← Book details Zumuntar Kenan Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 59 OF 98

Sashe 59

Zumuntar Kenan Part 1 Complete Hausa Novel · about 4 min read

wani yafi kwanta maka. Da babanta ya ce min Fa'iz ya ce Fa'izah yake so da aure jikina ya bani akwai wani al'amari mai girma tsakanin Fa'iz da Fa'izah da babu wanda ya sani sai Allah. Nayi addu'ar Allah Ya hadasu da alherin dake tare da junansu, Ya rabasu da sharrin juna Ya kuma sanya albarka a cikin aurensu. Amma ga abinda Fa'izah taga ya fiye mata, titsiye miji ya saketa. Ba zan yi mata baki ba sai dai duniya kanta makaranta ce mai azuzuwa kala-kala. Kuma na roke ki Rabi, kada ki sanya sunana cikin sha'anin nan, har gobe ni 'yar kallo ce a cikin al'amuran ku, ki bar iyayenta suyi hukuncin da ya dace da ita". Momi ta share hawaye. "Babu wadda ta baiwa uwarta kunya a cikin A.B sai Fa'izah don ta tabbatar muku da gaske ni bare ce a cikin ku...". "Ki bar fadin haka Aunty Maimuna". Rabi ta katseta cikin jin tausayi. "Dole ince haka Rabi, shin da me zan doshi babanta da shi yau ya yarda ban san da zaman Fa'izah cikin gidana ba? Duk muna zaune aka yi saki akan idonmu, wallahi duk mu za su dorawa laifi...". Bata idasa maganarta ba tayi shiru saboda sallamar Baba. Prof. Ahmadu A.B, ya shigo da sallama, duk ya rame yayi duhu saboda tashin hankalin rashin sanin halin da nake ciki, da kuma ina na shiga. Ya samu kujera gefen Momi na ya zauna, ya ce. "Wash Allah! Taimaka mini da ruwa mai sanyi Mainmunatu". Momi ta mike tayi (kitchen) don ta kawo masa ruwan, sai a lokacin ne ya lura da autar Hajja a gefe, ya ce. "A'ah! Rabi yaushe a garin? Kin zo kuma kin tadda tashin hankalin da diyarki ta saka mu ciki ko? Fa'izah ta bani kunya, ta bada min kasa a ido. Ban taba zaton tana da wannan halin ba na kafiya da kekasasshiyar zuciya wanda ba'a taba samun irinshi a zuri'ar A'B ba. Sai dai ta wani bangaren na yi mata uzuri tunda ance Barewa bata yi gudu danta ya yi rarrafe ba, kuma duk abinda ka yiwa iyayenka ko bajima ko ba dade naka 'ya'yan za suyi maka (auren Momi da yayi ba tare da yardar nashi iyayen ba). Allah Ka bamu ikon yiwa iyayen mu biyayya, ameen. Rabi ta ce, "Ai tana nan cikin gidan dakin Abdallah, ba wani waje taje ba. Sai dai Fa'iz din yazo ya saketa har nan". Baba ya zabura ya mike, "What! Shi Fa'izun ne ya yi mana haka? Duk ta da hakarkarin da nake yi akan auren nan, tunda aka fara maganar auren nan bamu ci abinci ni da ubansa ya fada mana ba, shi ne ya biyewa shirmenta?" Momi ta karaso da gorar ruwan 'Rogolis' da tambulan din karau a hannunta da gorar lemon (5alive) ta aje a gefe don tasan bacin ran da Baba ya samu kansa a ciki ba zai barshi ya sha ruwannan da yake son sha ba. Bacin ran ya kashe kishirwar. Ta ce, "Kada kaga laifinsa Baban Abdallah, ta nemi rabashi da ransa in bai saketan ba me zai yi mata ya ceci kansa? Rotsa masa kwalba tayi aka fa?" Baba ya mike yana salati, ya kara da. "Innalillahi wa inna ilaihi raji'un! Tana ina tambadaddiya ku gani in babballata itama jikinta ya gaya mata, kisan kai zata yi? Shi kuma ya tsaya yana kallonta?" Rabi ta tabbatar muddin na shiga hannun Baba a wannan lokacin sai tarihina yadda komi nashi yake tsima kamar ana kada mishi gangi, don haka ta tare kofar dakin Abdallah tana fadin. "Yo Yaya in ka daki Fa'izah a yanzu aikin me aka yi? Wacce riba za'a ci? Baka huce ba tunda aikin gama ya gama, bakin alkalami ya bushe. Mu duba takardar idan ya yi na Musulunci ayi kokarin gyarawa". Ta shiga wurga ido neman inda ta cilla takardar saboda tashin hankali, kafin ta ganota a tsakanin kujerar da take zaune. Baba da kyar ya zauna a kujerar da ya mike sai wata irin zufa yake yi, makwallatonsa na kaiwa da komowa, duk ilahirin jikinshi rawa yake. Ya karbi takarda daga hannun Rabi ya warware, ga abinda dansa Fa'izu Abubakar ya rubuta cikin takardar. Baban Giwa ko Baban A.B.U. Fa'izah ta takura min in saketa alhalin ban iya hakan ko giyar wake na sha. Igiyar aure dai kowa ya sani uku ce, to ni Fa'izu Mukhtar Abubakar na ninka (ribanya) igiyoyin aurenmu da matata Fa'izah Ahmad Abubakar ukku sau uku =(9) kenan. A kara tausar Fa'izah don Allah kada wanda ya kara dukanta indai akaina ne, domin nayi mata laifin da na cancanci horo daga gareta fiye da wannan da take mani. Ko kun manta baya? Na tafi kasar Ingila saina dawo a san abin yi. Danku, mai neman albarkar ku. Fa'eez Giwa.
Chapter 59 · 0% Book details