← Book details Zumuntar Kenan Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 57 OF 98

Sashe 57

Zumuntar Kenan Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Monica da kawarta Divya, suna daga cikin fasinjojin jirgin da Fa'izu Abubakar ya biyo zuwa Scotland, zai sake kwasa zuwa Ingila. Sunzo ne musamman daga Abidjan domin halartar kallon wasan kwallon kafa na gani da ido a (Chelsea UK). Ta gabansu Pilot din ya gifta a (reception) jaye da 'yar jakar kayanshi a hankali akan (marbles). Tsakanin Monica da Divya, an rasa wadda zata fara dauke ido a kansa har ya kulewa ganinsu ya bi (lifter) zuwa (underground). Monica ta tabo Divya. "Kin sanshi ne? Irin wannan kallo haka?" Divya ta girgiza kai, "Kamar nasan fuskarsa, ya taba debo mu daga Paris zuwa Ukraine". Divya ta ce, "Bahaushe ne fa tamkar mu ba Balarabe ba, sai dai ta ko ina babu fuska". Monica ta hadiyi miyan da ya tsaya a makoshinta, ta dafe kirji ta rufe ido tana ta faman gyada kai kamar kadangaruwa, wata irin soyayya na cinta Fa'izun bai san suna yi ba wai kunu a makota. Sun hadu da Majid a filin jirgin saman Wales, ba abinda Majid ya fara hangowa sai lafceciyar (plasta) akan Fa'iz da goshinsa. Hannu ya mika ya rungumo kafadunsa suka karasa wani dakin hutawa na musamman dake cikin filin jirgin, suka zauna a tare cike da gajiya da tsamin jiki na kwanan zaune. Majid Abduljalal Balaraben Syria ne wato (Shaam), tare suka yi karatu da Fa'iz a Russia da Johari da wani bakar fata Solomon Bayaraben Nigeria (they are very close to each other) don haka sun san tarihin juna, sun kuma san damuwar junansu. Majid bai tabbatar ba, amma jikinshi ya bashi anyita ba dadi da Fa'izah. Hasashen shi ya hasaso mishi ita ce ta yiwa Fa'iz wannan raunin. Fa'izu ya ja numfashi ya sauke, da gasken-gaske cikin damuwa yake mai yawa, wadda ta kasa boyuwa akan kyakkyawar fuskar shi. Maajid ya bubbugi kafadunshi, ya yi murmushi ya ce. "WO-MAN! Inka fahimci kalmar ko? Tana nufin Wo! MAN ka shiga uku kenan!". Duk halin da Fa'iz yake ciki sai da Maajid yasa shi dariya, ya yi mai isarsa kafin ya ce. "Maajid! Maajid!! Ya aka yi kasan cewa Fa'izah ce ta rotsa ni?" Ya ce, "Oho maka wannan kuma! Ni dai na san kai ba makaho bane balle ince faduwa kayi ka ci da baka ka fasa goshi ka fasa kai, na kuma san ba dambe kayi ba aka fi karfinka da (giantness) din nan naka Fa'iz. Na kuma tabbata ba gidan giya kaje wani yasha ya bugu ku kayi rigima ya rotsa maka kwalbar ba". Sai ya sake tintsirewa da dariya, ya ce. "To amma saboda Allah me yasa ka kirani adai-dai lokacin da kasan ina tsakiyar yakin neman soyayya a tsakiyar rikici da Fa'izah? Shin ko kasan wannan kadan ne da ace ban yi mata karyar saki ba da ta kwankwatse ni gaba daya da gilasai?' Majid ya yi tsaki ya ce, "Kai ka so duka wannan shirme na Fa'izah. Ni kam yana daga cikin abinda ya hanani aure yanzu, wato fargabar irin macen da zan debo ma kaina, don ni dai ba zan auri matar da bata so na ba wallahi. Idan wani ya ki ka da wuni, wani da kwana zai soka. Ba'a san maci tuwo ba sai miya ta kare, don haka mu bamu fara cin tuwon ba ma balle miyar ta kare, yanzu ne muka fara laluben har sai mun lalubo mai son mu. Mu matuka jirgin sama, muna bukatar mata masu matukar son mu, wadanda kullum muka fita sai sun kai goshinsu kasa sun roka mana kariyar Ubangiji saboda kullum rayuwarmu cikin sadaukarwa take, za'a dawo ko ba za'a dawo ba. In zamu fita su faranta mana, hakazalika in mun dawo. Sannan ba nymphos ba (masu yawan bukatar Da namiji) ka gane? Don haka ne naga wautarka da rashin azancin ka wurin nemo auren yarinyar da tun fil'azal kai tafi tsana sama da komai a rayuwarta wai a matsayin (life-time partner) dinka. Kada ma kayi gigin kawo mana Fa'izah a yanzu, ta hada maka zafin da zaka tura rayukan al'umma cikin (solar-system). Ka barta tukun, zuwa wani dan lokaci har ta sauke zafin kanta". Ya yi murmushi mai hade da sautin dariya. "Yau Majid so kake ka kasheni da dariya. Da alama kana da (good experience) akan WOMEN din nan. To ga tambaya, shin ya za'ayi Fa'izah ta so ni? Ni dai (I can't do without her no matter what). Ko kasan duk haukan kiyayyar da Fa'izah ke yi a kaina bana jin ciwo? Ka san cewa har iyayena Fa'izah ta zage su tas akan idona ban ji komai ba, me yasa?" Da sauri Majid ya amsa. "Don kana sonta mana, so irin na halaka ga maza, wanda ya zarce halastaccen so ya hada da ribatar zuciya, so na fiye da kima don iyaye ba'a hada su da wata abar banza (mace). Duk da ance so hana ganin laifi to amma banda iyaye. (They made us what we are today! They are, therefore, incomparable to any worldly material). Ka farka daga gigin son nan Fa'iz ka zama jarumi akan Fa'izah kamar yadda kake jarumi akan komai. Sai dai in kiyayyar Fa'izah ta ci gaba wata rana zaka kita kaima. Kiyayyar Fa'izah a gareka ta yi yawa, tafi wadda ka ce kayi mata. Ni dai in ni Maajid ne bazan jure ba, mace ta fasa min kai... ta zagar min iyaye, mace! Mace!! Mace!!! Woman, Imra'ah! Ana maa Adhry!!! Macen ma wata karamar yarinya Fa'izah da ta tashi a kauye irin Nigeria? Ba zan dauka ba". "Baka taba fadawa a son Woman din da ka rainawa kura bane Maajid shi yasa kake duk wannan cika bakin da kake yi. Nima da irinka ne, haka nake da wannan akidar. Ban taba zaton akwai macen da zata sani zub da kaina ba sai da Allah Ya dora min lalurar ciwon son Fa'izah. Ko kasan har kasa na dire gwiwoyina ga Fa'izah? Maajid SO BA KARYA BANE. Sai dai ta wani bangaren ina cizawa ina hurawa. Iyaye duka iyaye ne a zuciyar kowanne Da na halak Maajid. Na zagi uwar Fa'izah yafi sau shurin masaki akan idonta a kunnenta kawai don bata fito daga family dinmu ba, ban taba tunanin yaya take ji a ranta ba, duk da yarinyar ce a lokacin. Kuma kasan saboda mene? Ba wani abu bane kawai Maman nata (we are not bloodly related). Babanta yaje bautar kasa yayo (secret marriage) da ita daga Taraba da yake na gaya maka a zuri'armu ba'a auren (outsider). Bayan wannan Aunty Mainuna bata yi min laifin komi ba, baya ga ALHERI. Ko kallon banza nayi mata murmushi take mayar min a da can tana fadin yarinta ce, idan na girma zan gane wani baya auren matar wani, itama bata taba zaton zata auri bazazzagi ba tana cikakkiyar bafulatana. Da Allah Ya tashi saka mata Maajid rana daya sai Allah Ya yiwa al'amarin nawa juyin waina da kaunar abinda ta haifa tun ranar da aka haifeta.......". Labarin mai tsaho ne Maajid, (just bear in mind I have reason to love and respect Fa'izah and her mother to such an extent, and I'm ready to do everything to undo the hurt I caused to them). In kuma ci gaba da jajircewa ga rike igiyoyin auren Fa'izah da duk iya karfin da Allah Ya halicceni da shi har sai na dinke ZUMUNCIN A.B family ya koma yadda ABUBAKAR BAMALLI ke son ganinsa, hakan kuma zai ci gaba ko babu tsohuwa Hajjah (to the last journey) insha-Allah, ni na lalata ni zan gyara, duk da ance ba'a bari a kwashe dai-dai, jikina na bani ni zan kwashe daidai Maajid, sai Fa'izah ta so ni fiye da sonda nake mata in Allah Ya bamu tsawon rai da lafiya". Jinjina kai Maajid yayi, ta wani bangaren ya yarda ta wani bangaren bai yarda ba. "To da ka dire mata gwiwoyin a kasa, ka roketa me? Ta so ka?" Ya yi dariya ya ce, "Ina! Karewa ma kwarjini tayi min na kasa fadin abinda nayi niyya". Maajid bai san sanda ya fashe da dariya ba. "Amma ka ba da maza Pilot. Zan so ganin wace ce Fa'izar nan da zata ki namiji kamar ka ko yankar naman jikinta yake yi kullum, sai dai in ba mace bace. Tukunna ma cewa nake shekarun yarinyar basu fi ashirin ba? In har kana da tsokar zuciya a jikinka Abubakar, kuma kana son in yarda kai namiji ne mai mazakuta a jikinsa ba bonono kake mana ba mata-maza ne, ka share Fa'izah kayi kamar ka manta da al'amarinta kada ka koma inda take sai nan da (atleast) watanni uku. A kalla Fa'izah tayi haukarta ta gama ko da bata bari duka ba to 80% zai ragu tunda ta zame maka mutu-ka-raba daga kai har iyayenku. Sannan ne zaka neman sulhu cike da juriya da kai zuciya nesa, ka hadiye duk wani borenta so zallah zaka yi ta (portraying) ka zama kalar tausayi ka nuna baka da katabus sai yadda aka yi da kai, ka kwanta kace “in takani za kiyi to ga bayan taka”. Amma yanzu abinda yafi haka ma Fa'izah zata yi maka indai labarin da ka bani can baya da yanzu gaskiya ne, UWA ba abin wasa bace, ai na dauka ita kadai kayi ta yiwa shakiyancin. Tunda kace ita Maman (have reason with you) baka da matsala da ita kun fahimci juna tuntuni. Wacece Fa'izah? Me take takama dashi da zata ce bata son ka Fa'iz baya ga kyawun da take da shi? Me aka yi aka yi ta? Sai dai in muna-mata ce ba mace ba wadda tasan me ake so a namiji. Takamar diya mace kowacce iri ce kafin a daura mata aure ne, amma yanzu Fa'izah ta zama nama, bata da sauran abin tinkaho. Duk yawan kiyayyar ta fa muddin ta dauki ciki Fa'iz ta kare, domin a lokacin ne zata shiga fargabar ba zata so danta ya yi maraici ba, kuma ba zata so a kirata bazawara ba, ko kada ku rabu ta rabu da 'ya'yanta, Zata shiga tunanin yanzu fa ta zama (second-hand) ba zata je gidan da babu mace ba, kuma kasan ba son kishiyar nan suke yi ba, kuma idan ta fita, ba zata samo yaro kamar ka ba ko da ta samu mara mata din. Zata shiga
Chapter 57 · 0% Book details