← Book details Zumuntar Kenan Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 76 OF 98

Sashe 76

Zumuntar Kenan Part 1 Complete Hausa Novel · about 7 min read

A dai dai lokacin da ya tsaya gaban wani karamin (flat) mai jan get, yayi (horn) wani buzu yazo da sauri ya bude. Gidan karami ne, amma fa wanda akayi amfani da hikima da fasaha wajen gininsa da tsarinsa tamkar (European-building). Rufinsa ja ne, fentinsa ciki da bai fari da ruwan madara. Ainihin ginin gidan a tsakiyar gidan aka yishi fili fetal ya zagaye shi ya sanya shi a tsakiya. Gini ne na hawa daya (flat).
Korran shuke-shuke sunyi kyakkyawan layi a gefe sun bi katangar gidan har wajenta, haka akwai wayar lantarki ta (security) akan katangar gidan. Grass carpet ne lullube da harabar gidan korra sharr sunyi lub-lub alamun suna samun matukar kulawa. Wannan shi ne ainahin gidan da Pilot Fa'iz Mukhtar ya kwashe shekaru biyu kacal yana ginawa cikin garin Kaduna, ba da sanin kowa ba sai mahaifinsa Baba Muntari wanda shi yake turowa da komai ake masa ginin daga Ukraine, hatta zanen gidan shi ya turo masa ko kwabon Baban Kaduna babu a cikin ginin Fa'iz, cikin tsararriyar unguwar Malali GRA.
Ya bude motar zai fita, sai kuma ya juyo ya dube ni. Bani da alamar fitowa illa kuka da nake yi a hankali wanda yafi kama da kukan amarya mara gata, wadda iyaye da 'yan uwa basu rako gidan miji ba. Me na yiwa A.B haka da zafi? Wane irin rashin so ake min cikin zuri'armu? Me Fa'iz yake musu wanda ni bana musu? Daga can kololuwar zuciyata naji wata murya tayi (whisphering) rada cikin kunnuwana, "BIYAYYAH".
Wannan ya tabbatar min na dai tabbata matar FA'EEZ MUKHTAR ABUBAKAR tunda har yau gani cikin gidanshi matsayin matar gidan.
Na karbi kaddarar Ubangiji wanda Shi Ya nufi Fa'iz da zama miji a gareni. Bani da inda zani, bani da yadda zanyi, mu zauna a hakan, zaman dolen da ya zaba mana. Sai dai bana jin har illah masha-Allahu zan so shi, soyayya guda daya ce kuma na tabbata na yita na gama. Na karbi Fa'iz a matsayin mijin kaddara, na kuma ci alwashin ba zan kuma yi masa musu ko rashin kunya ba tunda ina kwadayin rahamar Ubangiji kamar yadda na yarda da tunasarwarsa gaskiya ce tsagwaro. Sai dai SO daga gareni bana jin har abada Fa'iz zai samu haka har in koma ga Ubangiji na Fa'iz ba zai samu dariya ta ba balle walwalata. Biyayya ita ce wajibina nayi alkawarin yinta da dukkan iyawata.
Na bude murfin mota na fita ba tare da na dauki komai ba, na doshi kofar da na tabbatar ita ce ta shiga falon gidan.
Ya karaso yasa (key) yana budewa. Wani saurayi ya bullo daga bayan gidan ya fadi yana gaishe shi yana amsawa, sannan ya juyo yana min sannu da zuwa. Ban amsa ba sai daga kai nayi.
Fa'iz ya ce da shi, "Yaya suke yau? Ince ko an basu abinci sosai?"
Ya ce, "Ranka ya dade an basu sunci sun koshi sun sha ruwa tun yamma yau suka kwanta".
Ya yi murmushi ya ce, "Sai da safe to Malam Ya'u. Ka zo da wuri don Allah don zan aike ka kayowa Madam cefane".
Ya ce, "An gama Yallabai. Mu kwana lafiya".
Na rasa suwa ake magana akan su.
Bai sake dubana ba ya bude kofar ya wuce ciki ya janye (curtains) ya sarkafe su a masarkafinsu. Na tube takalmana na shiga, duhu dindim, naji kafafuna bisa wani sassanyan (marbles) mai sulbi kamar bayan tarwada.
Yasa hannu ya kunna fitila daga bayan labule haske ya gauraye falon, kamar rana, sai dana runtse ido, sai ya rage fitilun ta hanyar kashe wadda tafi kowacce haske ta tsakiyar falon, hasken ya koma dai-dai.
Ya yi murmushi ya ce, "Ga dakinki Fa'izah, ga dakinki, bayan shi a ko'ina na gidan nan baki da shamaki. Wannan falon saukar baki ne, naki yana hade da dakin barcin ki, nima haka. A falonki (kitchen) yake, ba abinda su Yaya Rabi basu zuba miki ba irin na 'yan uwanki, amma sunce in gaya miki ba zasu rakoki ba, saboda halin ki ba irin na 'yan uwanki bane. Haka ba zasu ziyarce ki ba sai ranar da suka ganki da ciki irin na Ummi. Suna yi miki fatan ALHERI".
Wata harara na zabga masa, shima ya mayar min da wadda ta fita zafi, ya ce.
"Daga fadar sako? Allah Ya huci zuciyar ki; O.K?"
Na samu daya daga cikin tausasan kujerun (leather) da suka yiwa falon kawanya na luntsume. Ina kallon yadda aka shirya dakin abin sha'awa, na tabbatar aikin Aunty Rabi ne da Aunty Hauwa, sai na lalace ina kallo kamar a talbijin. Komai (orange) da (lemon green) kamar ka lashe, sannan babu tarkace amma kaya ne masu daraja baki daya tun daga kan (dining table) na tsurar bakin gilashi a can gefen falon ga na'urar sanyaya daki ta girke, doguwa (split) tana ta buso sanyi mai dadi, kayan lantarkin 'Samsung' kaloli ne kawai suka bambanta da na Ummi, ita nata komi (milk and brown) ne.
Ya dauko wayarsa yayi magana, ashe buzu mai gadi ya kira. Ya zo bakin kofa da sauri yana sallama.
Ya ce, "Kaga na manta Ya'u ya wuce, ungu mukullin mota ka kwaso duk kayan dake bayan motar da wadanda ke cikin (boot) ka kawo mata. Ka shigar dasu dakin can".
Ya karba yana fadin, "An gama Yallabai". Da buzuwar Hausarsa.
Ya dubeni kasa-kasa kamar ba zai yi magana ba, sai kuma ya ce.
"Ki tashi ki shiga nawa dakin har ya gama, ko zama za kiyi sai ya gama kalle ki cikin falon nan?"
Nayi mamakin dalilin fusatar shi haka bayan banyi wani abu da zai fusata shin ba. Na zambura baki, sannan na mike, kada inje ya faska min marin da ya saba faska mini. Don na lura yana matukar son tada hankalin fuskata da tafukansa.
Dakin daya kira nashi nan na shiga ina shan kallo. (INa ruwan 'yar kauyen Giwa).
Ina jin Baba Buzu yana ta shiga da su, sai da ya gama tas ya rufo motar ya kawo masa mukullin. Suka yi sallama shi kuma ya rufo kofar falon da (keys) ya ce.
"Malama fito min daga daki kada ki shafa min najasa a gado".
Kamar wata rakumi da akala sai na fito nayi wanda aka bani, babu musu, ba busa ba daga hannu. Ni kaina har mamakin (silence) dina nake yi. Ko da yake shaidan ne kadai za'a ce masa ga allah Ya kautar da ido.
Ganin bana jin barci, na ce bari kawai in shirya kayana a (wardrove). Ina jinshi ya kunna t.v a (main) falo yana sauraron labaran ALJAZEERAH na soma ninke kayana ina tsara su ina adanawa. Na cikin akwatunan da dinki suke bukata na barsu a ciki na jera akawatunan haka cikin (wardrove).
Ina tsaka da aikin nawa ya shigo, ya tsaya daga bakin kofa, ya canza zuwa pyjamas farare sol, hannunshi daya cikin aljihun 'pjs' din daya rike da kofar.
"Yunwa nake ji, ya za'ayi?"
A raina na ce, "Wannan wace irin tambaya ce? Ban biyo shi don in yi sana'ar kuku ba ko zaman aure irin na mata da miji, sai don amsa kiran Baban da yace min, ashe wayo yayi mani duka na hakura na fauwalawa Allah na mika wuya ga hukincinsa, yanzu kuma yazo yana son dora mini abinda ba dole na ba. Wanda ko kusa ba zan karba ba. Ai ita wannan din (girki) ba fadar Allah bace, al'ada ce, don haka ba zan karbeta ba. Allah cewa yayi su kawo a dafe su ciyar damu, babu ayar da ta ce a sayo mu girka, ni kuma da fadar Allah kawai nake amfani.
Don haka nayi masa shiru, ya gaji da jiran jin ta bakina, ya tabbatar ba zan tanka ba, sai ya ce.
"To a gasa min kaza da (chips) (favourite food) dina kenan. Don naga alamar ke a koshe kike. Akwai kajin a (freezer) din (kitchen), dankalin ma akwai a (kitchen). Duka Ya'u ya sayo, kayan gwari (su tattasai da tumatir) ne kawai babu gobe zai sayo miki, dazu da yaje sun tashi".
Ya juya ya fice. Ban amsa ba, amma a zuciyata na yanke shawarar zanyi, tunda sawa da hanawar duk a cikin umarnin Ubangiji suke.
Sai na saki aikin da nake yi na fito zuwa (kitchen) din. Ashe kallo na sama, babu irin na'urar girkin da iyayenmu basu jera min ba, komi na cikin (kitchen) din (orange) ne (freezer) da (cooker) sune (lemon-green). Na ba da ajiyar kallon zuwa gobe da safe na fara abinda ya shigo dani.
Cikin minti goma sha biyar na gama da yake dankalin ma a (fryer) na soye shi bai dauki lokaci ba. Na jera a (tray) yana zaune na dora a (dinning).
Naga mamaki a fuskarsa da na juyo zan koma daki sai na tuna ban ajiye ruwa da lemu ba, kada inci gaba da aikina ya kara taso ni. Na koma firjin dake dab da (dining) na ciro masa (Pepsi) da ruwan Faro.
Har na kai bakin kofar daki na, ya ce.
"Aunty Fa'izah saura ruwa da lemo".
Na cuno baki na harari tebirin sai shima ya kalle shi. Dariya yayi.
"Aunty Fa'izah ta soma zama (full-house wife): It's a job weldone!".
Da sauri na shige daki bana son zuciyata taji yabon da yayi mata.
Chapter 76 · 0% Book details