Sashe 3
Zumuntar Kenan Part 1 Complete Hausa Novel · about 1 min read
matashi mai garin jiki irin na zuri’ar A.B Giwa. Hancin nan mikakke har baka, kanshi akwai tarin suma. Gefe da gefen fuskarshi tsagin mallancinshi ya fito radau, dogo mai tsayi da kafadu tun a wancan kananan shekarun. Da gani daga masallaci yake rike da tasbaha a hannunshi na dama. Shigowar shi ta katse Ummi da Zanira daga musun su, ya wuce ko kallon mu bai yi ba kai tsaye zuwa kitchen ya dauki filas dinshi ya