← Book details Zumuntar Kenan Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 96 OF 98

Sashe 96

Zumuntar Kenan Part 1 Complete Hausa Novel · about 7 min read

* * *
Kwanaki bakwai da suka biyo baya, babu abinda ke wanzuwa a gidan sai amarci zallah, na a buga a jarida. Babu inda Fa'iz ke zuwa daga gida sai masallacin wani gida makwabtanmu, sai gidansu a Jabi Road shima duk dadewarsa baya wuce rabin awa.
Ranar da ya cika kwana goma sha hudu ya ce in shirya zamu je zaga dangi daga nan mu wuce Giwa wajen Hajjah, sun dawo daga Jeddah ita da Baba Na'ibi da Aunty Zainab inda aka kaita asibiti tsayin sati biyu.
'Yan uwa dake kewayen Kaduna muka fara zagewa, su Aunty Hauwa Maman Ummi, sai Jabi Road. Mama dai hadiyeni ne kawai bata yi kullum sai zuba mana albarka, haka Baban Kaduna albarka suke saka mana babu kakkautawa a duk lokacin da kafafun mu suka taka gidajensu. Da kara jan hankalinmu kan riko da ZUMUNCI. Su kan ce. "Ko babu aure mu 'yan uwan juna ne, don haka hakuri da junanmu ya zama dole don cigaba da (maintaining) burin Abubakar Bamalli, ya cigaba da ganin abinsa can inda yake, suna rokonmu ko bayan ransu...kada mu warware wadannan igiyoyi da suke kukkullawa a tsakaninmu kan kannenmu da 'ya'yayenmu, jikoki da tattaba-kunne.
Mun dauko hanyar Zaria bayan mun baro Kaduna, bayan motarmu shake da tsarabar su Walida (trolly) guda da Fa'iz yayo musu. Amma cikin rashin sa'a bamu same su a gidan ba. Walida tana makarantar WTC Soba tana shirin zana jarrabawar fita (SSCE) yayin da Abdallah ke makarantar horas da sojoji a Jaji (National Defence Academy). Kausar na S.S I a Sarauniya Amina, inda Walid autan Momi ya shiga shekararsa ta farko a karamar sakandire.
Babana Prof. Ahmadu A.B da Momina Maimunatu A.B, sun rasa ina suka-saka-ina-suka aje damu don farin ciki. A fili Baba ya daga hannu yana yiwa Allah godiya a cewarsa da Ya nuna masa wannan rana, wadda Hajjah har kullum ke ce da su tana zuwa! Yayi addu'a Allah Ya karawa Hajjah lafiya da tsawon kwana., Ya jikan ABUBAKAR BAMALLI. Gaba daya muka shafa da amsawa da
"Ameen".
Fa'eez ya tafi cikin city ya barni, ya ce zai je yaga Surajo ya dawo.
Bayan fitarsa ne Baba ya dubeni yana murmushi yake fadin.
"Yo ko ke fa Fa'izata?"
Na dago kai na dube shi nina murmushin nake yi. Rabon da inga yana walwala irin haka tun muna kanana sanda yake kaimu (Nursery) 'staff school'. Yana tuki yana mana tatsuniya har muje makaranta.
Idan ya debo mu akan hanya zai tsaya ne ya sai mana dafaffen kwai da gishiri ni da Walida da Abdallah. Kullum ne ranar Allah sai ya sai mana dafaffen kwai da zuma wai suna kara kwanyar karatu.
Idona ya ciko da kwallah da na tuno wahalar da na bashi 'in return'
"Na ce ko kefa? Dubi yadda kika yi kyau, kika ciko, da kika kwantar da hankalin ki. Amma watannin baya baki ga irin takaicin da kike sanya ni ba. Kullum idan na daga ido na dubeki a gidan nan wai na kasa lankwasa ki, wani abu ne ke tokareni a kahon zuci. Kullum tunanina wai 'yar da na haifa tafi karfina, tafi karfin UWATA da yayye na, a duk sanda nayi tunanin haka, na duba na hanga naga cewa babu wanda keda irin wannan dan cikin A.B ... sai inyi dakacen dama ba ni na haife ki ba!!!'.
Da rarrafe na isa ga Babana, kuka sosai nake har da majina.
"Ka yafe min Babana, ka dubi Allah kayi min afuwa, kuskure ne da aikin shaidan ina rokon Allah Ya kara nisantani da shi.
Duk abinda nayi nayi ne a bisa kuskure da rashin fahimta. Na roki afuwar yaya Fa'iz tuni ya yafe mini... Ina rokon ku kuma ku dubi Allah da nadamata ku yafe mini ko na cigaba da ganin haske a rayuwata... Ku taya ni rokon Hajjaty ta yafe mini...".
Baba yasa hannu ya dago ni, "Tuni na yafe miki Fa'izah, ina gaya miki halin da na shiga a baya ne ba don ban yafe miki ba. Allah Yayi muku albarka, Ya kyautata gabanku da bayanku, Ya baku zuri'a masu albarka!!!".
Ya sanya hannu ya janyo 'brief-case' dinshi ya fiddo wasu takardu, ya duba sannan ya miko mini.
"(Share) ne na banki na saya muku dukkanin ku, ke kuma na hada da bude miki 'account' da bankin JA'IZ don saukakawa mijinki wasu daga cikin lalurorinki. Na kuma bude shi ne da niyyar duk wata idan na dau albashi zan sanya miki wani abu a ciki, haka kason ku na wata-wata da ake baiwa duk wani da na A.B shi kuma na bude mishi 'account' daban da Bankin 'Fidelity' ga (details) dinnan ki adana a wurinki ko ki bawa mijinki ya adana miki".
Hannu biyu nasa na karba ina godiya. Na kare da cewa.
"Baba Allah Ya bar min kai!".
Murmushi yayi, "Nima Allah Ya bar min ke".
Momin tayi dariya tana jinmu bata ce komai ba, dana juya gareta sai naga ta sunkuyar da kai hawaye na diga daga idanunta.
Wato wannan din wata irin soyayya ce ta da da mahaifi da ita bata samu ba!
Kaico da iyayen dake haifar 'ya'yan su zubda su ko masu sacewa su raba su da iyayensu, saboda cimma wata manufa ta duniya. Ya Allah ka barmu da iyayenmu har karshen rayuwarmu, Ka kara musu lafiya da tsawon kwana, Ka basu ikon kula da hakkokinmu, muma Ka bamu iko da zuciyar yi musu BIYAYYAH don gamawa da duniya lafiya (Ameenm summa Ameen).
Dai-dai lokacin da Fa'eez yayi sallama shi da Surajo, Surajo ya gaida Baba da Momi ya koma tsokanata.
"Yau sati biyu kacal cikin takaba amma aka rangada kwalliya?"
Na galla masa harara Baba kuwa dariya yayi suka shiga hira na abinda ya shafi aikin Surajon (Banking), tashin zabuwar 'Doller' da 'sterling pounds' abin babu dadin ji. Sun dade suna hirar, tare da yiwa kasar mu addu'a. Muka yi sallama dasu muka dauko hanyar Giwa, shi kuma Surajo suka yi hannu ya shige motarsa ya koma cikin city inda gidan iyayensa yake. Har zuwa yanzun bai yi auren fari ba, na dai ji jiya Fa'iz na fadin ya kai kudin aure.
Muna tafe akan hanyar Giwa, sanyin na'urar sanyaya mota na ratsa kasusuwa zuwa bargon mu, sautin Abdurrahman Sudaith na tashi cikin Suratul Tagabun, Nake gayawa Fa'iz.
"Ko kasan rabon da kalami mai dadi ya hadani da Momi da Baba irin na yau, tun ranar da tsinkayi labarin daurin aurenmu? Na rasa wane irin so kafatanin A.B ke maka, kana da wata ilhama ta musamman da duk cikin zuri'armu babu mai ita. 'I salute!"
Na kai hannu na gefen goshi na daga. Gaisuwar girmamawa irinta bature.
Dariya na bashi sosai yayi harda bugun sitiyari.
"The salute best suits you! Yarinyar da ta gasawa kafatanin A.B gyada a hannu. Ta nuna musu JIYA BA YAU BA... GABA DA GABANTA WAI ALJANI YA TAKA WUTA... I salute too!!!".
Ya daga hannu a goshi, ya kankantar da ido cikin kallona.
Murmushi nayi cikin jin kaina yayi girma kamar fanteka. Na mika hannu na rike nasa, ya ce.
"Kinga matsa, kar kisa in watsar damu tun ban ajiye mai ce min BABA ba".
Dariya ta kamani sosai saboda yadda yayi maganar cikin zare ido da barazana launin idonsa na canzawa.
"To Baba Abubakar, direban zuciyata, the pilot that drives me crazy...".
Kuuu!!! Ya ja wani irin birki a tsakiyar titi, saura kadan ya yiwa wani mai babur diban albarka, motar tayi gaba tayi baya kamar zata hantsila. Kafin ayi haka kankame nake dashi ina shahada, idan mutuwarce ta zo ta daukemu tare ko yanzu ne na shirya mata.
A hankali ya gangara muka sauka a gefen titi.
Rikon da yayi min mai tsauri ne da saida kasusuwana suka amsa. Idan al'amuranshi suka birkita bana iya doje su a ko'ina ne. Ko nayi kokarin hakan bana cin nasara. Al’amuran soyayyarsa unimaginable, unabandonable' ne a gareni, and also, irresistible.
"Yaa Allah ka barni da Fa'iz, ka makantar da duk 'yan matan duniya daga kan mijina Fa'izu Abubakar, ka munanta shi a idanunsu ya zamo ni kadai nake ganin kyansa.
"You are my life Yaya Fa'iz... I'll always keep on loving you..."
"To say I love you Fa'izah, is not a way to express the feelings. .....!!!".
Muryarshi har bata fita, kuma kalaman, yana fadinsu ne tun daga karkashin zuciyarsa.
Bamu isa Giwa ba, sai karfe shidda na yamma.

***
Chapter 96 · 0% Book details