← Book details Zumuntar Kenan Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 97 OF 98

Sashe 97

Zumuntar Kenan Part 1 Complete Hausa Novel · about 9 min read

MURFI
Hajjah na kwance tsakiyar falonta, 'yan kananan jikokinta zagaye da ita lokacin da muka shiga tana ta faman bari-barinta data saba daga kwance. Hannuna cikin na Fa'iz muka yi mata sallama a falon.
Allah Sarki Hajjah! Mikewa tayi zaune daga kishingiden da take akan tuntu tana kyafta 'yan makyabtanta amma bata iya ta gane ko su waye ba.
Hakika tsufa ya zo, amma mai tafe tare da nutsuwa wadda riko da addini ke haifarwa a shekarun tsufa, hakoranta duka rabi sun zube, gilashin take lalube don ya kara ma ganinta karfi ta gane mu. Kasancewar bayan sallama da mukayi kasa-kasa, daga ni har Fa'izun babu wanda ya sake magana balle ta shaida muryarmu.
A tare muka isa ni da Fa'iz zuwa ga akwatin gilashin nata wanda yayi gefe guda, hannuna ne ya riga na Fa'iz sauka akan akwatun gilashin. Don haka ni na dauka na sanya mata.
Kallon-kallo ake tsakanin Hajjah Hadiza Giwa, da jikokinta Fa'izah da Fa'izu. A nasu fatar bakin, murmushi ne. A nata kuma cewa tayi cikin raunin murya.
"Abin tamkar a mafarki, ranar dana dade ina jira. Ranar da Fa'izu zai zo min tare da Fa'izah a matsayin matarsa, suna masu farin ciki da juna... suna annuri a fuska da zuci...".
Na zame hannuna daga na Fa'iz na runtuma na rungume Hajjaty....
"Yau ga ranar Hajjah... Ki yafe min Hajjah kuskure ne, ajizanci ne irin na dan Adam!"
Ta rungume ni sosai a jikinta tana dariya ina kuka.
"Daina kuka Fa'izan Hajjah, ni ai nasan wannan ranar na nan zuwa, ni ai nasan dama shirmenki kike da tarin kuruciya ke haifarwa.
Fa'izu nawa! Mijina na kaina, Abubakar Saddiku... akwai gaular data isa tace bata son sa? Ai sai dai ta fada don kawai taji dadin bakinta".
Murmushi Fa'iz yayi, ya zauna a gefen ta yana kada 'yan mukullayen shi.
"Hajjah tawa! Hajjaty!".
Duk sai suka bani dariya, su basu yadda ba mata da mijin ne.
Ina dariya mai cakude da hawaye na ce, "Tsinkayenki dai dai ne. Hasashenki bai zama a banza ba. Ki yafe min Hajjah kuskure ne wanda babu dan Adam din da ya isa ya kauce masa. Na yarda na amince ko iyayenda suka haifeni basu fiki so na ba, sai dai su ce su suka haifeni. Ina kira ga 'yan mmatan zamani su nutsu, su dawo cikin hayyacin su daga tasirin ilmin zamani, wajen akida da al'ada. Su daina kallon zurfin iliminsu da wayewarsu wani mataki na fin karfin iyayensu, sanin ciwon kansu ko abinda yake dai-dai ga rayuwarsu. Muna jarabtuwa da son abu alhalin shi din ba alkhairi bane a garemu, haka mu kan ki abu karshen ki a yayinda shi ne alherinmu. Mafi a'ala shi ne mu baiwa Allah ZABI a dukkan lamuranmu musamman 'AURE' mu daina bin soye-soyen zuciya da baiwa soyayya muhimmanci idan aka zo magana ta aure. Mu yiwa iyayenmu biyayya shine mafita.
Soyayya ta kwarai a hankali ake samunta ba farat daya take samuwa ba. Ba ina nufin babu 'Love at first sight' ba, 'a'ah, 'it is normally not a geniune one'. Kuma bata da karko.
Na gaba har gobe na gaba ne, haka iyaye har gobe iyaye ne koda a kungurmin daji suke zaune karewar rashin wayewar kai.
Ina rokon Allah Ya barni da ku Hajjaty! Ya kara muku lafiya da tsawon rai. Ya bani ikon yi muku biyayyah koda ta wuta kuka hura ganga-ganga kuka ce in shiga anan gaba. Hajjah Allah Ya bar mana ke!!!".
Murmushi tayi, wanda ya fadada zuwa dariya, ya fiddo wawulon da ya kara fadi a bakinta a dalilin faduwar hakora uku a bayan rabuwa ta da ita. Amma bata ce komai ba.
[26/02 8:44 AM] Sumayya Takori: Fa'iz ya ce, "Hajjah me ya sami wayarki ne? In an bugo bata shigowa".
Ta ce, "Kai don Allah rabani da wayar nan, kubi ku ishi mutum da kararraki, ko sallah yake ba zaku barshi yayi ta cikin nutsuwa ba. Ku dai ku kira mutum kiranma maras dalili. Na bude na cire batirin don ku kyaleni na huta ku da ubanninku da uwayenku".
Yayi dariya ya ce, "Haba Hajjah, ai muna jin muryarki cikin koshin lafiya dadi muke ji musamman in muna nesa. Hankalin mu na kwanciya mu cigaba da fafutukar rayuwa cikin kwanciyar hankali Hajjah".
Hajjah ta ce, "Idan ta zama dole ku kira Barau, sai ya kawo min muyi maganar a tashi amma ni ba zan iya ba. Tunda na cire batirin nan na jefa bayan gado kunnuwana suka huta na samu nutsuwar gabatar da ibadu na".
Ya ce, "Talbijin fa? Don me ba'a kunnawa alhalin abar taya hira ce? Kina kallon mutane koyaushe suna gilmawa kina kuma jin muryoyin su yafi zama shiru".
Ta ce, "Rediyo na ta isheni, in murdo tashar Kaduna in koma sashen Hausa na BBC, duk abinda ake fadi ina ji na kuma san 'yan uwana ne Hausawa Musulmi ba wadannan jajayen fatar da ba jin me suke fada nake ba".
Da alama ta bashi dariya amma bai yi dariyar ba, ya ce.
"Shi kenan Hajjah, yadda kike so haka za'ayi".
Ta ce, "Yo dama mana? Ayi ba yadda nake so din ba a gani in zan yarda, ga jikoki ashirin, tattaba kunne goma sha biyar, kullum suna zagaye dani muna hirarmu, kuje ku ku kadai nake jira ku karo in roki Ubangiji na Ya dau raina haka. Duk wani burina da na marigayi na cika shi, da taimakon Allah da taimakon babanninku 'ya'yan albarka, wadanda har yawun bakina ya bushe ba zan daina sanya musu albarka ba. Bana jiran komai sai fatan cikawa da imani".
Ta mike cikin dafa bango da taimakon Ya Fa'iz, ta nufi uwar dakinta tana fadin.
"Yau tunda na tashi da safe jikina yake bani zaki zo gareni Fa'izah, don haka na sanya aka yi miki dambun naman kaza cikin katuwar samira, aka kuma yi miki gashin naman rago irin yadda kike so da ruwa-ruwanshi, yana nan cikin magashi (oven) bude ki dauko, dambun na kai daki na boye don in Na'ibi ya shigo ya gani sai ya kwashe rabi".
Ina dariya cikin jin dadi na ce, "Allah ko Hajjaty? Sakallahu khairan".
Ta dakata a kofar dakin nata tadan yi murmushi.
"Irin wanda nayi miki ranar kamun ki, ranar da kika ja kafa kika gujeni baki kara waiwayata ba".
Tausayin Hajjah ya kamani, na mike na bita na amso dambun cikin samira. Muka zauna a tare a gefen Ya Fa'iz mun sanyashi a tsakiya, na bude na diba na kai bakina ragowar nace.
"To bude wawulon bakinki in zuba miki".
Ta bude bakin tana dariya na sanya mata lomar dambun naman mai dadin da baya misaltuwa.
"Nayi-na yi kimanta kin ki ko Hajjaty? Ni fa ban gudu na barki ba, naje inga Momi ne".
Ta harareni ta ce, "Nono kika je sha ba ganin Momi ba".
"Kenan baki yafe min ba Hajjah? Baki yarda kuskure ne ba? Idan baki yafe min ba Hajjah ina zani? In samo irin sanyin da nake samu a cinyoyin ki? Baki yarda ina son Hafizin ki ba kamar koma fiye da yadda nake son kaina? Yaya Fa'iz don Allah ka fada mata 'how much I love you'".
Dauke kai yayi ya cigaba da danna wayarsa kamar bai san bikin da muke yi ba. Wani tunani yazo min, ya zanyi in goge wannan tabo a zuciyar Hajjah na cewa ina son Hafizin nata yanzun? Wata zuciyar ta ce.
"Show her in another way".
Sannu a hankali na tashi daga mazaunina na koma gaban Ya Fa'iz. Na zube gwiwoyina na sumbaci goshinsa zuwa labbansa, sumba mai tsayi da zurfi. Ya bude ido cikin barazana yana zazzare su.
"Ke Fa'izah, meye haka? A gaban hajjahhh?"
Hajjah ta fashe da kuka, wanda a cewarta, "Na farin ciki ne".
"Na yafe miki Fa'izah, Allah Ya yafe mana baki daya".
Muna takawa a hankali a harabar gidan zuwa bakin mota, Hajjah a tsakiyarmu ta yo mana rakiya muna 'yan hirarraki wadanda duk akan 'yan uwa ne, masu haihuwa, masu aure da masu karatu. Su Indo, Inna Kubra suka biyomu da tsarabar Hajjah (dambun nama) basu barni na rike ba. Don haka da muka fito kofar gida nayi musu ihsanin da zasu jima basu manta ba.
Har mun kai jikin mota zamu bude Hajjah ta ce,
"Au, Hafizi?"
Fa'eez ya juyo ya dakata da bude motar.
"Na'am Hajjah".
Ta karaso garemu. Sai ta kama hannuna ta kamo nasa, ta hada ta dunkule. Da wani irin murmushin kauna a gefen bakinta, ta ce.
"Sai ina kuma kuka yi yanzun?"
Ya ce, "Gida zamu koma Hajjah. Gobe da safe kuma zamu bi jirgi zuwa Lagos wajen su Yaya Aliyu. Da mun dawo za muyi kaura zuwa (Wales) can inda nake aiki don jaurar tayi min sauki, in samu nutsuwar gabatar da ayyuka na Hajjah da Fa'izahta a gefe na, duk karshen shekara zamu zo mu ganku kuma ku ganmu. Ko in aikowa Baban Giwa tikiti ya kai min ke duk lokacin da naji son ganinki. Hakan yayi Hajjah?"
Murmushi tayi, wani irin murmushi da ban taba ganin Hajjah tayi irinsa ba.
"Nayi ta zama a duniyar kenan Hafizi kuna ganina kuna jin dadi? Ai mun iso gangara, me yayi saura Hafizi bayan fatan cikawa da imani?
Ga amanar Fa'izah a hannunka, na roke ka ka kyautata mata muddin rayuwar ka. Baku sani ba, kuma ban taba fada ba koda ga iyayenku, yadda nake sonka haka nake sonta ko a cikin jikokina ku na daban ne. Ina rokon ku ku hada kanku, ku kaunaci juna saboda Allah!".
Fa'iz ya sake damke hannuna cikin nasa, ya lumshe idonsa.
"Na yi miki wannan alkawarin Hajjah".
Har muka shiga motar ya tayar, Hajjah bata koma cikin gida ba. Ta sake matsowa jikin tagar da yake ta russuna dai-dai kunnensa, ta ce.
"Kayi tukin a hankali".
Sannan ta dago ta dubeni nima, "Fa'eezah ga amanar maigidana, Hafizina Abubakar Saddiku, ki bishi, ki yi masa biyayya kinji Fa'izah? Ki dawo min da mai sunansa in kin tashi dawowa ko mai sunana. Ina kulafucin ganin 'ya'yanku wanda nasan DA KYAR NE...".
Jikina yayi wani irin sanyi da al'amarin Hajjaty a yau. Magana take kamar mai yin wasicci kuma kamar mai hango gobe. Ko dan yatsana na kasa motsawa haka shima Hafizin. Na kasa amsawa sai kallon Yaya Fa'iz, shi kuma sai ya sadda kai kasa bai ce komai ba.
Da kyar na iya na ce, "Insha Allah Hajjah".
Ya yi ribas da motar gate din A.B Houses Hajjah na daga mana hannu. Ni kam mai raguwar zuciya sai nasa kuka, kuka nayi ta yi ba dan kadan ba. Kalaman Yaya Fa'iz ya kara tunzura kukan nawa, cewa yayi.
"Yau Hajjah duk ta kashe min jiki da kalamanta, ban san me yasa ba, gata dai lafiyarta kalau... Don Allah ki daina kukan nan Fa'izah, kina kara tayar min da hankali, kina sawa inji tamkar Hajjah mutuwa zata yi kafin mu kai Kaduna".
Na tsagaita da kukan amma ban daina ajiyar zuciya da sauke numfashi ba har muka zo gida.
A daren shima bai yi wani isasshen barci ba. Sau uku yana bugawa Aunty Maryam Maman Yaya Aliyu da Baba Na'ibi waya yana tambayar yadda Hajjah take har suka yi mamaki. Suka ce lafiyarta kalau, yanzu haka girki take yi wai zata yi sahur dashi, sannan ya samu ya rintsa sama-sama.
Chapter 97 · 0% Book details