Sashe 25
Zumuntar Kenan Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
**** Ranar da muka zana takardar karshe wadda ta kasance ‘Islamic Studies’ na daga hannuwana sama na yiwa Allah godiya da ya nufe ni da kammala makaranta lafiya ba tare da na taba karya doka ko guda daya da makaranta ta kafa ba, ba tare da na taba batawa kowa da zama ya hadani da shi ba a kan sani, sai bisa ajizancin dan adam, kamar yanda ban taba yin laifin da aka dauki bulala aka shimfida a fatar jikina ba tsayin shekaru uku. Na dawo hostel na shiga rarrabar da kayana ga juniors dinmu, na rabar da komai nawa har sutturar da nake amfani da ita a makaranta ban bari ba. Ban bar komai ba sai ‘hankici’ na da sutturar jikina wanda ya zame min tamkar jarabi. Na rufa shi a fuskata a wannan ranar, na yi kwance bisa gadon boarding school kwanciyar dana kira kwanciya ta karshe a sakandire. Na juya rigingine al’amuran na gifta min tamkar majigi, kamar yau ne Yaya Aliyu ya kawo mu QUEEN AMEENA COLLEGE KADUNA. Yau ga Allah ya kawo mu ranar barin ta. Shekaru uku tamkar kwana uku. Kwanakin, satittikan, watannin da shekarun sun shude ba za su kuma dawowa ba. Sai dai al’amuran dake cikinsu masu yawa ne a gare ni da ba zan iya mantawa dasu ba. Tunanin tashin hankalin da zan je in taras a gida gobe ya addabe ni. Kowa ka gani a harabar makarantar ‘yammata ta Sarauniya Amina a washe gari bakinsa har kunne yake, farin ciki ya wadace shi. Sabanin ni da ta kasance bakar rana a gareni. Duk da dimbin tarihin da ranar ta ajiye min mai dadi ga iyaye da ‘yan’uwana. Baya ga kyautar wadda ta fi kowa Da’a da kulawa da al’amuran addini (Amirah). Ni Fa’izah Ahmad Abubakar Bamalli Giwa, na karbi kyautar dalibar da ta fi kowa iya harsuna biyu mafiya shahara a duniya, wato Turanci da Larabci. Wannan duk karami ne a kan yabon da na samu a kan kananan rubuce-rubuce na ‘Literature’ Littafina ARE VOWS MEANT TO BE BROKEN? Gwamnatin Kaduna ta saya akan kudi masu yawa, Sarkin Zazzau ya saya, dansa Yariman Zazzau Mansur Modibbo ya saya a kan kudi masu firgitarwa. Galadiman Zazzau ya saya, Iyan Zazzau ya saya duka don rabawa a labiraren makarantun sakandire na jihar Kaduna. Wai-wai-wai. Ni Fa’izah na ga hasken camera a wannan rana, kamar ta bikin sallah. Haka na hau steps na rungumo kyaututtuka da award dina na literature. Babu abin da ya daga min hankali kamar rashin matallafi ko wani da ya shafe ni da zai karbe ni ya nuna min kauna cikin dangina da ya fito daga dimbin mutanen da ke hall din. Wannan ya tabbatar min daga Giwa har Kaduna da Zaria babu wanda ya zo mana. A yayin da na ke saukowa daga ‘steps’ din saukowar na tafiya ne dai-dai da bugun zuciyata, hardewa nake ina rangaji kamar zan ci da baki. Kafafuwana da hannayena baki daya sun sage. Ko kowa bai zo ba na zaci Yaya Aliyu zai yi kokari ya zo a wannan rana. A yayin da nake cikin wannan hali na takaicin rashin ‘yan’uwana, a yayin ne Ummi ta ratso daruruwan mutanen ta iso gareni ta tallafeni ni da kyaututtukana duka ta rungume mu muka karasa mazaunina tare, ana sakar mana hasken camera da saitin vedeo. Bayan taro ya watse na hangi Ummi can nesa dani tana magana da fadawa. Na cira kafa na ci gaba da tafiya rungume da kayana. Ba wasu kaya bane kyaututtukan da na samu ne da jakar takarduna rataye a kafada ta, sai hankcina a hannun hagu ina mai share gumin babu gaira babu dalili dake shararo min, abin mamaki tun daga tsakiyar kaina gumin ke tsattsafowa yana biyo goshina. Ummi ta biyo ni da sauri har tana hadawa da gudu-gudu don ta cimmani kamar babu abin da ya faru tsakaninmu, ta ce, “Ya kika taho kika barni Fa’izah? Kinga abin mamaki babu wanda ya zo mana anya lafiya?” Na kalle ta kawai na ci gaba da tafiyata. Daga bisani ganin ta jeru dani muna ci gaba da tafiya sai na ce, “Ai ina ganin Ummi tafiyarmu tare ba za ta yiwu ba, don ni nan Zaria na nufa”. Ummi ta dube ni baki sake ta ce, “Ki je Zaria ki yi me?” Nima cikin mamaki na ce da ita, “Ah! Mutum da gidan ubansa har a tambaye shi abin da zai je yi?” Ta ce, “Ban fahimce ki ba, amma ko ina dai za ki kafata-kafarki, don yau wata haka-haka nake ganin ki”. Na ce, “Haka-haka kamar ya ya? Na yi miki kama da sabon kamu kenan”. Ta ce, “Allah ya baki hakuri, ni ban ce ba, amma muje sai a kaimu Zariyar ko kuwa?” Na dube ta da mamakin yadda ta manta mun samu sabani a junanmu. A raina na ce “Shin Ummi kina tunanin zamu koma kamar da alhalin kina son makiyina ni da uwata?” Ban ce mata komai ba muka rankaya zuwa bakin titi. Mun yi tsayuwa fiye da ta rabin awa babu taxi, in ma sun gifta mu a cike suke. Ban so zan yiwa Ummi magana ba, amma hakan ya zame min dole. “Kawai mu hau okada, tunda ba wasu kaya garemu masu yawa ba”. Hakan kuwa muka yi. Ban ga kowa a harabar gidan Baban Kaduna ba, babu motocin Baba ko daya, babu yara ko daya masu yi mana oyoyo idan mun zo! Tun daga nan gabana ya soma faduwa, na fiddo naira dari biyu na baiwa masu okada muka karasa bakin gate muka gai da Malam Hassan maigadin gidan. Ya ce, “Ku kadai kuke tafe?” Har muna hada baki wajen cewa, “Eh, wallahi Malam Hassan. Ina jama’ar gidan suka tafi ne? Mantawa aka yi yau muke graduating? Babu wanda ya je mana daga Giwa, Zaria har nan cikin Kaduna?” Ya ce, “Hala mantawa kuka yi yau ake daurin auren Zanirah da Alh. Aliyu???” Wallahi baya ga wannan ban sake jin komai ba, ban sake sanin inda kaina yake ba. Sai tsintar kaina na yi a asibitin Jinya dake cikin garin Kaduna, Ummi na gefen kaina tana mini firfita. Na soma kokarin tuno abin da na ji (DAURIN AUREN ZANIRA DA ALIYU). Na fashe da wani gursheken kuka a cinyar Ummi, ita ma Ummi kuka take, na tabbata kukan tausaya mana ne ni da Yaya Aliyu, cewa take “Ya aka yi haka Fa’izah? Garin ya ya ni ban san zancen ba? Ya ya aka yi haka? Na dauka ke za a baiwa Yaya Aliyu?” Na mike zumbur ina layi na ce, “Ummi ya zama dole in je Giwa a yanzun nan, dole ne in je Giwa kada Zanira ta dauka ina bakin cikin auren ta da Yaya Aliyu ne, ta wuce haka a gareni, tashi mu tafi Ummi”. Ummi ta share hawaye ta mike, halin da nake ciki ne yasa ban bambance motar suwa muka shiga zuwa Giwa ba, ashe motar Yariman Zazzau ne Mansur Modibbo wanda ke biye damu da abokinsa tun daga Queen Amina har Jabi Road. A kan idonsu na fadi, kuma su suka kawo ni asibiti tare da Ummi. A hanyar mu ta zuwa Giwa Mansur ya ce, “Shin wace ce ita wannan Zanirah da labarin aurenta ke sumar da Fa’izah yake sanya Ummi kuka?” Maganar tashi sai ta bamu dariya har ni da ke cikin hali na kaka-ni-kayin zuciya. Ummi ta ce, “Duk wani bayani da zan yi maka a yanzu ranka ya dade ba za ka fahimta ba, Zanirah is our bloody sister”. Ya ce, “To na hakura da jin wace ce real Zanirah sai na dawo. Ni dai fatana Ummi don Allah ki rinka shigar dani kin ji? In na kai ku yanzu juyowa zan yi sai sati mai zuwa zan dawo, saboda zan yi tafiya zuwa Abia State na san kafin lokacin Fa’izah ta dawo normal!” Ni kam kallon shi ma ban yi ba fuskata na cikin cinyoyina, tunda na rasa Yaya Aliyu babu abin da zan nema a wani Da namiji, domin ko kusa ba zan samu mai hali abin so da irin kyakkyawar zuciyarsa ba. It’s indeed a great loss! Addu’a nake a cikin zuciyata, “Ya Allah ka sanya min hakuri da dangana, ka bani juriya da karfin zuciyar fitar da Yaya Aliyu Haidar daga Zuciyata”. Dai-daikun jama’ar da na gani a harabar A.B Estate ya tabbatar min har an gama daurin auren Zanirah da Yaya Aliyu! Wayyo Allah ni Fa’izah na rasa Yaya Aliyu kenan, tabbas na rasa shin, na hakura har ga Allah daga yau na bar wa Zanirah Yaya Aliyu. Sunan Allah Ya zuljalali wal ikrami nake taunawa a harshe da hakorina. Babu shakka zuciyata ta yi sanyi illa jikina dake faman karkarwa, amma a kan fuskata farin ciki ne bayyananne. Ni kadai na yi sallama falon Hajjah domin na baro Ummi waje tare da su Mansur Modibbo wanda su da gaske suke neman iri suka zo gidan Bamalli. Lallai iska na wahalar da mai kayan kara (na fada cikin raina). Gaba dayansu ‘ya’yan Hajja Hadiza su goma sha biyar in ka dauke Yaya Rabi auta dake Kano, Baba Muntari, Baba Na’ibi, Baba Ibrahim, Baba Barau, Baba Sadi, Baba Sani, Baba Salisu da su Yaya Hauwa, maza goma mata hudu kenan, duka zaune falon Hajjah wanda yake makeken gaske suna tattaunawa ko a kan mene ne oho! Na tsugunna na gaida su daya bayan daya. Hajjah ta ce, “Yar albarka, kuna raina wallahi, yanzu nake cewa a je a dauko ku don ita kanta amaryar yanzu ta shigo daga tata makarantar?” Ni dai na ce, “Uhm! A raina na ce, ‘dole ki ce min ‘yar albarka mana tunda kin san yankan bayan da kika yi min, kin barni da cizon yatsa.... ai dole kisa min albarka!’ Amma a fili sai na ce, “Wallahi kuwa mun yi mamakin rashin zuwa kowa, sai da muka je Jabi Road, Malam Hassan ke gaya mana daurin auren Yaya Aliyu da Zanirah ake yi, shi yasa ma bamu damu sosai ba muka taho da kanmu kawai”. Na mikawa Babana kyaututtukan da na samu cikin ledar Ghana must go da cheque din kudaden da na samu. Su Baba suka shiga dubawa suna kwararamin albarka tun karfinsu. Sai dai duk abin nan da ake na lura Yaya