Sashe 20
Zumuntar Kenan Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
**** Shin wace irin amsa zan rubutawa Yaya Aliyu ne? Wallahi ban sani ba. Na shafa ko ina ban ji amsar da ta dace cikin kwakwalwata ba saboda kunya. Kuma wadda zan saka ta yi min gayyar ta watse (Khadija-Ummi) anyi ta ba dadi. Ina kuma ganin faduwa ce babba gareni in je ni neman sulhu. Sai dai in mu koma gida a haka amma ba zan ba da kaina ba ta kara kular dani a banza, don da alama babu sauran mutunci cikin al’amarinta in dai a kan wannan dan’uwan nata ne Musa a fuska, Fir’auna a zuci. A kullum sai na karanta wasikar Yaya Aliyu a kalla sau cikin carbi. Aike na duniya Yayan ya yi in ba da amsa na ki, don tsakanina da Allah da gasken ban san me zan rubuta mishi ba. Don haka ne wai na bari ayi hutu tunda ya matso in yaso sai mu rubuta ni da Zanirah. Yau saura sati biyu hutu Yaya Hauwa ta shigo makarantar wajen kawayenta malaman makarantar. Bayan ta gama abin da ya kawo ta, ta yi kirana staff office ta ce, “Fa’izah na gaji! Zaryar Aliyu gidana ta ishe ni, wai amsar me za ki ba shi ne? Ki yiwa Allah ki bani takardar nan in ba shi in huta ya sarara mini”. Na ce, “Yaya Hawwa ki kyale Yaya Aliyu don Allah sai mun zo gida. Saura kwana goma sha hudu ya rage”. Ta ce, “Ai shi kenan, ni tausayin shi nake ji wallahi. Ya damu fiye da zaton ki, wayar safe daban ta dare daban, ga ayyuka masu tsauri a gabanshi. Yarinya karama sai tamaula kike da ‘yan maza, ki ji tsoron gamuwarki da Allah Fa’izah ki tausayawa Da na”. Na kyalkyale da dariya na ce, “Yaya ni ba ‘yarki ba ce sai Yaya Aliyu kadai?” Ta ce, “A’a, ni na fara cewa haka? Duka daya kuke”. A ranar ne kuma hukumar makaranta ta sanar cewa, babu ‘yan set dinmu a masu zuwa hutu saboda karatun bita na jarrabawar karshe. Sai dai wadanda ke cikin Kaduna ne kawai za su fita su dawo sati daya jal. Muka debi kayan sawa uku cikin jaka muka yi gidan Yaya Hauwa. Tsakanina da Ummi sai harara. Kwanana daya gidan yaya Hauwa gidansu Ummi kenan, duk na kasa sakewa sakamakon rashin sabo da gabar da muka tsira a junanmu. Sai dai duk iyaka kokarina na yi Yaya Hauwa ba ta gane ba, don ko da za ta ji din na tabbata ni za a daurawa rashin gaskiya duk da nice mai gaskiyar, da rashin dadin zuciya ya isheni na dau wanka na sha atamfa super da mayafi, na yiwa Yaya Hauwa sallama da niyyar za ni gidan Baban Kaduna Jabi Road. Ta ce, “To dai kada ki sake ki je Giwa, kin san dai dokar makarantar nan, iyakacinku cikin gari. Ga ummi ta shiga wanka ki tsaya ta fito ku tafi tare mana”. Na ce, “Ai kwana zan yi, kin san kuma Ummi ba za ta yarda ta kwana gidan Baban Kaduna ba saboda abokin fadanta (Junior)”. Ta yi dariya ta ce, “Yiwa Idi direba magana ya kai ki yana nan cikin lambu wajen tsintsaye yana basu abinci”. Shigarmu harabar gidan ke da wuya idona ya kyallo mani motar Yaya Aliyu fake a harabar adana motoci. Gabana ya fadi, tabbas na yiwa Yaya Aliyu laifi babba kuwa, na yiwa Aliyu Haidar babban laifin da ban san (punishment) din da zan fuskanta ba, bani kuma da uzuri ko hujjar kare kaina. Na gyara murya zan ce da Malam Idi mu koma na hango fitowarsu shi da Baban Kaduna yana rike da brief case din shi. Dole na fito, duk gwiwoyina sunyi sanyi kalau. A dai-dai motocin Baba dake jere a cikin rumfar adana motoci na tsugunna har kasa na gaida Baba. Kallon da Yaya Aliyu ke min a yau ya kara sanya min mutuwar jiki da sanyin gwiwa har muryata karkarwa take ina gai da Baban. Ya ce, “Faduwa ta zo daidai da zama, yanzu Mamanku ke cikiyarku game da shirin da za ku soma na bikin da za ku sha nan da watanni uku. Ina kika baro Ummin?” Na ce, “Ummi na gidan Yaya Hauwa. Biki kuma Baba? Na wa?” Ya yi dariya ya ce, “Na Hassanar ku”. Ido warwaje na ce, “Zanirah?” Dariya ya yi, “It sounds like a film ko (kamar a shirin fim), to ya za a yi? Hajjah ta tada hankalinta aure za ta yiwa Zanirah, kinga kuwa babu mai ta cewa. Ko akwai?” Da sauri na shiga girgiza kai, na ce, “Babu kam, babu Baba”. Na mike da sassarfa zan shige Baba ya ce, “Baki ga Yayanki bane babu gaisuwa?” Yaya Aliyu ya ce, “Kyale ta Baba ai ta je kwaleji ta waye ne, kada ki sake ki bar gidan nan sai mun dawo Giwa yanzun nan”. A hankali na cira kai na dubi Yaya Aliyu, sanye yake da shadda (Hilton) ruwan toka mai gautsi. Sai sheki take cikin hantsin na safiyar Asabar. Ya rame sosai ya dan yi duhu, in ban yi kuskure ba sai in ce ko (ulcer) ce ta tashi ta kwantar da shi muna makaranta. Dara-daran idanunshi sun fada sun yi ciki sun yi ja ainun. Muka yiwa juna wani irin kallo na sakan biyu a hankali na ce, “Ina yini?” Ban damu da ya amsa ko bai amsa ba na wuce da sauri, har ina tuntube da kofar shigewar. Gaba daya yara suka diba ga Fa’iza, ga Yaya Fa’izah. Daya bayan daya nake daga su tika-tika dasu ina direwa. Na tambayi Junior Mama ita da waye? Ya ce ita da Yaya Zanirah ne sun zo su tare da Yaya Aliyu tana ta kuka wai za a yi mata aure. Na yi sallama a falon, Mama ce ta amsa. Zanirah na hango ta hade kai da gwiwa can a kusurwar falon tana rusar kuka. Na ce, “Wai Mama da gaske?” Ta ce, “Ni gara da kika zo, na kasa ma Zanirah, ni yanzu da ta zo ta sani a gaba tana rusa min kuka me zan yi a kai don Allah? Sanin kanku ne in Hajjah ta yi hukunci Babanninku basa musu. Wannan kukan duk aikin banza ne Zanirah kike yi ba zai sa ba, ba kuma zai hana ba”. Cikin kuka Zanirah ta ce, “To waye Mama? Waye mijin? An ce wa Hajjah yanzu ma irin zamaninku ne da ake irin wannan auren a kwashe lafiya? Ni ba aure nake ki ba, karewa ma ina da wanda nake so. Ta yi hakuri mana mu kammala makaranta zan kawo mata mijin”. Ni sai Zanirah ma ta bani dariya, don ni dai tun tasowar mu ban santa da wani saurayi ba. Na samu wuri gefen Mama na zauna na ce, “Wallahi Mama ni dama na san dole ne tsayin Zanirah ya dami Hajjah, duba ki ga duk ta fimu cika ido ga tsayi, Hajjah na yawan cewa “doguwa hankalinki a gwiwa, ni kar ki fado min a ka”. Mama ta yi dariya Zanirah ta zabga min harara. Mama ta ce, “Daman Zanirah ai ta girmeku, shekaru biyu ta baki kwarara, ke kuma kika bawa Ummi watanni biyar. Ni kam ban ga laifin Hajjah ba don an yiwa Zanirah aure yanzu, shekarunta goma sha tara ris, sai dai tunanin wanda ta baiwa auren. Na yi iyaka tunanina amma hankalina bai bani ba. Baban ku ma ya yi tambayar duniyar nan amma ta kafe sai ana saura kwana uku daurin auren sannan kowa zai ji”. Na ce, “Kai wannan tsohuwa da rigima take, ke Zanirah to mene ne abin kuka? Muma muna tafe, kin sani dai ko ba yanzu ba mawuyaci ne Hajjah ta kyale ki zuwa jami’a da shekaru kusa da ashirin, kai Hajjah ta yi dai-dai....” Zanirah ta taso kamar za ta make ni, ko me ta tuna? Sai ta juya ta yi bed room din Mama tana sharbar kuka wiwi kamar ranta zai fita. Ni dai Allah-Allah nake karfe uku ta yi na bar gidan zuwa Zaria kafin Yaya Aliyu ya dawo ya taddani, duk da Aunty Hauwa ta ce in bi umarnin makaranta duka gidajen biyu ba zan iya zama ba, can Ummi mun yi fada, nan Yaya Aliyu zai tirke ni. Ya kasa ganewa cewa nauyinsa da girmansa da nake gani ba zai barni in ba shi amsar wasikarsa ba. Na yi kokarin hakan amma na kasa. Karfe ukun na yi na dauki jakata na yafa mayafi, na yiwa Mama sallama na roke ta tasa Malam Garba ya kai ni Zaria. Zanirah ma ta dauko kayanta ta ce, ba za ta kwana a gidan ba ta fasa tunda Mama ta goyi bayan ayi mata aure da mijin da ba ta sani ba. Malam Garba ya ja mota, bai tsaya a ko ina ba sai a kofar gidanmu, yana aje mu ya juyo Kaduna. ‘Yan kannena kam sun yi farin ciki da ganina, suka shiga gyara mana daki. Daga momi har Baba babu wanda ya dawo aiki, Abdallah mai bi mani ya girma, yanzu yana aji uku na sakandire. Yayin da Walida ke aji shidan firamare ‘yar shekaru goma, Kausar na aji hudu, sai auta Walid yana Nursery. Yaran gidanmu akwai nutsuwa da kyakkyawar tarbiyya, suna masifar son junansu, ko ina suna tare. Idan Momi da Baba sun tafi aiki su kulle kansu a gida suyi ta karatu, in sun gaji suyi game suyi kallo, ga son baki, kula da sallah da son zuwa Islamiyya nan cikin (Area One). Walida ke fiddo ire-iren aiken da Yaya Fa’iz ke musu na kayan wasa masu aiki da batir da jirage masu tashi sama sosai na Abdallah masu aiki da (remote control). Zanirah ce kawai ta nuna sha’awarta ni ido kawai na bisu da shi. Momi kan yi abinci ne mai yawa ta cika musu cooler, don haka mun samu abinci mai rai da motsi, mun ci mun yi kat! Mun yi wanka ina shafa a gaban madubi daure da faffadan tawul, ya yin da Zanirah ke gefe ta mike kafafunta cikin ‘sofa’ sanye da doguwar riga a jikinta, ta zuba min ido kurum. Walida ta kyalkyale da dariya ta ce, “Aunty Fa’izah Yaya Zanirah fa kallon ki fa take yi”. Na dan juyo muka yi ido hudu da Zanirah, na