Sashe 18
Zumuntar Kenan Part 1 Complete Hausa Novel · about 7 min read
“Wannan haka yake”. Daga can cikin wani sako na kwakwalwata aka bani amsar. Tabbas biri ya yi kama da mutum. Yawan zancen Fa’iz da Ummi ke yi har ya so ya baci. Bana jin akwai ranar Allah da za ta fito ta fadi, bakin Ummi bai ambaci kalmar ‘YA FA’IZ’ ba. Na kuma sha jin an ce ‘adadin soyayyarka da abu adadin yawan ambatonsa a bakinka.....!;
“Amman Ummi kin cika banza, shashasha, dabba, mahaukaciya wadda ba ta san ciwon kanta ba.......!”
Ban san sanda kalaman suka yo ambaliya daga bakina ba. Kafin hawaye su shimfido a kundukukina. Na soma shesshekar kuka sosai. Su duka suka dube ni a razane. Na mike tsaye na shiga nuna Ummi da babban yatsana, idona a rufe bana ko ganin abin da yake gabana, na surfeta tas da zagin da ba ta taba tsammani daga gare ni ba.
A karshe na kare zancena da cewa, ......”Ummi in har kin yarda ki auri Fa’iz, ki sani karshen zumuncina dake ya zo, ko a hanya muka gamu babu gaisuwa tsakaninmu. Fa’iz kike so Ummi? Kyawun fuska ne zai rude ki ki manta da waye Fa’iz? Fa’iz Bamalli? Fa’izun gidan Babllan Kaduna ne fa, kyawun fuska zai rude ki? Mugu azzalumi, makaryaci, masharranci, mugun da bai san girman zumunci da girman iyaye ba. Mutumin da ya nuna mana kyara da tsangwama irin wanda wani dan’uwa bai taba nunawa wani dan’uwansa ba, Fa’iz HAFIZIN HAJJAH shi kike so Ummi?’
Muryata har dakushewa ta yi a wannan lokacin. Na dube ta da dukkan idanuna na ce, “Ummi kin manta baya? Kin manta duk abubuwan mugunta da tsanar da Ya Fa’iz yai mana? Shin farar fata koko zuwa Rasha ya rudeki ga son Fa’iz Ummi? Ko kuwa tukin jirgi da yake koyo.....?”
A nan ne ran Ummi ya yi mugun baci, domin da kallona kawai take kamar ta ga mahaukaciya. Ta ce, “Ke Fa’izah dakata, cin mutuncin naki ya isa haka, ya ishe ki kin ji ko? Kada ki kara don kuwa ni ba ‘yar cikinki ba ce da za ki sani gaba kina min wannan hayagagar ba tsoronki nake ba.
Da kin ki da kin so Fa’iz dan’uwanmu ne jininmu ne, ko me Fa’iz ya yi miki ya ci a ce kin manta haka nan as time goes on.... Haka kike da riko da gaba wanda ya wuce na musulunci? Wai ke baki san kuruciya bane? Ke abu baya taba zuwa ya wuce a wurinki?
Fa’izah ina son Fa’iz fisabilillahi na fada a yau na kara da babbar murya I LOVE FA’EEZ! Kuma insha Allahu shine mijina, ki yi duk abin da za ki yi, kada Allah yasa ki kulanin, kada Allah yasa mu yi zumuncin. In na auri Fa’iz don Allah kada ki zo gidana, in na haihu da Ya Fa’iz don Allah kada ki zo barka, kada kuma ki kawo riga ki ce a sawa dan ko atamfa in yi zanin goyo! In ce dai shine zumuncin?
Ni babu abin da Fa’iz ya yi min baya ga yanke gashi wanda daga baya ya zo ya zame min alkairi, domin ya zamo silar da na yi gashi irin wanda ban taba zaton zan yi ba (Fa’iz ya taba yankewa Ummi duka jelunan kitsonta da ya kamata a dakinsa ta dauki hotonsa ta boye cikin hijabi za ta fita).
Wata mugunta ko cin mutunci ko wulakanci kika ce ke ya shafa, matsalarku ne. Tsakanina da Fa’iz daban, tsakaninki da Fa’iz daban, ban ga dalilin da zai hada ki yi mana jimilla cikin al’amarin ba. Don haka ni a wajena komai ya wuce lafiya-lafiya, lafiyar Allah muka rabu ni da Ya Fa’iz cike da begen juna da fahimtar juna. Insha Allah sai kin goya ‘ya’yana da Fa’iz, kin ji ko Fa’izah?”
Ta fada cikin karaji da zazzaro idanuwa, duka a lokaci daya tamkar zararriya, ta daga hoton Fa’iz ta kai bakinta ta sumbata, ta kuma rungume a kirjinta ta ce, “Fa’izah, kin ce farar fata da kyawun Fa’iz ya rude ni ga son shi? Shin kin manta nima fara ce ba baka kamar ki ba? Kyawu na Bamalli duk ina da shi? Kina kuma tsammanin zuwan Ya Fa’iz Ukrain da tukin jirgi ne ya karkato zuciyata ga kaunarshi? Kin yi kuskure da wannan tunanin naki mara tushe Fa’izah. Bari in gaya miki sirrina da ko uwata da shi kansa Ya Fa’iz basu sani ba. Na fara son Fa’iz ne daga ranar da ya dauko ni a Gusau ya taho ya barki......”
Wata irin sarawa kaina ya yi na rasa me zan cewa Ummi don bakin ciki. Da dai a gida ne ba makaranta ba daura hannuwa zan yi a ka in fasa mata kururuwa ko in rufe ta da duka. Tunda babu damar yin ko daya daga ciki sai na ce, “Kaico! Kin cuci kanki Ummi tunda kika sanyawa zuciyarki soyayyar wanda bai cancanta ba, bai san mutuncin dan Adam ba balle dan’uwansa na jini. Na tausaya miki Ummi, muddin kika yarda kika auri wannan mugun mutumin na rantse sunanki sorry....”
Ta katse ni da cewa, “Ki ce ma sunana sarai asarar duniya ba sorry ba, ‘to be frank’ yanzu na saka danba a son FA’IZ MUKHTAR ABUBAKAR BAMALLI GIWA.....!”
Na ce, “Kin bata wayonki Ummi, wallahi kika aure shi za ki kwashi kashinki a hannu. Na rantse mai hali.......”
“Baya fasa halinsa fa Fa’izah!”
Ta karasa tana min dariyar tura haushi. Ta kuwa tura din. Ta ci gaba da cewa, “A ganina wannan ba damuwar ki ba ce tunda dai ba ke za ki zauna min dashi ba, bai shafe ki ba kowacce irin rayuwa zamu yi ni da Ya Fa’iz, tunda abin sa-kai-ne. Ina SON SHI HAKA!
Shine kadai ya tara dukkan abubuwan da nake so ga Da namiji, har ma ya zarta. Kafin a samu namijin da ya tara sura da ‘attributes’ din duk da ‘ya mace ke so irin Fa’iz za a jima Fa’izah. Don haka Fa’izah a yau ina mai farin cikin shaida miki cewa, ina son FA’IZ MUKHTAR ABUBAKAR BAMALLI GIWA!”
Sai na ce, “Allah ya ganar dake Ummi. Kin riga kin yi nisa ba za ki ji kiran ba. Allah ya shirye ki, ya ganar dake makiyinka baya taba rikidewa ya dawo masoyinka, ‘no matter what.... sai in ya ga kiyayyar tasa ba mai ci ba ce.....”
“wai ke sai kira kike FA’IZ MAKIYI! To makiyin wa? Ke ko mu? A lokuta da dama Yaya Aliyu kan ce bakya magana sai mai ma’ana da hikima a ciki, amma ga shi ni yanzu duk kin cika ni da rubbish (shirme). Wallahi duk kin isheni da surutu mara ma’ana. To wannan shirmen da kike shi zai sanya in tsani Fa’izun nima?”
Ta yi dariya ta shiga tattare kayan ta cikin ledar da aka kawo su. Tabbas da da ne ba yanzu ba da GIRMA da HANKALI suka zo ba, babu abin da zai hanani rufe Ummi da dan iskan duka, yakushi da cizo irin wanda muka saba da zarar mun samu sabanin ra’ayi ko don in huce bakin ciki da takaicin da ta kunsa mini, amma ina! Girma ya zo!! In ma mun yi ba zai mana kyau ba!!!
Sai na kyale ta na kwanta a gado na kama kuka mara sauti. Ni babban bakin cikina da muka yi a gaban su Haulatu muka farke sirrin gidanmu a gabansu, shin da me za su fassaramu ba dabbobi ba?
Wasikar da Fa’iz ya aiko abin da ya rubuta a ciki kawai “Ga Hankicina ki bawa Fa’izah, sauran kayan naku ne ke da Zanirah”.
Wannan wasika ta bai wa su Ummi da su Naja dariya. Wato su tsaraba wadda za ta amfane su, Fa’izah da ba a so ‘HANKICI! Suka kyalkyale da dariya.
Haule ta ce, “Kai zan so in ga Fa’iz dinnan face to face, am sure he will be vey funny”.
Ummi ta harareta ta ce, “Me kika ce? Ki ganshi ki yi mai uwar me?”
Suka kara kyalkyalewa da dariya. Naja ta ce, “Sorry Khadijan Fa’iz, ai mu Fa’iz ya wuce da ajinmu ba cewa zamu yi muna so ba. Wutsiyar rakumi ta yi nesa da kasa!”