← Book details Zumuntar Kenan Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 16 OF 98

Sashe 16

Zumuntar Kenan Part 1 Complete Hausa Novel · about 5 min read

****
To haka rayuwarmu ta ci gaba da mikawa, tafiya ta yi tafiya. Shigarmu ajin karshe a sakandire na dauke da wasu muhimman al’amura da ba zan taba mantawa dasu ba cikin tarihin rayuwata. Don haka ya zama dole in farka shekarar baki dayanta.
Alal hakika a lokacin na fara wadatuwa da abin da ake kira “Hankali” wanda yawan shekaru ke samar da shi. A lokacin ne kuma na fahimci mu’amalata da Yayana Aliyu ba komi ba ce illa SOYAYYAH! Soyayya ce muraran yake nuna min cikin ‘yan’uwana baki daya ba tare da shi kansa ya sani ba, a gaban kowa baya iya boye kulawarsa gare ni. Duk dangi babu wanda bai kwana da sanin matsanancin son da Yaya Aliyu yake min ba ko ba a furta ba.
Sai dai da bakinsa bai taba ko da kuskuren gaya min da fatar bakinsa ba, sai dai actions and emotions dinsa su nuna. Ko da cikin hira ya yi subul da baka sai ya yi kokarin gyarawa ya mai da zancen ko subutar bakin sa (otherwise).
Shekaru na goma sha takwas kenan, duk wani budurci ya tabbata gare ni. Hankali da nutsuwa sun wadace ni. A zahiri, tunda na soma hankalin nima nake so da kaunar Yaya Aliyu, so ba na wasa ba. Cikin kannena da tsararrakina da danginmu duka zancena daya ne (Yaya Aliyu). Shin don mene ne ba zan so Aliyu ba.
Mutumin da ya kwashe shekaru goma sha daya yana kula dani, kulawar da iyayen da suka tsuguna suka haifeni basu yi min ita ba. Yana bauta mini, yana dadada mini, yana faranta mini. In har ban so Aliyu Na’ibi ba, wallahi ni butulu ce cikin butullun ababen halitta wanda zuciya ba ta aiki a jikinsu.
Tun daga aji biyar na sakandire na dauki wasa na aje gefe, na bude file na sanya shi na adana a cikin akwatun karfe. Na yi “facing” karatuna yadda duk wani dalibi na kwarai ke yi da taimako da shawarwari da kulawa tattare da kwarin gwiwa irin na Yaya Aliyu.
Allah ya hore min baiwar kirkira (fiction) na labarai masu ma’ana da fadakarwa ko kuma articles, ina ba da wa ana sanyawa a magazine din makaranta, fili guda aka ware min a mujallar makaranta mai suna ‘KNOWLEDGE IS LIGHT’ tare da Fa’izah Ahmad Abubakar (English Club). Nice kan gaba a fita muhawara (Quizz and Debate) din duk da za ayi da harsunan nan uku, Hausa, Turanci da Larabci.
Da farko in na yi rubutun ‘yan ajinmu nake bai wa su karanta in ajiye, daga bawa shugaban clud dinmu ya karba ya duba sai ya mika shi ga hukumar makaranta. A lokacin an canza Yaya Hauwa daga principal an kawo Haj. Amina Atiku. Ita ta fara dubawa ta ce “Akwai ‘sense’ da ‘exceptional talent’ a ciki”. Rubutuna ya burge principal dinmu sosai, ya kuma bawa malamanmu da yawa mamaki da sha’awa.
Wani novel ne na rubuta labarin wata Bafillatanar yarinya da wani dan makarantarsu da yake taimaka mata a fannin karatu, kasancewarta dakikiya har ta zamo zakakura sahun gaba a masu kokarin makarantar.
Jin dadin hakan ne ya sa ta yi masa alkawarin za ta aure shi da zarar sun gama karatun sun samu aikin yi. Tsawon shekaru takwas tana dakon alkawarin. Bayan nan suka rabu kowanne ya koma wata duniya daban. Ga shi ta yi alkawarin ne a shekarun odolscence (goma sha uku ba ta gama mallakar hankalin kanta ba, ba ta san mene ne alkawari ba da muhimmancinsa balle SO, kauna da auren kansa).
Rayuwa ta mika, bayan rabuwarsu ta ci gaba da jiransa. Katsam Barister Haseen Danbatta ya fado cikin rayuwarta, wanda ya fassara mata hakikanin mene ne so, ya karantar da ita fannoninsa from every angle, dadinsa, dacinsa, zakinsa da rashin dadinsa, bambancin so, kauna, kusanci, shakuwa da halacci.
A zahiri wannan shine mutumin da zuciya da ruhinta ke so, suka kuma aminta da shi. Gangar jikinta da tsokar zuciyarta baki daya ke buri tun kafin bayyanarsa. Ga shi iyayenta sun takura mata da ta fidda mijin aure haka nan, shekaru takwas tana jiran wanda ta yiwa alkawari ya kuma yi mata halaccin da ba ta taba jin an yiwa diya mace ba.
Abin da mai karanta labarin zai tambayi kansa shine, shin za ta ci gaba da jiran wanda ta yiwa alkawarin ko kuwa za ta watsar da halarcin da alkawarin ta auri wanda zuciyarta da rayuwarta ke so? Labari ne tsakanin soyayya da alkawari da na sanyawa suna ARE VOWS MEANT TO BE BROKEN?
Ga shi na yi shine cikin sassaukan Turanci dai-dai karantawar dan sakandire, kuma dai-dai iyawata. Gyare-gyaren da malamar English Language dinmu ta yi min a ciki ba mai yawa bane, grammertical correction ne ta yi. Sai ka rantse da Allah Abubakar Gimba ne ya rubuta.
Principal dinmu ta kirani ta ce za a kaddamar da littafin ranar da zamu gama makarantar, kuma za a buga shi a dinga saidawa a makarantun da ake yin Literature da kasuwanni don sauran al’umma masu karatun Novels don nishadi. In yaso sai makaranta ta rike ribar, amma duk abin da aka samu wajen kaddamarwar nawa ne.
Da wannan daddadan labarin na tarbi Yaya Aliyu a wani visiting da ya zo mana. Na zaci zai yi farin ciki, amma sabani ga tunanina ya yi shiru bai ce komai ba. Na ce, “Baka ji dadi bane Yaya Aliyu? Na dauka abin kirki na yi? Na yi zaton wannan abin farin cikin mu ne duka?”
Ya ce, “Ba wai ban ji dadi bane da hikimarki ba Fa’izah, amma ina son ki san wani abu guda daya, taura biyu ba ta tauno, tunda karatu kika zo yi ba rubutu ba ki mai da hankali ki yi karatun nan. In kin kammala kin san dai hajjah ba barinku zuwa jami’a za ta yi ba AURE za ta yi muku. Sai ki yi ta rubutun da za ki yi a gidan aurenki, ni kuma na dauki nauyin wallafawa”.
Na ce, “Yaya Aliyu na san wannan, amma komai da lokacin da na ware mishi cikin al’amuran rayuwata. Wallahi bana rubutun da malami cikin ajinmu, ko ana karatu sai a karshen sati (week end) da (prefs), a sa’ilin da bani da ‘test’ ko ‘exams’ a kusa. Wato lokacin da ya kasance farko-farkon ‘term’. Inda bana karatu da ban kawo maka positions masu kyau ba ai”.
Ya ce, “Shi kenan Fa’izah, ai ko lauya nan ya ganki ya barki wurin dadin baki da kawo hujja da persuation. Allah ya taimaka. All the best my sister. Cross word!”
Chapter 16 · 0% Book details