← Book details Zumuntar Kenan Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 65 OF 98

Sashe 65

Zumuntar Kenan Part 1 Complete Hausa Novel · about 4 min read

Ummi da angonta Yaya Bashir suna cikin (kitchen) suna hadin (burger) da suke so su ci. Da ya fito sashen Mama a bakin kofa suka yi karo da Shu'aib ya tambaye shi kwatancen gidan Yaya Bashir.
Ya ce, "Yaya Fa'iz muje mana in raka ka, nan ne Kabala Custain ba nisa".
Ya ce, "Amma da kanka za ka dawo? Don ni daga can ba gida zan dawo ba".
Shu'aib ya daga mishi kai suka jera suka fito suka shiga motar Baba, Fa'iz ya ja motar a hankali suka fita daga gate din gidan nasu.
Ummi ce ta fara hango shi ta tagar (kitchen) din wadda ke santar harabar adana motar su. Tayi ihu harda dan tsalle ta ce.
"Ya Fa'iz in town".
Suka fito da sauri ita da Bashir suka game dashi a main falonsu. Daga matar har mijin bakin su yaki rufo sai jera masa sannu da zuwa da yaya hanya suke yi yana amsawa da ka, yana dan yatsine fuska. Ya bi daya daga cikin lafiyayyun kujerun falon ya nitse. Takaici ko kishin yadda yaga Ummi da Bashir ne suna rayuwarsu babu abinda ya dame su duk sunyi haske sunyi kiba, koko tunanin tashi 'yar bala'in amaryar ne yasa shi yatsine fuska oho! Da irin tarbar da shi zata masa? Allah kadai Yasan ZUCIYAR MUTUM (sunan wani littafin TAKORI).
Suka zauna kusa da shi suna manne da juna. Ya dube su sai ya saki fuska.
"Mr. and Mrs.".
Suka hada baki wurin cewa, "Allah Ya taimaki angon Fa'izah!".
Ummi har da jinjina da hannunta.
Bashir dariyar shegantaka yake mishi ganin yadda ya zabge amma ba zai fasa halinsa na rainawa mutane wayau ba da ginshirar babu gaira babu dalili ya ce.
"Shin Pilot Giwa yayi ciwo ne?"
Ya ce, "Lafiyata kalau, me ka gani?"
Tare da cin laya kada su kawo mishi shegantakar da ba zai dauka ba, amma sai da Ummi ta ce.
"Kaima dai dear! Fa'izah's calamity mana! 'Yar banza Bakin Bunu Bata Baibaya...".
Ji yayi kamar shi ta zaga, kuma dai shi baya son a dinga shigar masa rigimarsa da Fa'izah ko ace tayi ba dai-dai ba, zai fi son ka zauna a gaban sa kayi ta yabonta kana bashi labarin rayuwarta fiye da nuna kana taya shi takaicin abinda take yi akansa. Ya share zancen da cewa.
"Shin kuna lafiya? Na same ku lafiya?"
Bashir ya ce, "Gani ya kori ji".
A yayin da yake tuttula mishi (fresh milk) din Peak cikin tambulan din dake hannun Ummi, ta mika mishi ya daga mata hannu.
"Barshi, bana tare da yunwa, Mama ta bani abinci na ci".
Ummi cikin rashin jin dadi ta ce, "Amma ta yaya zaka shigo gidanmu ka fita ko ruwa baka kurba ba?"
Kamar zata fashe da kuka, sai ya mika hannu ya karba ya shanye ya dire kofin bisa (center table).
"Na yaba da tsarin gidanku, Allah Ya ba da zaman lafiya. Ni zan wuce". Ya mike.
Dan uwa rabin jiki, Yaya Bashir sai yaji tausayin Fa'iz ya kama shi duk da basu cika shiri ba ya gano damuwar dake tare dashi da halin da ya shiga ganin irin rayuwar da suke yi shi da Ummi suka mike suka fito tare da shi.
Bashir ya ce, "Wai ina Fa'izar ne?"
Ba tare da ya juyo ba, kamar yadda bai fasa tafiya ba ya ce.
"Tana nan".
Ummi da Bashir suka hada ido suka yi murmuishi, shi kuma ya sake hade rai da fuska har da tsuke baki kada su kara tambayarsa game da Fa'izah, kowa yayi (minding business) dinsa. Ita kuma Ummi bata fahimci hakan ba, sai ta ce.
"Don Allah ka kawo min ita mu wuni yaya Fa'iz, na matsu in ganta, nayi-nayi tayi hakuri ta ki saurarona...".
Sai kawai ya samu bakinsa da furta, "Me kika yi mata?" Alhali bai yi niyyar yin furucin ba.
Ummi ta ce, "Matsalar mu ce, amma ka tambaye ta mana, ai kunfi kusa".
Sai yaji kamar shaguben da yake gudu suka yi masa. Ita kuwa Ummi tsakaninta da Allah ta fada, ta kara da cewa.
"Sai yaushe za ku tare mu zo rakiya?"
Ji yayi kamar Ummi ta zage shi, ya ce.
"Ummi, ina wasa dake? To babu rana babu wata!".
Dai-dai sanda suka kawo inda ya yi (parking), Shu'aib na zaune bencin megadi suna hira yana jiransa. Ya bude boot din motar yasa Shu'aib ya fitar musu da tsarabar da ya kawo musu. Electronics ne na amfanin (kitchen) cikin kwalayen su guda biyar samfurin 'Binatone' microwave, juicer, mixer da 'rice boiler' sai 'blander masu karshen (quality).
Shu'aib ya shigar musu da su gida ya dawo suka shiga motar suka tafi, Ummi da Bashir na godiya suna daga musu hannu har suka fice daga harabar gidansu suka hau titi.
Yana tukin ya dan juyo ya dubi Shu'aib ya ce.
"Yo kai in haka ne ai zaka yi min amfani wajen sauke kaya, shige muje Zaria kawai".
Chapter 65 · 0% Book details