Sashe 82
Zumuntar Kenan Part 1 Complete Hausa Novel · about 2 min read
sanyin jiki, don dama neman hanyar mikewar nake yi na rasa, saboda gangar jikina da zuciyata sun gaza karbar sababbin al’amura masu girma irin wadannan da Fa'iz ke bijirowa dasu a wannan lokacin, wadanda bazan ce ban sani ba ko ban san sune suke wanzuwa a cikin aure ba. Sai dai ban taba yi ba ko kusantar yi ba a kulliyar rayuwata, daga yarinta har zuwa girma, sai ko yanzu da Fa'iz ke son tabbatar min da cewa, lokacin yin nasu ya zo. Goyon bayana da hadin kaina kadai yake jira, domin tabbatuwarsu, 'and I lack such a courage!' (Na rasa wannan kwarin gwiwar). A ganina ‘it’s not the hightime. ..... (lokaci bai yi ba). Don haka wanda ya danna kararrawar nan in banyi masa addu'ar alheri ba hakika ya cancanci inyi masa fatan ALHERI. Na bude kofar ba tare da tambayar ko waye ba haka ba tare da waiwayar halin da Fa'iz ke ciki ba, Surajo ne. Nayi murmushi na bashi hanya ya wuce amma kallo daya zai yi min ya tabbatar a rikice nake, kuma hankalina a tashe yake domin na tabbata ya zo ne domin ya dauki Fa'iz ya kaishi filin jirgi. "Madam rikici, ke kika rike Pilot ko? Kina sane da cewa karfe goma sha daya zai tashi? Don Allah a ringa lura da lokacin aiki cikin lokutan ayyukan soyayyar kada a koro ko ku koma direban tashar da kuka saba". Fa'iz ya harare shi yana gyara zaman gilashin sa a kyawawan idanunsa, bisa doron karan hancin sa. Ya kwalawa Ya'u kira, ya shigo da sauri, ya dauki jakar suka fita. Surajo ya aje min kwalin waya (Samsung-tablet) ya janyo kofar falon. Na bisu da kallo cikin shatatowar hawaye dana kasa maida su ko rage gudun zubarsu akan kundukukina. Ko hawayen menene? Bazan iya cewa ba. *****