← Book details Zumuntar Kenan Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 34 OF 98

Sashe 34

Zumuntar Kenan Part 1 Complete Hausa Novel · about 1 min read

****
A gida nake bai ma Yaya Rabi labarin karonmu da sabon laccara mai tangardar harshe. Ummi ta ce, “Na ko so in ganshi, baki dan kakkaura mai yanayi irin na Yaya Bash yana driving wata (vauxhall) shudiya. Gaskiya gayen ya yi a rayuwa Aunty Rabi. Sai dai na yi mamakin yadda karamin yaro kamar wannan ya kai ga matsayin senior lecturer?’
Rabi ta ce, “Meye abin mamakin a ciki? Mai first class ko 2.1 zai iya zama lecturer komai kankantar shekarunsa. In kuma a waje ya yi karatun speed din ba daya bane. Mufty shekara daya kacal ya yi masters a Aston University”.
Ummi ta zaro ido ta ce, “One year Aunty Rabi?”
Ta ce, “Baki bina bashin rantsuwa ki shafa ki ji wai shafa-labari shuni”.
Chapter 34 · 0% Book details