Sashe 56
Zumuntar Kenan Part 1 Complete Hausa Novel · about 5 min read
A lokacin ne mutuwar da Ya Rabi ta ce min Dr. Nazir yayi ta dawo min danya sharaf, tuni hawayen dake makale cikin idanuna suka tsinke baki daya. Addu'a ce mai kyau ya yi ga masoyina na hakika, wato Dr. Nazir Sani Galadanci. Don haka na ce.
"Ameen Ya Rabbi".
A yayin da ya sanya kafarshi waje zai fita daga dakin. Wani sauti ne ya fito tun daga karkashin zuciyata na zuciyar 'yan uwantaka va tare da yayi shawara dani ba.
"Haka zaka fita kayan ka duk jini?"
Sai bayan na furta ne naji kunya da alamun nadama, sosai idanunshi ke nuna cikin juwa yake karfin hali kawai yake na duk maganar da yake yi, a hankali yayi murmushi ya dan juyo ya dube ni.
"Za suke tuna min da irin kyakkyawar sallamar da muka yi da matata (a da) kanwata FA'IZAH A.A GIWA. Don haka kada ki damu da su, ko nazo sanya (uniform) ba zan zubar da su ba, zan tafi da su har Great Britain". Yayi murmushi (a karo na biyu) “ki sanya kayan da Momi ta baki” ya fice da sauri.
Oho kuma wai inji wohoho! Kai ya shafa, ni dai tunda na rabu da alakakai falillahil-hamdu. Dama abinda yasa ni tambaya ganin yawan jinin ne tunda haka yake so meye ruwan Fa'izatu?
Momi ta dube shi a yayin da ya kai kofar fita zuciyarshi a jagule, ta ce.
"Yanzun Fa'izu haka za ka shiga cikin mutane kaya duk jini? Ka zo ga na babanku ka saka sai ka tafi".
Ya yi murmushin da Hausawa ke kira yake.
"Babu komai Momi, da naje (Airport) canzawa zanyi zuwa (uniform) ai".
Rabi ta ce, "Daga nan sai ina?"
Ya ce, "Ina da (interview) ne Aunty Rabi a kasar Birtaniya".
Idanun Rabi sukai rau-rau, hawaye na son zubowa ta ce.
"Haka zaka yi tukin jirgi Fa'iz da rauni a cikin kanka?"
Cikin kosawa da son ya tafi kafin likin da yayi ya balle, ya ce.
"Babu komi Ya Rabi, bi'izinillahi Rabbi".
Ta ce, "To baka hakuri da tafiyar zuwa sati mai zuwa kafin nan Fa'izar ta sakko ku tafi tare? In ta zauna nan me zata yi mana?"
Fa'iz ya sake murmusawa cikin takaicin kalaman Aunty Rabi, ya ce.
"Shin cikin ku Ya Rabi wa ke da jan wuyan sanyata ta bini ba ma gidana ba har wata duniya a yadda take ji da taurin kan nan? Yanzun ma dabara nayi mata muka rabu lafiya, ki rufa min asiri in tsallake in bar Nigeria Ya Rabi". Yasa kai ya fice abinshi.
Bai isa (Airport) ba sai ana kiran sallar magariba, a yayin da ya karya motar ya shiga filin jirgin ne zugin da radadin da tsakar kanshi ke yi ya tsananta. Ya kashe motar a wuri na musamman ya fita ya dauko jakar kayanshi na (boot) ya rufe motar, cikin sauri ya gama cike-ciken takardun da zai yi. A yayin da ya shiga (pilot's changing room) domin sauya kayan jikinsa zuwa na matukan jirgin sama ya tuna da abinda ya ce da Fa'iza, ya yi murmushi. A lokacin ne cikinshi ya soma kugi, wani irin kugi da bai taba yi mishi ba, yana tuna mishi rabon shi da kwakkkwaran abinci tun dirar shi Nigeria daga Russia. Yanzu kam da zuciyarshi tayi sanyi, hankalinsa ya kwanta da samun kalami mai dadi daga Fa'izah yana jin zai iya hadiyar abinci ko abin sha. Abinda bai taba samu ba tun tasowarsu (kalami mai dadi daga Fa'izah) ko da yake shima din haka bata taba samun rana irin ta yau daga gareshi ba. Don haka ya yi (marking) ranar (as precious). Wata rana mai dumbin tarihi a cikin ranakun rayuwarsa.
Fa'izah tayi kuskure da take tunanin zan iya sakinta koda daya ne balle uku rigis, saboda shima haukan da ake zaton mata ya sameshi ko me?
A yadda yake jinta a zuciyar nan tasa, yake jinta a ko'ina na ruhi da bargon jikinsa? Shi kam bai san ma yana son Fa'izah ba sai yau din nan, ashe ada hasashe yake, ba don wani kyawunta ko kyakkyawan girman da tayi ba, a'ah yin Allah ne kurum, shi ya daura masa ta yadda bashi da harshen da zai fassara soyayyar Fa'izah a zuciyarsa, tun ranar da ya bar Giwa zuwa kasar Rasha.
Ya tuna rotsen da tayi mishi, sai ya girgiza kai ya yi murmushi. Kuruci dangin hauka kenan. Fa'izah na ganin hargaginta da (power) dinta shi zai kwatar mata 'yancin da take so, har yaji tsoronta ya sake ta? Tsoron sa Allah-tsoron sa ranar da zai dawo gida Nigera daga wannan tafiya da zai yi wanda ya tabbata idan taji tsiyar da ya shuka mata a takarda ta nemi tsire shi da mashi, wannan ne hukunci na karshe da yake tunanin Fa'izah zata yanke masa in ya dawo.
Bai kai karshen tunaninsa ba (computer) ta shiga ankarar dashi lokacin tashinsu yayi. Za su tashi ne karfe uku na sulusin daren ranar ta Alhamis daga (airport) din Abuja zuwa Wales din kasar England ba kamar yadda ya kintata da farko ba, wato karfe goman dare, don haka lokacin haduwarsu da Majid ma ya canza don sunyi 'transit' a ‘Scotland'.
Karfe sha biyu na safiyar washegari suna Wales. Kowa dake cikin jirgin ya fita in ka dauke (pilot) Fa'iz Giwa, yayi shiru shi kansa bai san me yake tunani ba har saida wani abokin aikinsa ya ankarar dashi za'a rufe jirgin, sannan ne ya daura idon shi akan jakar kayanshi ya dauka ya mike ya fito.