← Book details Zumuntar Kenan Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 37 OF 98

Sashe 37

Zumuntar Kenan Part 1 Complete Hausa Novel · about 5 min read

****
Fada na duniya babu irin wanda Aunty Rabi ba ta yi min ba a wannan daren. Ta inda take shiga ba ta nan take fita ba, har sai da na saka kuka. Na farko daren da muka yi, na biyu tsayawa a waje da namiji tsayin karfe sha dayan dare. Na uku wayar da ta ganni da ita, da izinin wa na karbo ta?
Don bakwa gaban iyayenmu ba zan ci amanarsu ba. Abin da ya zaunar daku gidana shine karatu ba (flirting) ba. Wannan wayar dole ki mai da masa abarsa gobe. Gaskiya ba dani ba, ba a gidana za a karya dokar A.B House ba, gara ma ku sake tsari. Gobe abu na farko da za ki fara da zarar kun shiga makaranta shine mayar da wannan wayar.
Yaya Muftahu bai ce komai ba. Haka na kwanta zuciyata ba dadi da haushin Aunty Rabi. Duk kula mazan da Ummi ke yi ba ta taba yi mata fada ba sai ni da na yi sau daya, ni da nake da niyyar aure ma ba flirt irin na Ummi ba. Da zuciyata daya nake son malamina, da gaske auren shi zan yi in Allah ya yarda.

I love you. If you hate it, kill with an arrow. But please not in the heart because that’s where you are. Gud night.

Sakon da ya fara shigowa cikin wayar kenan da na saka layin da ya bani cikin kwalinsa.
“Why will I hate it?”
Na tambayi kaina cikin murmushi.
“I do love it too!”
Na baiwa kaina amsa. Don haka na baiwa Malami na amsa.

“You inspire in me a love so deep and powerful that cannot be destroyed by any arrow! How I wish there is a way you could see into my soul. My love on you is far to strong Mallam!”

Daga wannan na kashe wayar gaba daya.

****
Washe gari tun asuba nice farkon yin wanka a gidan. Ban jira Ummi ba balle Yaya Muftahun dake sauke mu ya wuce office, na yi tafiya ta ni kadai saboda fushin da nake yi da Aunty Rabi, ban yi ko tunanin wani abu wai shi kalaci ba.
Babban burina in dora idona a kan lecturer. Kusan nice farkon shiga laccarsa ta karfe goma ta safe. Kai! Ni Fa’izah na shiga uku!!! Don I become infatuated to him fiye da kima. Akwai wani sirri dake cikin kwayar idanunsa da ba duk maza Allah ya mallakawa ba.
Sai dai kuma cikin rashin sa’a bayan ajin ya cika (class-representer) din ya ce ya mai da ita (fixed) karfe biyu na rana. Kamar na fashe da kuka dai-dai lokacin da wayar da na jefa a jaka ta kama tsuwwa. Cikin rashin kuzari na amsa da tunanin yadda zan yi in mayar da ita din kamar yadda Aunty Rabi ta yi umarni.
Muryar mace ke tambaya, “Dacta ne?”
“A’a, ba shi bane, wace ce?”
“Ke me maganar wace ce?”
“Matarshi ce!”
Sai ta kyalkyale da dariya ta ce, “Ki ce Haulatu Sani Galadanci na gaishe shi, kuma inda hali yana jiranki a office dinsa. Saboda ke ya dage laccar ku zuwa anjima. He can’t wait to see you.... cross sword....!”
Kunyar Haulatu ta kama ni ainun yadda ta yi ta canza murya ta shammace ni na yi tabargaza, na yi shuka a idon makwarwa.
Jiki babu nauyi na nufi inda Haulatu ta kwatanta min cewa nan ne ofishin nasa. A ofishin akwai hoton gwamna mai ci a lokacin da na shugaban kasa, sai na Alh. Dr. Ado Bayero. Sanda na yi sallama rubutu yake yi amma bai kasa amsa min ba.
Na samu kujera na zauna har ya kare, sai ya turo min folder din da yake rubutun nasa hannu biyu na amsa. Ko da na duba (note) dinsa ne da na yi missing har guda biyu cikin hand-writing dinsa mai kayatarwa da ban sha’awa.
Idona ya kai ga dan karfen dake like saman kofar shigowa ofishin da ban rufe ba. Sunansa ne radau DR. NAZIRU SANI GALADANCI. Wato Dr. Yayan Haulatu ne uwa daya uba daya ta yi min irin wannan ninkewar? Kai abin da mamaki.
Har mun yi sallama na kai bakin kofa sai na juyo na ce, “Na yi mantuwa ne”.
“Ta me Fa’izah?”
Na dawo a nutse na ciro wayarsa daga jakata na mika masa, yasa hannu ya karba yana fadin “Ya kika dawo min da ita?”
“Aunty Rabi tana ta fada ne, ita ce ta ce na dawo maka da ita, ba za a barni na rike waya ba sai na yi aure”.
Ya yi kasake cikin kallona da murmushi, “Sai na ji na kara son ki, na kuma kara yarda da cewa da ki kai ke din ‘yar babban gida ce. Abin da ban taba ji ba a wannan zamanin ‘yammata kamar ku a jami’a iyayenku sun hanaku rike waya, kuma kun bi, anyway. Ki ce ma Aunty Rabi ta yi hakuri, ba za ki sake rike waya ba sai kin zama matar Dr. Nazir insha Allahu”
[13/02 6:26 PM] Sumayya Takori: Da sassarfa na karasa ficewa daga ofishin ina murmushi.
Yinin ranar zungur na kare shi ne cikin tunanin Dr. Nazir da maimaita ambaton sunansa cikin zuciyata sakan bayan sakan, minti bayan minti, awa bayan awa son Dr. Nazir karuwa yake yi a raina. Yana kara habaka a birnin zuciyata.
Chapter 37 · 0% Book details