← Book details Zumuntar Kenan Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 78 OF 98

Sashe 78

Zumuntar Kenan Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

*** Cikin wannan yanayin kwanaki suka ci gaba da mirgina mana har muka kwana goma, ranar Juma'a da yamma naji kugin mota, sai dai ba irin na motar Fa'iz bane. Na mike na daga labulen falo, sai na hangosu Walida, Shu'aib, Yahya, Junior, Abdallah, Kausar da sauransu suna fitowa daga mota, direban Mama Malam Sani ya kawo su, kowanne da 'yar karamar 'troller' din dana tabbata kayan sanyawarsu ne a ciki, yadda dai na gansu a gidan Ummi. Wani irin farin ciki naji ya rufeni don dama ina fama da kadaici da kewar su. Har da hadawa da gudu wurin bude musu kofa, kowanne yabi lafiyar kujera yana wash-wash, 'ya'yan hutu malam. Manyan su Shu'aib ne kawai basa cewa wash din, sai gaisheni cikin girmamawa. Na nunawa Junior dakin dake kusa dana Fa'iz shima (bedroom) ne (single) ba falo, ba abinda babu na ce su mazan su kai kayansu can, matan suzo mu hadu a nawa dakin sai ina-naka-saka nake dasu. Kausar ta kwantar da kanta a cinyata kasancewarta shiru-shiru ba kasafai ta fiya magana ba. Na ce, "Wai daga ina kuke ne?" Walida ta ce, "Gidan Aunty Ummi". Na ce, "Tun (last week) dana baro ku kuna can?" Suka ce, "Eh". Kausar ta dago kanta daga cinyata ta ce, "Koro mu fa suka yi ita da Yaya Bashir, yau ya dawo bayan hutun mu bai kare ba". Abdallah ya ce, "Kora da hali dai ba kora ta ku tashi ku tafi ba". Nayi musu kallon son jin karin bayani, dariya na son kama ni. Walida ta dora bayani. "Saboda Yaya Bashir ya dawo ta barmu a falo tun safe, sannan bata dora mana (break) da wuri ba, suka kyalemu yunwa na cinmu. Da ta fito bata hada mana ruwan wanka ba, ta ce kowa yayi da ruwan sanyi wai hitar (toilet) din gidan duka ta lalace. Ki dubi sanyin nan da ake. Shi kuwa Yaya Bashir din kai tsaye daya fito ya ce mu hada kayanmu mu koma gida, wai mun cika mishi kunne". Dariya nake kamar cikina zai fashe, Walid ya karasa. "Tunda dama hutun sati biyu muka je sai yaya Junior ya ce muzo nan kawai mu karasa kwana biyun mu sai mu koma gida, don dama Monday duk zamu koma (school) ke kam mun san ba za kiyi mana abinda Aunty Ummi tayi mana yau ba". Na janyo autan Momi jikina ina dariya, "Ina kuwa zanyi muku Walid? Ni farin ciki nake da zuwan ku, inma kun dawo gidan kwata-kwata ne (you are most welcome) dakunan gidan zasu ishemu". Duk suka hau murna sosai. Na ce, "Yanzu me zaku ci?" Abdallah ya ce, "Chicken burger?". Yahya da Junior suka ce, "Shinkafa da salad". Shu'aib ya ce, "Quaker oat kawai zansha da 'peak' ta ruwa". Kausar da Walid suka ce, "Wake da shinkafa da mai da yajin tafarnuwa". Taashin hankali gobarar gemu, (inji hawwa lawan meturare) tawa ta sameni ni Fa'izah. Na fada cikin raina, naja numfashi. "Uhm! Gaskiya abin naku (is too much). Dankari! Sunan wata jarida, dole Ummi tayi muku kora da hali har da sandan ma in tana dashi, in haka kuke kullum to tayi bala'in kokarin rike ku har kwana goma. 70% na abubuwan da ku ka lissafo bani da kayan hadinsu, kuma ko inada su jikina akwai jini da bargo ba zan iya ba. Chicken burger da Indomie kawai zan yi muku dukkan ku. Shi kenan?" Gaba daya suka ce, "Eh, ya isa". Banda Yaya babba (Shu'aib) shi harar su ma yake, ya ce. "Ai basu da hankali ne". Na ce, "Naga alama Yaya Shu'aib". Gaba dayanmu muka shiga (kitchen) banda Shu'aib, aka zage ana aikin hada burger, mai yanka tumatir da salad daban, mai baking da blending tsokar kazar da za'ayi amfani da ita shima daban. Haka mai tsaga biredin da shafa masa mayonnaise da salad cream shima daban. Nan da nan aiki ya kammalu kowa da (plate) dinsa ina ta rabo Fa'iz yayi sallama ya shigo. Sai kuma ya tsaya turus! A bakin kofa yana kallonmu, hannunsa dafe da habarsa. Yake fadi cikin kidayawa da dan alinsa. "1,2,3,4,5,6,7... duk a dan gidana? Ina zamu kaiku? Gaskiya ba zai yiwu ba, ba kuma zata sabu ba wai bindiga a ruwa. Banda dukkan ku taron mahaukata ne ana zuwa gidan mutane ba (notice in this century?) Kuma wai kwana? Ba daya ba har biyu? (Look at you all with your noses like hippopotamus's". (Dube ku duka hancinanku kamar na bauna). Suka aje lomar burger hankali tashe, rai bace. Ya samu kujera ya rage tsawo, ya dora kafa daya kan daya yana karkada 'yan mukullayen motarshi, ya sake fadin. "Wai da ba gidan Ummi na ganku ba?" Walida tayi rau-rau da ido, "Ai sun koromu...". "Au, shi ne ni aka zo aka tare min? Ga gidan dan iska ko? Abokin wasan ku?" Suka yi shiru tsuru-tsuru dasu abin tausayi, da alama wani abu ya bato masa rai a waje yazo ya huce a kansu. "To kuje kuci abincin duk kuzo in kaiku Jabi Road, ba mai kwanar min a gida". Kausar ta sha mur, Abdallah ya turbune, Junior ne mai karfin halin musantawa. "Haba don Allah Ya Fa'iz! Ka barmu mana? Don kwana biyu kawai?" Yahya ya yi kicin-kicin da fuska, "Kaima in kaje gidanmu ai Mama bata korar ka, daki ma take baka". Fa'iz ya fiddo ido waje saura kadan dariya kufce mana ni da Shu'aib, ya ce. "Kuji min marasa kunyan yara, ina fade kuna fade? To wallahi ba zaku kwana ba, ko ana dole? Bana son bakuntar, aje na gode. In ba wuni ba kada wanda ya kara zuwar min gida kwana, OK?" Tsit suka yi, sannan suka karasa cinye abinda suke ci. Duka suka mike cikin sanyin jiki suka dauko jakunkunansu suna ja a hankali duk suka bani tausayi. Wato mai hali baya fasa halinsa. In ka jima baka hadu da mutum ba, tambaye shi wani abin amma banda halinsa. Shi kuma irin tasa ZUMUNTAR KENAN! Idanuna suka cicciko da kwalla amma na rantse ba zanyi magana ba tunda nasan don inyi maganar ne kawai da bashi da alfarmar samunta haka kawai shi ne yake neman dalili. Suka yi waje, ya tashi ya bisu yana, "Oya! Kuyi sauri ku shige muje". Kamar ya samu wasu tumaki, haushi da takaici ya sake kamani. Na kudurta a raina duk yadda za'ayi yau ba zan gasa kazar da (chips) ba ladan korar min kanne. Sai dai nima ya kore ni. Anan kan kujerar da nake zaune ina sakawa da kwancewa barci ya kwasheni, har ya dawo ya rufe ko'ina ya kashe kayan wuta ban sani ba. Sai ji nayi yana tashina ta hanyar kiran sunana da jan babban yatsan kafata. "Yaya banga (chicken) akan (dining) ba?" Na mike na kalle shi cikin matukar fushi amma na kasa magana, na mike tsam kawai na shige dakina na rufo kofa, garam! Da safe ma kin fitowa nayi in dora karin kumallo duk da jiya ya ce in dora da wuri zai je Abuja da sassafe kan visar sa. Har bakwai da rabi ban bar gadona ba, duk da ba barci nake yi ba. Ya tabbatar bazan fito din ba balle in bashi ko ruwan zafi, sai ya iso kofar dakina yana balle 'links' din hannun rigar shaddar 'hilton' dake jikinsa fara sol. A bakin kofar ya tsaya yana fafin. "Ran Aunty Fa'izah ya dade, an tashi lafiya?" Shiru babu amsa, don haka ya dora gundarin bayaninsa. "Jiya nasan ban kyauta ba dana kori su Junior. Ina da dalilai na nayin hakan (which are all for our own goodness: Na farko kin sani Allah bai halicce ni da son hayaniyar yara ba. Na biyu ke ba kirki ne dake ba abubuwan da kike aikatawa ba lissafi a cikinsu, yaran nan kuma suna da fahimta sannan basu da mantuwa, gasu da daukar zance komi aka yi akan idanunsu sai ya koma kunnen Mama da Baba. Hatta rotsen da kika yi min a (Area One) Yahya ya gayawa Mama Junior ya gayawa Baba na kuma rasa ta inda suka jiyo. Haka kike so suje suce kina hararata, ba kya kulani wani zubin har tsaki kike mini komai da ya kamata ace mata na yiwa mijinta ni sai na roka sannan a hagunce ake yi min...". Tsakin da baya so na sake saki na juya masa keya na ba banza a ajiyarsa. Kai ni surutan da yake yi ma sun isheni nasa hannu na toshe kunnuwana. "Ina (breakfast) dina? Na gaya miki Abuja zan tafi". "Banga damar girkawa ba". Ya ce, "To Allah Ya bamu rai da lafiya". Na ce, "Amin Ya Rabbi". Ya juya ya fita ya janyo min kofar a fili, na ce. "Umma ta gaida Assha". Bai jima da fita ba na mike nayi bayan gida wurin Dawisu don basu abincin safe. Ina watsa musu hatsi daga nesa suna kara matsowa gareni cikin alamun nuna sabo, wato sun fara ganeni. Ya'u ya iso ya gaida ni ya ce. "Aunty na kawo cefane yana can kofar falo". Na ce, "Ina godiya Ya'u, anjima a sake musu ruwa, wannan ka gani duk yayi kura". Dariya abin ya baiwa Ya'u, amma sai ya ce. "Aunty kina son 'yan gidan nan naki, zan kara himma wurin kulawa dasu". Na ce, "In kayi hakan kaima Allah zai kula da kai". Na koma na kwashe cefanen da ya aje dokin kofa na shiga (kitchen) na adana kowanne a muhallinsa. Fa'iz bai dawo ba sai dare, sanda ya shigo gidanma bacci nake, ban san ya shigo ba. Na fito ne da daren don samawa cikina abinda zai ci naji yana kwalamin kira kamar tashin duniya. Duk da na firgita da irin kiran amma na share na shige kicin sai gashi ya biyo ni (kitchen) din a sukwane hannayensa rike da tulin hotuna. Fusatar dake fuskarsa ba zan iya bayyanata ba. Ta gefen ido nake kallonsa ina ci gaba da abinda nake yi, sai ji nayi ya finciko ni ta baya, saura kadan in fadi Allah Ya taimakeni na dafa (cabinet) na mike a lokacin na lura hotunan da Surajo ya kawo ne rike a hannunsa, fuskarsa a murtuke, idanunsa sun kada sunyi jajir yake magana harshensa na sarkewa. "Meye na daukar hoto da Suraj haka (very so close) har jikinku na gugar
Chapter 78 · 0% Book details