← Book details Zumuntar Kenan Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 52 OF 98

Sashe 52

Zumuntar Kenan Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

**** A uwar dakin Mama take lallashin Bashir yana kunkuni cewa yake. "Aure? Aure?? Wane irin aure yanzun nan haka sabida Allah, mutum yana tsaka da cin kuruciyar sa, ko an gayawa Hajjah zamanin da irin na yanzu ne? Kuma a rasa wanda za a aurawa wannan lukutar yarinyar mai shegen qarfin tsiya sai ni? Salon in na mata ba dai dai ba ta hau ruwan cikina yadda take danne su Zanirah? To ni yanzu ma daga gama karatu ban kama aiki ba anzo an dora min aure, ku ne za ku dinga yi min dawainiyar auren? Sannan ni wallahi ba zama nazo yi ba, na zo ne kawai in ganku in koma. Dama ace 'yar siririyar ku ka aura mini 'yar wajen Baban ABU sai in karva da godiya, me ma take ne da suna Fa'eez?" Fa'eez dake gefe ya juya musu baya yana kallon tangamemen hoton Fa'izah da Zaneerah, sun sha goggoro ranar bikin Zanirah da Mama ta kafa a falon, ya wani irin juyo cikin (slow-motion) ya qwalalowa Bashir kyawawan idanunshi, ya ce. "Yaya Bash! Ahir! 'yan iskan idanunka bisan matata! Na gaya maka, na qara (warning) dinka, o.k?" Mama ta dafe kai, "Fa'iz, yaushe ka koyi rashin kunya ne for Allah's sake waye baya kuskure a bisa rashin sani? Ka bari Bashir ya dora idonshi bisan ummi kamin ya yi wadannan sambatun banzan mana. Bashir, kana magana ne akan wasu kwailayen yara mitsi-mitsi daka tafi ka bari shekaru takwas a baya da suka wuce. To wadannan...". A yayin da ta miqe ga daya 'enlargement' din dake can hanyar kofar fita na Zanirah da Ummi, shima ranar bikin Zanirah ne sun sha ankon beig swiss laces mai ratsin silver da goggoro kalar adon leshin, wato (silver), wanda in ba ka daga idonka sama ba baza ka hango shi ba saboda anyi (placing) dinsa da nisa, ta taka kujerar cin abinci, ta dauko ta sauko fuskarta cike da annuri ta dora ma Yaya Bash akan cinyarsa. "Ga Ummin Hajjah". Bashir ya kurawa Ummi ido na 'yan dakiku yayin da kalmomin da suka shiga fita daga bakinshi bai san dasu ba... "How does this girl turn to slim?" Duk da tension din da Fa'iz yake ciki wanda Bashir din ya hada masa sai da dariya ta kama shi, ya yi murmushi cikin takaici ya tashi ya bar dakin yayin da Mama ke kyalkyala dariyar jin dadi tana kallon idanuwan Bashir da ke neman zazzagowa akan hoton. A ranta ta ce. "In banda anfi karfin Ummi me zata yi da Bashir don Allah? Ita kam tana fatan Ummi ta zam silar kimtsuwar xanta daga halin da ya tsunduma kanshi babu gaira babu sabar, don duk komi yana dawowa kunnenta, duk da Fa'iz ba duka yake gaya mata ba sai dai ya ce tayi masa addu'a, ya canza hali rana daya. Ta daga hannu sama ta godewa Allah Al-khaliku sarkin qaga halitta da ya suranta Ummi kirar da ta fi karfin namiji ya wulakantata. Ta sani da yawa kamilallun mata 'ya'yan gidan tarbiyya suke shirya mazajensu masu mugayen dabi'u irin na Bashir, don haka ta kara godewa Hajjah tare da binta da kyakkyawar addu'a a zuciyarta na Allah Ya ja kwananta cikin zuri'arta har kansu (junior) ko ana so ko ba a so. Allah Sarki Maman Kaduna, a wannan ranar bata yi bacci ba, kwana tayi akan kafafunta tana kai sunan Fa'iza ga mai duka, kan ya karkato da hankalinta taso Fa'izu. Mama hawaye take da idanunta, a yayin da take rokon mai cusa soyayya da ya cusa soyayyar Fa'iz a zuciyar Fa'izah. Soyayyar da babu kamarta a duniya wadda ta fi gaban wadda take yiwa Nazir Galadanchi. Babu abinda ke damun Mama irin ganin yadda Fa'iz ke neman ya susuce kamar baya ji sosai, sai kayi magana sau uku kafin yasan da kai a gabansa, tunani yake ko da yaushe. Tun dawowar shi bai iya ya tsaya ya ci wani ginannen abinci ba kullum sai tea, lemo, snacks. Jiya kam da ta shiga boys qutarers nemansa yana wanka ta tadda hotunan Fa'iza sunfi kala goma anyi enlarging dinsu an kafa a kowanne kusurwa na daki da falonsa, musamman cikin bedroom, tayi tunanin ina ya samo hotunan? Da ta tambayi Yahya ya ce shi ya aika ya karba mishi wurin Walida. Mama kam ta tabbatar hakkin Fa'izah ne ya kama Fa'iz. Babu mamaki in ya tuka jirgi a wannan lokacin ya saito shi cikina garin Giwa wanda hakan babu makawa zai murkushe musu dan garin na iyaye da kakanninsu da bai taka kara ya ba balle ya karye. Mama ta tabbatar nutsuwar Fa'iz kawai samun zuciyar Fa'izah, ko da bai furta ba bai kuma nuna (weakness) dinsa ba, har gobe Fa'iz Abubakar, namiji ne mai amsa sunan namiji ko a cikin daruruwan maza baka fiya gane (weakness) dinsa ba, balle akan mace. Ita din ma don ta sa mai ido ne, amma da fatar bakinsa bai furta mata ba. Wanda hakan kuma (samun zuciyar Fa'iza) ba shakka ba karamin aiki bane ga duk wanda yasan Fa'izah da Fa'izun wurin kafiya da taurin kai. Wadannan sune halayen da Hajja ke hange har take ganin hada masu irin halayyar gamayyar aure shi ne dai-dai. A yau kam Mama ta qalubalanci tunanin Hajjah akan-kanta. Hada masu halayya daya aure cikin A.B ba dabara bace so-karvau. Zanira da Aliyu kam hadi ne na Allah, laushi na dukan taushi. Amma masu taurin zuciya da kafiya ba dai-dai bane hadasu aure, in daya ya taso daya ba zai sauka ba, haka in daya ya hau daya ba zai yarda ya fado kasa ba yayi lallami ya kaskantar da kai ba ga dan uwansa. Yadda Fa'izah ke ganin ta watsar da kanta inta kwantar da murya ta roki Fa'iz SAKI, haka Fa'eez Giwa ke ganin zub da kima ne da aji, muddin ya kwantar da kai ya baima Fa'izah haqurin abinda ya yi mata a baya. Duk da abin ya zo ya zame masa jidali, ya hana shi ci, sha da sukuni da jin dadin komai dake cikin rayuwar duniyar baki daya. Ya hana shi barci da walwala balle komawa bakin aikin shi. Don haka Mama ke addu'ar Allah Ya sauke na Fa'izah, domin muddin Fa'izah ta sauke dole ne shima Pilot din ya sauka. To a washegari ne kuma Aliyu ya kada mata 'ya'yan hanji da albishirin gudun Fa'izah. Bata iya ta fadiwa Fa'iz ba sai dai shi a lokacin ya damu da ya ga Fa'izah ko da gani da ido ne a kalla zai samu sauki daga azabtuwar da zuciyarshi ke yi a dalilin rashin ganin nata, inyaso ko ganinta ya yi kawai daga nesa ya haura takalmansa ya bar mata garin da kasar baki daya, in ta rage bala'in ta bishi Amsterdam su zauna. Indai sun kasance gida daya ai maganar kafiya da kiyayya sai ayi ta yin mai dalili, ba yanzu da ko harararta baya hange ba. Ya kurawa jerin jakunkunan da ya danqara dalolin shi ya sayo da sunan lefe ido. Shin wacce Fa'izah yake tunanin za ta daura zaninshi? Ko da yake a lokacin yana kan aiki a Istanbul ne, giyar son ta buge shi, ya shiga hada su a kasuwar (AKMERKEZ Shopping Mall) ba tare da ya yi shawara da kowa ba ko yasan 'size' da take amfani da shi a yanzu. Ya dubi shekaru ne kawai ya kintata, kuma da ya ganta bata zarce yadda ya kintatan ba. Ya bude yana duba su a hankali har da (underclothes). Fadin abinda ya kashe akai bata baki ne, amma ta wace hanya zai bata ta karba tunda a zuri'ar su ba'a lefe? Shi ne abinda ke damunsa. Ya mayar ya zuge ya koma ya jingina da filo ya lumshe idonsa, abin duniya ya bi ya dame shi, ya rasa ta hanyar da zai bullowa matsalar aurensa. Hausawa kan ce, "Tun ran gini ran zane". Haka "Juma'ar da za tayi kyau tun daga Laraba ake ganeta". Sannan "Kowa ya sayi rariya yasan zata zub da ruwa". Kuma "Tsuntsun da ya ja ruwa shi ruwa kan doka". (So he has to bear the outcome of his wrong doings...) Ya nisa "Ba abinda lokaci ba ya magani". Wani sashi na zuciyarsa ya yi (whisphering) wato rada. Dai-dai lokacin da wayarsa dake kan bed-side take ta tsuwwa. A fusace ya dauka domin bai son wani abu ya katse tunanin nan da yake yi, tunanin kaxai sassauci yake saukar mishi tunda ba zai iya gayawa kowa halin da yake ciki ko abinda ke damunshi ba, sai dai su tattauna shi da zuciyarsa su baiwa juna shawara, su kuma lallashi juna tunda babu mafita sai jajircewa, ya rike igiyoyin aurensa gam-gam har zuwa lokacin da Allah zai tausasa zuciyarta wadda babu wanda ya san yaushe ne? Sai Zuljalali wal ikrami. "Na'am!". Abinda ya ce kenan ba tare da ya duba fuskar wayar ya ga wane ne mai kiran ba. "Ka ajiye duk abinda kake yi haka ka taho gobe. Yanzu na samu sakon ana kiranmu (interview) jibi da British Airlines. Ka sani wannan dama ce ba ta wasa ba, don Allah Abubakar ajiye komai ka taho don Allah. Night flight na gobe zamu bi zuwa Great Britain". Abokinsa ne Ba'indiye Maajid Abduljalal ke magana kamar zai fashe da kuka. "Amma Maajid za ka cuce ni, ka san abubuwan da suke gabana kuwa?" "Zan cuce ka ko zan taimake ka? (This is a life-time opportunity) Abubakar, ina shawartarka (don't miss it...) koma mene ne ke a gaban naka ajiye shi, ba Fa'izah bace? Don Allah kada ka ba da maza (achievements are greater than women). Ka yarda dani, ka karfafa zuciyarka muyi wannan fafutukar tukunna, sai ka dawo ka ci gaba. Na yi maka alkawarin (I'll stand by you) inga cewa kun dai daita da matarka idan mun dawo (and I promised to help you to the end of the battle my friend, be a man) Fa'iz, ina jiranka. Akwai (morning flight tomorrow) daga Abuja, nima shi zan bi daga Berlin zamu hadu a Airport din Wales, ina jiranka". Ya kashe wayar ba tare da ya bashi damar ya yi korafi ko musu ba. Ya ajiye wayar cikin matuwar jiki, sai kuma ya daga ya kira British Airlines ya yi 'booking' duk da jikinsa a mace yake. Wani sashe
Chapter 52 · 0% Book details