Sashe 73
Zumuntar Kenan Part 1 Complete Hausa Novel · about 7 min read
da ya sayo. A raina na ce, "Lallai direban tasha ya canza, da can mutum ne wanda baya wasa da sallah, amma yau sai da ya zauna ya take ciki yayi wanka sannan zai yi sallolin dake kansa. Ya jima yana sallar da ban san la'asar ce ko magariba ko isha ba, kamin ya yi sallama ya kunna sautin Abdurrahman Sudaith cikin wayarsa yana saurare cikin Suratul An'ami. Ya kuma shiga gyaran akaifarshi da ‘nail cutter’ yana bin karatun da wani irin sauti mai dadi da na kasa tantance Fa'iz ko Sudaith wane ne hafizin gaskiya? Dole na rage sautin talbijin tunda dai ni ba shaidan bace. A hakan wani irin barci yan soma fisgata, barci mai dadin gaske wanda na tabbata gajiya da samun nutsuwa ne suka saukar dashi. Ni dai sai juyi nayi na jini bisa tsakiyar ni'imtaccen gado, lalluve da lallausar bargo. Ban farka ba sai washegari misalin karfe goma na safe. Nayi mika, nayi salati, nayi tasbihi ga Ubangijina na nufi (toilet) na cika baho nayi wanka. Na tarar kayana da na tube na wanke jiya sun bushe don haka maimakon daya daga cikin dogayen rigunan su na mayar. Atampha ce (exclusive Sheraton) riga, zane da kallabin su. A (toilet) din na shafa (lotion) din E45 cream da ya sayo nayi daurin kallabina tsaf, sannan na fita ina cin magani ina harbin iska. Zaune yake cikin kujerar zaman mutum daya, ya daura kafa daya kan daya, yayi kyau har ya gaji cikin (light blue) din jeans, na tabbata suma siyo su yayi jiya tare da nawa kayan. Don dogayen rigunan daya sayo min ma kalar makuba maroon, milk da black daga gani sayen (boutique) ne. Rike da 'yar karamar radio yana sauraren harshen Hausa na Rediyo Najeriya Kaduna. Na samu wuri can nesa dashi na zauna na zuba tagumi. Da alama Fa'iz bai da niyyar tafiya ma kwata-kwata, na dai ja bakina na kara tsukewa cikina ya soma kiran ciroman garinmu Giwa. Ya rage sautin rediyon cikin sassaucin kallo. "Madam, babu gaisuwa?" Kokari yake mu hada idanu amma na ki. Ya yi murmushi . "Kiyi hakuri, na canza miki wurin kwanciya ne jiya saboda kada wuyanki ya kage". Ya sake yin shiru. Ya tabbata ba zai samu amsa ba. Hakan bai hana shi karawa ba. "Me kike son kiyi (break-fast) da shi?" Ya dan canza fuska, wato ya dan sha mur. "Fa'izah ba zaki magana ba?" Na sunkuyar da kaina hawaye suka soma mirginowa a hankali ta kasan idanuna. Ya aje rediyon ya taso ya iso har inda nake, ya kama hannuna na dama ya rike cikin nasa, nayi kokarin janye hannuna amma ya rike tamau, gam-gam. "Me zaki ci eye Fa'izah na?" Da wani irin karyayyen sauti, mai kassara gabban jiki da sanyaya zuciya. Da hanzari na mike na nufi (toilet), duk da nasan bani da abinda zanyi a ciki. Gaba daya jikina rawa yake yi, haduwar fatar jikimmu wani 'chemistry' ne da bazan iya fassarawa ba, mai dauke da wani irin (shock) tamkar (electrical shock). Na maida kofar bayin na rufe, na jingina da ita, na lumshe ido a hankali cikin kokarin (regaining consciousness) wanda ya yi min wahalar dawowa. Sai da na samu nutsuwa sannan na fito. Wannan karon bashi a falon. Na dauki takarda da biro nayi rubutu layi biyu kacal, ina kokarin ajeta a inda ya tashi ya bude kofar ya shigo da sallama ciki-ciki. Nima ciki-cikin na amsa, ko kadan bai ji ta ba, don dai amsawar ta zama farillah ne. Ina kokarin dagowa ya dafa ni, "Me ki ke rubutawa?" Kamshin '212' dinshi da kamshin bakinsa na (mouthfreshner) mai karfi da yayi amfani dashi ya cika hanci na. Ban son irin wannan kusantar da yake son assasawa a tsakaninmu ko kadan kuma ba zan lamunta ba. Nayi saurin aje takardar na ja da baya da zafin nama. Ya yi murmushi ya dauki takardar ya bude ya soma karantawa a fili. "Don Allah don Annabi Yaya Fa'iz ka kaini Kaduna wajen Mama. In kuma ba yanzu zaka tafi ba, to don Allah bani kudin mota in tafi, ina da abinda zanyi da yawa". Ya aje takardar ya dube ni da shanyayyun idanunsa. "Kina da wani abin yi ne dama wanda yafi mijin ki muhimmanci? Na duaka miji shi ne (foremost) a rayuwar kowacce diya mace indai tagari ce. Nima ina da abin yin na tattara na watsar saboda matata Fa'izah, ko bance ita tafi komai muhimmanci cikin rayuwata ba tana da hakki cikin lokuta na, wani neman duniya ko sabgogin duniya wadanda ba sa karewa basu isa su sa nayi watsi da wannan hakkin ba. Ko da yake nasan ke baki dauke ni a matsayin mijin ba, balle ki bani wannan muhimmancin. Zamu tafi, amma sai kinyi min magana cikin dadin rai, irin wadda macen da ke son mijinta take masa. Son samu kice I LOVE YOU YAYA FA'EEZ!!! Har sau uku. In ba haka ba, mu karashe sati biyun hutuna anan, daga nan mu wuce Birtaniya, ke da gida sai kinzo haihuwa. Kin san dai ba mai nemanki don an san muna tare. Don haka zabi na gareki". Ya juya ya soma fiddo abinciccikan daya sayo a ledar su, yana dorawa a (centre-table). Ya ci abinshi cikin kwanciyar hankali ya dora da Gahwah mai zafi (Coffee). Ya shige uwar dakin ya bi lafiyar gado da yake dakin ciki da falo ne. Amma ya sauke kafafunshi a kasa. Ni fa na kammala, ke nake jira. Na zauna na ci son raina na koshi, har da kara tea bayan na shanye kofi guda. Naji ni dai-dai, nayi hamdala ga Allah. Na kwance daurin da nayi na dankwalin atamfata na yafa da yake dankwalin babba ne sai ya rufeni ruf. Na nufi kofa na tsaya. Ya mike ya fito falon ya jingina da kofar da ta raba uwar dakin da falon, ya ce. "Au, baki ji abinda na ce ba ko? Tunda kunya kike ji dauki biro da takarda ki rubuta min kinji sabuwar kurma?" [19/02 4:34 PM] Sumayya Takori: Ban musa ba, sai dai a raina na ce, "Inji kunyar ka? Amma da nayi asara. Kunyar maras kunya ai asara ce!". Na dawo na dau takarda da biro na jingina da bango na soma rubutu. Da na kammala na aje nan, na sake komawa bakin kofa na lafe. Ya dauki takardar ba tare da ya bude ba ya sanya a aljihu ya taho yana fadin. "Kin manta da guzurinki". (Yana nufin sanitary pard). Ban bashi amsa ba ya shiga (toilet) din ya kullo duka kayan a ledar da ya shigo dasu ya fito ina ta manna masa harara kamar kwayan idanuna sa fado. Ya yi murmushin sa (broad smile) ya ce cikin rada. "Wannan hararar, wata rana kallon so zai koma, wannan hararan, wata rana in wata tayi min Fa'izah dukan tsiya zata yi mata, sai inda karfinta ya kare akan duk wanda yayi min ita. Wannan hararan, ni a ganina 'I love you ne, I can't do without you ne'. Ba abinda lokaci baya magani". Ni dai bance komai ba, kulawa ma yabawa ce koko Hausawa sunce sai an kula kashi yake doyi. "Saura ki sake batawa Baba mota, wannan karon Shu'aib zansa ya wanke. In yaso in ya tambayi na mene ne? Sai in turo miki shi kiyi masa bayani". Kokari yake mu hada ido, na ki. Na koma na sanyo (slippers) din bandakin don bai sayo da takalmi ba. Muka sauka kasa ya basu mukullin su muka wuce, 'parking lot'. Nayi-nayi in bude kofar gidan baya, na kasa ban sani ba ko kulleta yayi, dole na hakura na shiga gaba, shima ya shiga mazauninsa ganin naki rufe kofar daga inda yake ya sunkuyo har muna gugar juna ya rufo kofar ruf. Maimakon ya ja motar, sai ya bude takarda ta ya soma karantawa a fili. "I hate you. And I would never love you forever... In mafarki kake, ka farka...!!!" Ya zuba min shanyayyun idanunshi masu cike da wata irin fitina, maimakon kalamaina suyi tasiri mara dadi a kansa. Sai naga kamar dadi sukai masa. Na juyar da kai domin ba zan iya jure kalon abubuwan da ke cikin idanunshi ba masu kama da (magnet) mai jan zuciya tamkar jan wutar lantarki, wadanda a fakaice wasu irin sakonni ne suke bayyanawamasu nuna matukar bukatar miji zuwa ga matarsa ta sunnah. Sai naji wasu bangarori na jikina suna kokarin karbar wannan sako, idan har banyi da gaske na zama jajirtacciyata ba kamar yadda nake wannan mutumin zaiyi saurin cin galabata dole in kara jajircewa. Wanda ba komi bane illa kokarin ganin ban yarda mun sake kadaicewa ba. Domin nima din 'adolscent' ce mai bukatar mahadin rayuwa, don dai auren ya zo ba a yadda na so ya kasance bane. Ya kasance ya zo min tareda wani mutum da ba abinda zai yi ya burgeni a rayuwata, ko ya wanke dattinsa dake raina. Ya yi murmushin da yafi kama da takaici ya tada motar. Bai sake magana ba har muka fita garin Minna. Yayin da ni kuma na tsayar da idanuna gefen da bishiyoyi suke zuciyata cike da farin cikin ko yaya ne dai kalamaina sunyi tasiri.