Chapter 41 · 0% Book details