Sashe 23
Zumuntar Kenan Part 1 Complete Hausa Novel · about 1 min read
in ita ba ta ci girma ta bar min ba, sai dai duk mu rasa, ko duk mu samu. Zanirah ta mike ba zato ta kunna fitila dakin ya gauraye da haske. Ta shiga kallona tsaf, ba ta ce komai ba sai ta shiga toilet ta dauro alwala ta zo ta burma hijab ta hau doka nafilfili. Hankalina ya kara dugunzuma ya tashi, don a ganina Zanirah na rokon Allah ne a kan ya mallaka mata Yaya Aliyu ni ya hanani. Sai na kara rikicewa da kukan tun karfin gunjin da zan iya a hankali yadda sauran jama’ar gidan ba mai ji na. Ba shiri Zanirah ta sallame sallarta ta ce, “Fa’izah wai lafiya ne?” Na dan saurara da kukan na ce, “Na fara kukan rabuwar mu ne Zanirah....” Da alama ba ta yarda ba har zuci, sai ta yi murmushi ta ce, “Allah yasa hakan ne har zuciyarki. Da sai in ce rabuwa ta zama dole ai, tunda babu yadda za ayi mu dauwama tare a matsayin mu na ‘ya’ya mata. In babu aure akwai mutuwa, akwai kuma kaddarorin Ubangiji iri-iri”. Mu karasa a littafi na 2 Tare suke,Takori