Sashe 36
Zumuntar Kenan Part 1 Complete Hausa Novel · about 5 min read
ka fahimci lallai namiji ne wanda zai tattala matarshi matuka, wanda zai lallaba matarshi fiye da Abdullahin Haulatu. Abdullahi ya mike yana fadin “Haulatu zan wuce, zo ki ji mana”. Ummi ma ta mike ta ce, “Ni toilet za ki nuna mani a cikin gida”. Gaba daya suka fice. Daga ni sai malamina Mr. no name. A sannan ne na fahimci sun fita ne duka don su barmu mu biyu. Ya dan motsa a cikin kujerarshi sannan ya ce, “Fa’izah!” Wannan kira ya dade yana amsa kuwwa a sassan jikina. Ban iya na amsa ba sai kara dukar da kai ina murza zoben hannuna. “Har yanzu ban yi abin da zai sa a sake dani ba? Ko sai na kai ga durkuso bisa gwiwoyi na? Domin wannan afuwar Fa’izah?” Na dan fiddo ido, “Ta ya ya malami zai durkusawa dalibinsa?’ “Ta dalilin yana SON dalibar soyayya mai yawa.....” Ya fadi cikin kwaikwayar muryata. Da a ce ban ga yadda yake ciccijewa yana cin magani a aji ba, sai na rantse cewa ba shi bane. Lallai so ba dama ne. Jin na yi shiru ina tauna maganarsa sai ya katseni da cewa, “Shin Fa’izah ta tsai da gwani ne tsakanin Giwa, Zaria, ko Kaduna?” Sai na yi dariya cikin jin kunya, “Don me ka yi tunanin wannan? Mu ‘yan Giwa bama hada taura biyu a baka”. Murmushi ya yi tare da girgiza kai, “Mu ‘yan Kano muna hadawa, kenan rabon kanawa ne ya hana?” Murmushi na yi cikin jin shauki. “Fa’izah I’m serious. I’ve interest on you. Shin za ki iya auren malamin makaranta?” Dagowa na yi na dube shi da dukkan idanu, “Babana ma malamin makaranta ne”. “But you are born with a silver spoon in your mouth (kin fito daga gidan masu hannu da shuni), kaman hakan zai zama takura”. Ya fadi cikin murmushi. “A’a, ban fito daga (silver spoon) ba, na fito daga BABBAN GIDA (point of correction) mai babban suna”. Tafi ya yi min sau uku, “Mene ne bambancin guda biyun?” “Akwai bambanci da yawa. Babban gida kudi bai yi yawa ba, amma babu yunwa babu rashin suttura a cikinsa. Sannan masu shi dattijan kwarai ne masu magana daya. Idan kuma ka ce tajirin gida kana nufin gidan hutu”. Wannan karon dariya yake yi sosai wadda ta sanya ni shagaltuwa a kallon sa, kyawunsa na kara kayatar da zuciyata. “Na yarda dake Fa’izah, to amma fa sai kin ki ji kin ki gani a tafiyarmu. Abin da na gani ina so da zuciya guda ba zan iya munafuntar shi ba, ina da tabo Fa’izah, wanda na san as soon as an fara ganinmu tare za a kawo sukar sa. Duk da an ce waka a bakin mai ita ta fi daxi, ina jin kunyar kaifin idanunki....” Ya yi dan murmushi.... “Ina son mata Fa’izah, ina son su da yawa..... na yi amanna da cewa har gida za a biyo ki a gaya miki wannan, sai in ba a ganmu tare ba. Amma na yi miki alkawari Fa’izah tsakanina da mahaliccina from you it will cease to exist (son matan) na yi miki alkawarin bari har abada in har kin amince ki zamo uwar iyalina. Daga ganina dake na farko zuciyata ta gaya min ke ce (life-companion) dina mafi cancanta. Kaunarki ta fara ne daga ganina dake na farko (love at first sight) na rasa nutsuwar zuciyata a tsayin wunin ranar da daren baki daya. Da nake kwatantawa Haulatu kamanninki da level din karatunki take ce min ke best friend dinta ce tun a secondary, da take yawan bani labari. Shine ta hada mana wannan dabarar ta dinner (to dine here together) ta kuma turani in dauko ku. Gaba daya tarihinki na jishi wurin Haulatu, na kuma kara tabbatarwa kaina INA SON FA’IZAH! Shin Am I accepted Fa’izah?” Kaina na sunkuyar ina murmushi. Abin nan da masu iya magana ke cewa, labarin zuciya a tambayi fuska, don zuciyata ta yi na’am tun ma kafin ya furta. Har nake jin cewa, ba son mata ba ko mata dari gare shi zan iya zama ta casa’in da tara in har nice uwar ‘ya’yanshi. Domin yanada duk abubuwan da za a so shin a kansu. Ga dai ilimi, ga kuruciya, ga kyau na a manna a jarida, ban ga makusarsa ba. “Ko da ban furta ba, kallo daya za a yi min a tabbatar da na fada a matsananciyar kaunar ka. Daga lokacin da idanuwana suka fada a kanka Malam”. Magana nake a zuci, ban san cewa a fili nake yi ba. Ganin ya lumshe idonsa ya bude ya ce, “Na gode”. Ya tabbatar min ya ji abin da na ce. Wannan sai ya tuna min da lokacin da na karbi tayin soyayyar Yaya Aliyu a Zaria, ga shi ban ci ribar waccan ba, na amsa ta biyu, kada Allah ya kara dandana min dacin ta. Cikin dan lokacin nan mun tattauna abubuwa da dama mun kara fahimtar juna. Har zuwa lokacin na kasa tambayar shi sunan shi. Sai wurin karfe goma Haulatu ta fargar damu, da kyar muka katse hirar muka fito zuwa mota. Ina ganin Ummi da Haulatu na gulma suna rada da dariyar shegantaka ko kula su ban yi ba. Don na san da ni suke. A kan hanya ma hirar muke yi. Ya gaya min ya yi dukkan karatunshi ne a Taiwan inda ya karanta harshen Larabci ziryan. Shi da Abdullahi ‘ya’yan family friends ne, haifaffun garin Dambatta. Da kyar muka iya yin sallama don sai da Ummi ta shige ta barmu. Sai shigowar hancin motar Yaya Mufty ne yasa muka yi sallama ya jira fitowar shi da yin parking din shi suka yi hannu, sannan ya shiga motarsa ya tafi. Har zai fita get ya dawo ya yi min horn na juyo “Phone no na manta Fa’izah”. “Ni da Ummi bamu da waya”. “Saboda me?” “An hana mu rikewa ne”. Hannu yasa ya dauko tashi a gefe, “Ki rike wannan saboda ni Fa’izah. Na yi alkawari ba zan zamo mai hana ki karatu ba!” Ya cire layin ya miko min (Sony experia) sabuwa dal. Na rasa abin da ya hanani kin karba, na kuma rasa wanda ya sani yin godiya. Wala’alla soyayyar kenan?