Sashe 58
Zumuntar Kenan Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
fargabar me zata je ta tarar gidan mutumin nan dama ta zauna da wanda bata so din ita azo a tadda ita tunda ku zama da mace fiye da daya al'adarku ne. Kiyayyar diya mace tana da wasu magunguna guda uku wadanda in kana dasu, wallahi sunan kowacce diya mace "sorry" ko ko ince (finished product). Na farko mace na son yawan kyauta na abinda tafi so daga hannun mijinta, kyauta wadda zata ratsa mata zuciya ba gayan kudi ba. Sannan mace Allah ya yi ta da son a nuna an damu da ita, duk inda kake, ka nuna mata tana ranka kana tuna ta da so da kauna. Tana kuma son a darajja ta (kada ka nuna mata danginka sun fita, suna kuma kada ka nuna musu ta fisu) ka barwa kanka wani sirrin na zuciyar ka. Tana so ka kwantar da kai ka bata hakuri in ka bata mata rai. Da fari zata nuna shariya ne, amma zuciyarta sanyi take, tana hucewa a hankali. Idan ka matso 'yar kwalla zaka ji ta ce, "Shi kenan, ya wuce". In ka kawo kyautar nan in ranta yana bace zata ce, "Ni bai dameni ba" ko "bana so ka bar abinka" amma a cikin zuciyarta sonka karuwa yake yana fidda rassa. Haka kayi kokarin ka fahimci duk wani (likes and dislikes) dinta shima ka dage da gujewa/aikatawa. Ka rike amanarta, kada ka dinga zancenta da kowa ko da 'yan uwanka. Duk inda kake, ya zamanto kana yawan nemanta tare da nuna mata ita kadai ce a gabanka saurin mata basa burgeka ko da ba hakan bane (in reality) a zuciyarka. In kayi riko da wadannan Fa'iz kiyayyar Fa'iza komin girmanta babu inda zata je. Fa'eez ya dube shi cikin mamaki. "Who taught you all these?" Maajid ya yi murmushi. "Matar Yayana (psycologist) ce muna dasawa da ita sosai. Tana yawan bani 'theory' akan mata da abinda suke so. Ko baya ga haka ni ba irinka bane da inji kadai kasa gaba. (All work without play make jack dull boy) ina karance-karancen Novels domin samun nishadi (mostly authorized by women). Kuma ina soyayya da mata kala-kala a kasar mu. Ina zaunawa da kanne na mata ina jin hirarrakinsu da damuwoyin da suke ciki da mazajen su, ina sakar musu fuska ni ba (terror brother) bane irinka". Fa'iz ya kyabe baki ya ce, "In ka gama surutunka don Allah tashi muje mu samu (hotel) in kwanta in huta. Zazzabi ke neman rufeni sabida jinin dana zubar. An gaya ma Fa'izah na kamar sauran matan da ka fahimta ne? An gaya ma Fa'izah zata tsaya ta saurari mutum har yayi mata wani dogon sharhi in ta tsane shi? Koko an gaya maka Fa'izah abin hannun maza ya dameta da zan bata abu, ta amsa bata kwada mini ba? (Above all) ma ta yaya kake tunanin ni Abubakar Mukhtar zan yiwa mace kuka har in tsaya lallashinta ta samu kafar wulakanta ne?" Maajid ya kunna sigari ya dasa ma lebbansa, ya ce cikin murmushi. "Meye kuma ya rage baka yi ba? Yanzun nan fa ka gama ce min ka durkusa da gwiwoyinka a gaban Fa'izah ba matse maka baki nayi ba". "Tsugunno daban, kuka daban. Ko da na tsugunnawa Fa'izah bance mata komi ba balle inyi mata kwallah. Da in yiwa Fa'izah kwallah don ta so ni wallahi gara mun dauwama a haka. In na sami sararin aiki inje gidansu ko ta taga ne in leka in ganta in dawo bakin aiki na kada Allah Yasa ta biyonin, an gaya maka a matse nake da mace kamar ka?" Maajid ya fashe da dariya, ya ce. "Ba'a rabu da Bukar ba an haifi Habu. Amma da ka tabbata sakarai, haka kawai Allah Ya halatta maka abu ka haramtawa kanka? Fa'izah dai mace ce dake shekarun shekarunta na (teenager) ba abinda tafi bukata a yanzu irin kasancewa da namiji da zama gidan mijinta, musamman da kace duk tsararrakinta an kaisu dakin aure. Ka zauna nan kayi ta rikon aure, ta yi saurayi mai debe mata kewa koda da hira ne asarar wa?" Ya kai mishi wani mugun kutufo a kwibi, ya ja jakarsa keey...! Ya taka da gudu ya shige (lifter) ya barshi a baya. Fa'iz yayi tsaye kafafunshi harde da juna yana bin (lifter) da ta dauki Maajid zuwa sama da kallo har ya daina hango farar fatar Maajid da fararen kayansa da kwantaccen bakin gashin kansa na Larabawan Syria, yana mai auna maganganun da suka fito daga bakin Maajid din cikin ma'auni na hankali da tunani. Ya tabbata duk abinda Maajid ya fadi gaskiya ne, to amma ta yaya zai bullowa Fa'izah su kasance tare? Bama a gida Nigeria ba a duk inda ya sanya kafa? Barma (bomb) din da ya taho ya barota dashi ya fashe me zai je ya tarar bayan fashewar (bomb) din? Dole ya bi shawarar Maajid na tilasta kansa kin ganin Fa'izah da dosarta har bayan watanni uku kamar yadda Maajid ya ce. "Kai to kuma har wata uku! Wata uku fa ba kwana uku ba!! Fa'izah zata iya yin saurayi a tsayin lokacin. Yadda take kin shi din nan zata iya yin saurayin da zai debe mata kewar mataccen nata. Ya rike kanshi da hannunshi biyu yana girgizawa da sauri... "No! Babu mai barinta, iyayensu ba zasu bari wani abu ya taba mishi aure ba tunda tana tsakiyarsu. To itama bata da hankali ne? Ai aure yafi gaban wasa". A wannan karon hawayen kawai yake ganin idan ya yi (shading) zai samu sassaucin kishin da ya tokare shi ya hana shi hadiyar miyau. In kuma ya sake ya bari suka zubo ya tabbata Fa'izah ta maida shi kamar sauran maza da Maajid yake misali masu yiwa mace kuka don ta so su. Kada Allah Ya nuna masa wannan ranar. *** [18/02 2:48 PM] Sumayya Takori: A ZARIYA Na fito falo fes dani cikin doguwar rigar Momi, baki na kamar gonar auduga, ban zauna a ko daya daga cikin kujerun da suka yiwa falon kawanya ba sai a tsakinin Momi da Ya Rabi, suka dan matsa gefe suka bani fili a darare duk da ita Momi babu alamun jin tsorona a fuskarta, ta bani filin ne kada in dire akan cinyarta. Duk sai suka bani dariya, ga Aunty Rabi mai yi min kallon hauka sabon kamu. Na tsugunna gaban Momi da gwiwoyina biyu, na ce. "Don Allah Momi kiyi hakurdi ki yafe ni, duk bacin ran da na sanya ki da kashin kajin da na shafa miki na zama cikin gidanki ba tare da saninki ba. Wallahi ni kaina wani abin idan ina yi ban san sanda nake yinsa ba, ji nake kamar ana kitsa min shi a tsakar ka, bana cikin hayyaci na. Ya Rabi kema don Allah kiyi hakuri, kuma wallahi Momi bata san ina gidan nan ba". Nan suka dubeni baki bude kamar sunga wadda ta warke daga cuta. Yaya Rabi ta muskuta ta ce. "Yanzun kin kyauta kenan da abinda ki ka yiwa Yayanki da yazo miki sallama zai yi tafiya? Fa'izah kisan kai za kiyi? Kisan ma na mijinki dan uwanki, rabin jikinki? Fa'izah kina son gamawa da duniya lafiya da kike ta da hankulan rayukan iyaye da masu kaunarki akan sanin kanki?" Na kara kwantar da kai da kaskantar da murya sai ka rantse duk duniya ba za'a samu mai kirki na ba. "Kiyi hakuri Ya Rabi, komi ya wuce bi'izinillah. Tsakanina da Ya Fa'iz yanzu sai gaisuwar mutunci da mutuntawa, na bashi hakurin ciwon da na ji masa tunda YA SAKENI!". Rabi ta shiga salati tana sallallami tare da tafa hannuwa, kafin ta kai karshen salatinta take direwa ta dauko sabo. Kafin ta fashe da kuka ta ce. "Kin cuci kanki kin cuce mu Fa'izah, hakkin iyayenki da na Hajjah ba zai taba barinki zama lafiya ba. Kin bata wayonki, kin fita zakka cikin A.B, kin zame mana bakin bunu bata baibaya. Bace min da gani tun ban lallasaki ko na tattaka ki ba...". Ko a jikina wai an tsikari kakkausa. Sai na sa hannu biyu na mika mata takardar, Rabi ta mike tsaye kamar an fisgota ta fisgi takardar daga hannuna, na tabbata in na tsaya tabbas zata tattakanin, sai na mike tsam koma daki na murza key. Na shige cikin bargon Abdallah tunani dubu dari da hamsin ya aureni 70% na Dr. Nazir ne. Mutuwar shi ta dawo min danya, inama ana mutuwa a dawo! Ga damar da nake nema kwana da kwanaki ta samu, amma wanda nayi ta hakilon akansa mai sawa da hanawa ya yi ikonsa akansa. Na rufe ido ina kuka, tunanin kyakkyawar soyayyar mu cikin Jami'ar Bayero da wajenta ke gifta min filla-filla. Na yiwa Allah godiya da na zamo silar kimtsuwar Nazir Sani, ya kuma mutu akan niyyar AURE. Babu abinda zanyi domin nuna soyayyata a gareshi bayan nema masa rahma da gafarar Ubangiji a halin yanzu. Momi dai ban san halin da take ciki ba don bata yi magana ba, sunkuyar da kai tayi, sai Ya Rabi ke ta fadace-fadacenta wanda ko a kwala ta. Kukan rashin Nazir nake baka da zuci, na jiyo muryar Ya Rabi na cewa. "Shima Fa'iz ya yi karamin tunani, ba'a biyewa mace, da maza na biyewa mata da cikinmu babu wadda ba bazawara ba. Idan hankali ya bata shi ake sawa ya nemo shi, haka nan komai aka yi shi cikin fushi, sai anyi nadamar aikata shi". Ashe Momi na hawaye take yi, can na jiyo tata muryar tana fadin. "Yo ai shi kenan, sai ta yi ta zama idan zaman gidan iyaye dadi ne ga baligar mace. Duka sa'o'inta babu wanda ya ba da kunya sai Fa'izah Bakin Buni Bata Baibaya a cikin A.B. Fa'izah bata dauko zuciyata ba sam, zuciyata mai tsafta ce da ban taba kwana da wani a cikinta ba balle in tashi da shi tsayin shekaru a cikinta. Duk wanda yayi min ba dai-dai ba ko nice da gaskiya uzuri nake yi masa da ajizanci irin na dan Adam. Dukkanmu masu kuskure ne da gazawa a wani bangaren, balle Fa'iz akan Fa'izah ne kawai za'a ce bashi da kirki. Na kuma yi mishi uziri tun a wancan lokacin da rashin haxuwar jini ne kawai, ko cikin 'ya'yanka ba ma 'yan uwanka ba sai kaji